Saturday, September 29, 2018

LITTAFIN SHATA: NA SHA WAHALAR SHEME A LITTAFI NA FARKO - Dr. Aliyu Ibrahim Kankara




NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN SHATA A DUNIYA - DR. ALIYU IBRAHIM KANKARA
-Na sha wahalar Sheme a Littafi na farko

Na fara son Alhaji Shata da wakokinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Sa'ilin ban wuce shekaru 6 da haihuwa ba. Tun lokacin son da na ke ma Mamman Shata na musamman ne. Tun iyaye na ba su fahimta har su ka gane. Ko a Telebijin aka nuno shi ya na waka na kama murna kenan, da zaran kuma an dauke wuta kafin ya ida wakar, to har kuka na ke yi kuma na dinga fushi kenan har safe. 
Ni babana ba ya da wata alaka da Shata, amma ganin ina son sa ya kan zaunar da ni ya bani labarin sa, na zuwan da ya ke yi a RTK Kaduna (watau BCNN da kuma daga bisani NBC) a tsakanin 1969 da 1972 lokacin mahaifin nawu na aiki a can, da kuma ziyarar da ya kan kai ma amininsa Alhaji Hamza Kankara har Musawa lokacin ya na aiki a gonar mahaifin Shata Malam Ibrahim Yaro. 
Sai cikin 1975, watarana da babana za ya tafi Katsina, ya ce in shirya in bishi tunda a sannan ban shiga firamare ba, a sa'annan ya na da wata mota Morris Marina. Ba zan manta ba mun shiga Funtuwa a tsakanin mangariba da isha'I, har mu ka bi santar gidan Shata. A daidai kofar gidan Shatan mun zo wucewa sai babana ya ce da ni: 'Ali Gadanga, ga gidan Shata, ga shi can ma zaune kofar gida'. Ya fadi mani hakane saboda sanin da ya yi ina matukar son makadin. Sai na ce masa 'mu tsaya in gan shi' Sai ya  ce : 'a'a, saboda mu na sauri'. Amma gab da za mu wuce Allah Ya jiye mani muryar Shatan, na ji ya na cewa 'a zo a kwashe kwanonin abincin nan'. Wannan kenan. 
A tsakanin 1976 da 1978 an kai ni riko Daura wajen wana Ahmed Ibrahim Kankara, lokacin ya na aiki a can. To a can mu kan ga wasan Shata a kofar fada in ya ziyarci Sarki, da kuma Neja Club da ke kan hanyar Zangon Daura. Har ma nine Shatan Islamiyya Firamare inda na yi karatu. Idan an gama shara da marece, sai a zo bakin ofishin Hedimasta a yi wasan kwaikwayo, to nan ni kan dan yi wakokin Shata 'yan ajinmu na yi mani amshi. Sunan Hedimasta din mu Hamisu Famili, wanda daga baya ya zama Matawallen Daura. 
Cikin 1979 ina aji 5 na Firamare a Kankara (bayan babana ya bar Kaduna, mai riko na kuma na bar Daura) sai Shata ya zo kamfe na GNPP a cikin tawagar 'yan siyasa a Kankara, nan mu ka yi ta bin motar sa da gudu aka zagaya gari da mu, shi kuma ya na waka. Wannan ta sa wanshekare ni da abokina Garba (Abubakar) Suleiman Kankara (yanzu yana aiki a Dakin Awon Jini na Asibitin Tarayya ta Katsina) mu ka sawo littafi mai warka 40 mu ka fara rubuta tarihinsa, har ma mu ka samu shuwagabannin GNPP na yankin Kankara su ka bamu abinda su ka sani gameda makadin. Amma a lokacin ana ta yarinta, ba mu dauki abin da gaske ba, sai dai mi? abin da yaro ya ke so kuma ya girma da abin nan a zuciyar sa watarana sai ya tabbata, to ashe Allah Za Ya tabbatar da abin a gaba.
A tsakanin 1986 da 1994 ina karakaina, in kai gwauro in kai mari a tsakanin Daura, Malumfashi, Dutsinma, Kankara, Funtuwa da Katsina, duk samari masoya Shata sun sanni kuma inda duk na je ana maraba da ni ana kuma son in zauna in bada labari sabo na Shata da na kalato. Sai da ta kai ma a Malumfashi da Daura mun kafa Kungiya ta masoya Duna na Bilkin Sambo.  Cikin 1987 na fara zuwa gidan Shata kuma mu na haduwa da shi a Zariya (a Magume gidan Sani Gadagau, Bakatoshi) da Kano da Funtuwa da Katsina (Nasara Guest Inn, gidan Sa'in Katsina). Ba wanda ya fara kai ni ya gabatar da ni wurin sa, ni na kai kaina, musamman saboda dalilan can na sama. Cikin 1990, ina tammanin ma ran Lahadi 3/9/1990 ne lokacin na kammala karatu a Kwalejin Ilimi mai zurfi (CAS) Zariya na tafi Funtuwa na samu Shata na kai masa wani littafi da na rubuta mai suna Karon Battar Karfe (na yaki ko hikaya ne), na kwana har da safe ni da shi da Mati Bomber mu ka tafi ofishinsa na kan hanyar Zariya, lokacin ya na shugaban Jam'iyyar SDP, nan mu ka wuni. Na gabatar masa da littafi, na kuma bukaci ina so ya biya kudi a wallafa littafin. Amma ban samu nasara ba, don bai ce ya amince ba, bai kuma ce ba ya yi ba. Na yi wakokin Shata a CAS Zariya a kungiyar mu ta Hausa, a matsayi na na Shatan CAS, sannan da ina Jami'ar Ahmadu Bello na zama Shatan ABU na kungiyar Hausa, duk don dalilin soyayya ta da Shata, mai benen-bene na Izzatu Musawa. Ka ga kenan wanda duk za ya bada labarin ko nuna son Shata baya na ya ke. Wanda duk ya sha wuta baran tsire ne, kuma labarin dare a tambayi kura. 

