Sunday, September 23, 2018

Funny short story: A SA MIN KIRAN SALLAH





A SA MIN KIRAN SALLAH
Na
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Wani Danfulani ne ya dauki azumi, kuma gashi a ranar ana yin rana sosai, don haka azumin yana baiwa Danfullo wahala sosai. Yana zaune ya yi jugum, ya kunna rediyo sai ya ji ana yin ZABI-SONKA, kowa yana buga waya ya gaishe da mutane uku, sannan ya fadi wakar da yake so a saka masa.

Danfulani ya buga waya aka bashi dama ya gaishe da mutane uku a karshe ya zabi wakar da yake so a sa masa.

Danfulani ya ce “Ni kam ina gaishe da Baffa Lamurado da Goggo, kai shu kenan, kawai a sha min kiran sallar magariba.”


10 comments:

MAKAHO MAI FITILA

MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...