Saturday, September 29, 2018

MATA-MAZA


MATA MAZA
Daga Fauziyya D. Sulaiman


Na taso cikin wani yanayi na matukar tsaro da mahaifana su ka dorani akai, duk wani wasa da maza tsarakuna ke yi mahaifana kan hana ni shiga, yayin da su ke taka tsantsan da ni gurin zama kusa da mata, sannan mahaifiyata ta na sanar da ni kar na sake ko da wasa na bar jikina a waje kowa ya gani, idan na yi hakan zan iya mutuwa, wannan tsoron na tashi da shi cikin raina matuka, don haka bana jin ban da mahaifana ba wani da ya taba ganin al'aurata.
sai dai na fahimci wani abu bayan na fara girma, akwai wani abu da na ke da shi irin na halittar kannena maza, sannan kuma ina da na halittar kannena Mata, da abin ya dame ni sai na tambayi mahaifiyata ni me ya sa na ke da guda biyu. A lokacin da na yi mata wannan tambayar na ga matukar tashin hankali a tattare da ita, amma sai ta ce min kar na kara yin irin wannan maganar idan na kara zan mutu.
kasancewar tunda na tashi ake tsorata ni da mutuwa ya sa duk wani abu da ya dangance ta ina tsoransa. Bayan na shekara goma shadaya mahaifina ya tattarani ya kaini almajiranci binni, duk da na san ni namiji ne kamar yanda iyayena suka sanar da ni, amma yanayin jikina ba shi da kwari irin na maza, hatta muryata da tafiyata irin ta mata ce, hakan ya sa tun ina garinmu ake tsokanata idan na yi magana har kawo zuwan almajiranci.
Lokacin dana kai shekaru goma sha biyar sai na ga kirjina yana dagawa irin na mata, amma sai na ci gaba da boyewa kamar yanda mahaifiyata ta sanar da ni. Watarana na je ganin gida ina kwance a daki ina bacci sai na ji kamar na yi fitsari a kwance, na tashi cikin gigita sai na ga duk jini ya bata jikina, na fara kuka da ihu ina kiran mahaifiyata, lokacin da ta shigo ta ga abin da ya faru hankalinta ya tashi kwarai da gaske, don haka ta kira mahaifina ta gaya masa, shima ya shiga damuwa, sai suka bani tsumma da wando karami suka ce na saka, anan ma sun kara gargadina da kar na sanar da kowa, sannan mahaifiyata ta sanar da ni duk wata zan dinga yin wannan abin kar na damu.
Na ci gaba da rayuwata a haka ina boye kaina ga yan'uwana maza, sai dai watarana ina cikin bara a cikin binni bakin hanya wata mota ta kwasheni ta yi watsi da ni, na ji mummunan ciwo a kafafuna da ta kai sai da aka kaini asibiti ranga-ranga.
Bayan taimakon gaggawa da likitoci suka bani da taimakon wasu bayin Allah aka yi min aikin da na sami saurki, sai dai tun da aka kawo ni asibiti likitoci suka sanar dani ni Mata-Maza ne, dole sai an yi min aiki an mayar dani daya.
Na shiga damuwa da tashin hankali, duk da mahaifina yana ta min nasiha da kwantar min da hankali, Amma ranar da likitoci suka tattauna da mahaifina su ka tabbatar min da cewar kwan halittun mace sun fi karfi a jikina, don haka dole mace za mayar dani .
Tun ranar da na ji wannan maganar na kasa bacci saboda tashin hankali sai kuka, ta yaya zan koma mace bayan na yi tsahon shekaru ashirin da daya a matsayin namiji, amma bayan ganin irin halin da na shiga na tashin hankali ya sa likitoci suka kara zama suka tattauna, sun ce zan iya komawa namiji amma sai dai a fitar da ni kasar waje domin yi min aiki, amma mahaifina ba shi da ko kudin motar da zamu iya komawa garinmu balle abin da za a yi min aiki. Ina jin yanzu kamar na gudu na bar garin nan, domin ta yaya zan kalli abokaina bayan an mayar dani mace? Shin waye ke da laifin kasancewar rayuwata a haka ne? Shin iyayena sun so na kasance namiji ne kawai domin ace suna da da namiji ko me ya sa suka min haka? Wannan sune tambayoyin da ke damuna babu kuma mai bani amsarsu har zuwa yanzu da na ke sanar da ku damuwata.

1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...