Mafarin Tunanin Wallafa Littafin Tarihin Shata, 1992
A cikin 1992, lokacin ina karatun Digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello, aji biyu (300 Level) Allah Ya hada ni da wani yaro a Jami'ar mai kwazo mai ilimi ana ce masa Kabiru Husaini Gwangwazo, kuma lokacin ya na karanta Digiri akan harshen Turanci. Mun fara haduwa da shi a taron OUA na wasan kwaikwayo na daliban Turanci, inda ya fito a matsayin Shugaban Zaire watau Mobutu Sese Sekou. Sha'awar da ya bani ta sa na nemi mu yi abotaka, ya amince. Muna nan, mu na nan, ya zo wuri na, nima in je wurin sa. Sai rannan na dauki littafi na na Hausa da na rubuta mai suna Sako Daga Birni Al-Shabdad (na hikaya ne) na ba Gwangwazo domin ya duba mani. Bayan kwanaki, sai wani dan rikici ya sanya aka rufe Jammi'ar. Ina gida Kankara, sai na yi amfani da wannan damar na tafi Kano wajen sa domin in amso littafin. Sai na tarar an tsare shi a Ofishin 'Yan sanda na Bompai saboda littafin Danmasanin Kano da ya rubuta, aka kaddamar, amma a baya ya ranci kudaden mutane saboda hidimar bai biya su ba, sun sa an kama shi. 
To, a unguwar Takuntawa inda ya ke da zama sai aka kai ni wajen abokan huldar sa, to su su ka kai ni wajen sa a Bompai. Sai na tarar suna da wata kungiya mai suna Young Writers Club (YWC) Kano, wadda Kabirun ma mamba ne. To nan su ka rike ni na yi kwanaki a wajen su, su ka yi mani abin arziki, nan kuma na rika kwana wajen su. Kuma su ka bani fam na cika na zama dan kungiya. Ina tuna cikin su akwai Suleiman Gezawa, Rabi'u Kura, Rabi'u Mohammed, Mohammed Garzali, da sauransu. A cikin shirye-shiryen kungiyar ana rubuta tarihin mutanen da su ka shahara ko na garuruwa. To sai su ka bani shawara mi za ya hana in tafi Funtuwa in nemo izinin rubuta tarihin Shata daga wajen sa ? Tunda dama sun yi tunanin hakan tun kafin in bakunce su. Sai na amince. Na tafi Funtuwa, na yi sa'a na samu Shata a gida, na bashi labarin abinda ake ciki da kudurin wannan kungiya, da abin da ta sanya ni in yi mata. Ya yi murna. Har na ce masa : 'sun ce ka fadi mani ranar da ka ke a gari, don mu zo tare da su'. Ba zan manta ba har ya kama fada ya na ce mani 'ai yanzu na girma, na daina yawon zage, bare a ce a za a zo ba a same ni ba, saidai fa ko in kun ji ana wani buki a Rediyo, watakila zan je, to sai ku dakata sai randa ku ka ji ba a yin wata sabga ko nadin sarauta'. Mu ka rabu a haka. Na koma Kano na shaida masu. Su ka bani dama da in rubuta littafin. Na fara rubutu, wanda ya kai ni har cikin 1994 (bayan shekara 2 kenan) Na kammala. Sai mu ka kai littafin ga Ahmed Mohammed wani mai kafanin buga littattafai a Gidan Goldie kusa da Singer, Kano. Ana ta cuku-cukun ya za a yi a samu kudi a buga shi, sai na tafi bautar kasa a Legas. Ran da ma zani tafi, na biya ta Funtuwa na yi bankwana da Shata (ran Lahadi 13/11/1994) har ma na bashi kofin littafin, ya amsa ya rika ya duba. Har ya na cewa 'yanzu nan wannan duk aikin tarihi na ne? Na ce masa 'e'. Ya yi fatar Allah sa albarka. Sannan ya ce idan na dawo daga Ikko za mu zauna. Ya kuma lissafa mani wasu a Legas da in na je in yi ma intabiyu, mutanen sa kamar su Alhaji Na'Allah Dan Ibrahim da Alhaji Salmanu Agege, shugaban 'Yan Daudu na Afirka, da sauran su. Kuma na yi hakan.

Shirya Littafin Shata Ikon Allah

Na dawo daga bautar kasa cikin 1995. Sai kuma abokan aiki na na Kano su ka nuna gazawa ga buga littafi na jan kafa. Waje daya kuma na samu labarin Ibrahim Sheme daga Ya'u Wazirin Shata da wani abokina Kabir Dan'azumi Kankara wanda mazaunin Kaduna ne, bil hasali ma gida daya su ke zaune da Sheme din a unguwar Badikko. Kafin Ya'u waziri ya kara tunkara ta da maganar Sheme, sai kwaram rannan Shata ya yi ma ni bayanin sa. Ya ce mani na san shi? Na ce masa 'ban san shi ba, ba mu taba haduwa ba'. Shata ya ce mani ya kamata mu hadu, abinda ba ni da shi ya taimaka mani da shi, shi ma abinda ba ya da shi, da ni ni ke da shi sai in bashi'.  Amma bai nuna ya na so mu hade ba, amma ni a fahimta ta haka Shata ke nufi.  A waje daya Ibrahim Malumfashi (wanda ya zama Farfesan Hausa daga bisani) ma ya taba yi mani maganar sa, amma ba shi ya kai ni wurin sa ba.  Ni na kai kai na wurin Sheme a gidan san a Badikko din nan da dare, ina kuma zaton cikin 1995 din ne, don lokacin ban ma gama bautar kasa ba.  Sheme ya yi murna da gani na, cewa ya dade ya na jin labari na amma sai rannan mu ka hadu. Ya zaunar da ni, ya dauko mani aikin san a littafin Shata na gani, na kuma yaba.  Tun daga rannan bamu kara haduwa ba sai cikin 1997 da na koma Kwalejin Ilimin Kimiyya ta Kaduna da aiki. Ya taba samu na a ofis, ya nunaya kamata idan zamu hade ayyukan mu wuri daya mu yi haka, idan kuma ba mu yi to kowa ya kama gabansa. Matata Habiba ('yar mutanen Mangu)ta na sheda cewa Sheme, ban da ofis (tunda wannan ba ta gani ba) ya taba zuwa gida na a nan Kwanar PRP kusa da Angwan Sanusi duk akan zancen yiwuwar hadewar mu. Da, da farko Sheme na zawarci na amma na so in noke saboda halin rayuwa a gaba, amma sai matata ta nuna tunda ya nuna yana so mu hade in dauki aiki na in bashi, ta ce ta tabbata a gaba abin alheri za ya zama. Ta kuma tabbatar mani da cewa duk da ya ke ba ta taba ma ganin sa ba, ta san ba za ya cuce ni ba. Na rantse da girman Allah abin da ya faru kenan. Sai na aminta. Ran wata Asabar da safe Ibrahim Sheme ya zo waje na ya ce in dauko masa littafi na ya gani. Ba musu na shiga na dauko littafi gaba daya na bashi, don ni ba na iya tsallake maganar matata. Na yarda da ita. Mu na nan mu na nan, sai ya tura ni in yi intabiyu da wasu mutanen Shata, don shi ayyukan ofis sun sha masa kai. Kuma ina ta yi masa biyayya saboda ko ba komi akwai tazarar shekaru kimanin 2 ko 3 ma kuma ya na gabana a makaranta. Gashi a lokacin ya na 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatun Digiri na Biyu daga Ingila, ya na ta bani sha'awa. Inda duk ya tura ni ba gardama sai in tafi, watau a nan Kaduna. Sannan kuma na kan dauke shi in kaishi ga wasu da Shatan ya yi ma waka da shi bai ma san su ba, misali: Malam Na Gwandu mai nama, wanda ta hanyar Ahmadu Doka na san a Kaduna ya ke da zama. Sannan na dauke shi na kaishi ga Hauwa 'yar Bori matar marigayi Sarkin Bori Sule a Titin Bashama Tudun Wada Kaduna. Dole ne in fi Ibrahim Sheme sanin mutanen da Shata ya wake sabili da a kullum ina tare da Ahmadu Doka (unguwa daya mu ke zaune) da sauran makada da mawaka da su ka sha yin kwaramniya da Shatan, su ke bayyana mani mutanen Shatan. Ni da Doka, kuluyaumin ba mu da wani labari sai na Shatan.
Cikin 1998 sai Sheme ya tafi Funtuwa, ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano. A nan ya samu labarin wasu 'yan Kano su 2 su na rubuta tarihin sa daga bakin Shatan, don sun ma same shi aasibiti sun nuna masa aikin da su ka yi. Saidai su Sarkin Daura ya sanya su. Saboda haka Shata ya ce ma Sheme ya tafi Kano ya nemo su ya ce su zo Funtuwa ya na kiran su, don ya sanya su hade da mu. Amma Shata ya yi ma Sheme kashedin kada ya bayyana masu cewa bukatar sa a hade. Sheme ya dawo Kaduna ya same ni gidan marigayi Adamu Yusuf BBC ya bayyana mani abinda ke faruwa. Har na bata rai sai ya bani hakuri y ace haka Allah Ya so kuma mu yi fatan Allah sa abin ya zama alheri. Mu ka sa ranar tafiya Funtuwa, watau Asabar mai zuwa ta ran 19/9/1998. Tun ran Juma'a Sheme ya dauke ni, tare da wani abokinsa Aimana Datti Usman mu ka tafi mu ka kwana Funtuwa. Wanshekare da safe mu ka hadu da baki daga Kano a gaban Shata. Nan da nan Shata ya nuna da za a hade da ya fi, amma mu je mu yi shawara. Mu ka fito garejin motar sa mu ka yanke cewa mu 4 mu zama daya ga wannan tafiya. Mu ka koma mu ka shaida masa.
Amma cikin ikon Allah sai Allah Ya mantar da Shata ya tuna ma Sheme da sauran bakin nan wancan zancen littafin sa da na ke yi da kungiyar YWC ta Kano su ka sanya ni. Ni kuma, saboda kawaici sai Allah Ya rufe mani baki, saboda ma ina ganin ga wani sabon shafi an bude, to mi za ya sanya in kawo zancen abin da ma ya wuce? 
Mu kwana nan, za mu dora a gaba insha Allahu.



A nan take mu ka sasanta kawunanmu mu ka kuma sanya Sheme ya jagoranci wannan tafiya. Amma ko a sannan din yawan littattafan da na wallafa na Hausa sun fi na Sheme yawa; ba wai akan littafin Shata na fara rubutu ba. Mun aminta ya zama jagoran mu saboda shi ke da Komfuta don haka a kyauta ya ce za ya sanya a buga littafin kafin a kai shi madaba'a, kuma sannan ya gwanance wajen rubutu tare da basirar rubuta littafi. Mu ka dauki hotunan tarihi tare da Makada Shata har kala 12. 
Sauran hirarrakin da abokan mu su ka yi da wasu jama'a a cikin kasasuwan rikoda da ba su kai ga rubuta ko fassara su ba, su ka tattara su ka bamu. Shi kuma Sheme ya bani su, tare da bani umurnin in zauna in rubuta su in bashi. Na himmatu na yi aikin na kai masa. Daga cikin hirarrakin akwai ta Sidi mijin Hotiho da Hauwa mai tuwo.  Shima Sheme, hirarrakin da ya yi a kaset-kaset ya bani in dai rubuta, a ciki akwai ta Laila Dogonyaro, Musa Musawa da Bawa Dungun Mu'azu. Tun daga ran da mu ka bar gidan Shata su biyu su ka sakam mana aikin, su ka zare jikin su. 
A Kaduna, Sheme ya ke fada mani cewa 'Aliyu ka ga mutanen nan sun bar mana aikin nan, sun daina yin intabiyu da mutanen Shata'. Idan mu ka yi masu korafin haka sai su ce 'kun kira mu kun ce ga aiki kun ga mun ki amsa'? Sai ni da shi mu ka dukufa don nemo sauran hirarraki daga mutane, amma ni nawu aikin ya fi nashi fadada da nauyi, shi ma ya san haka. Don shima kan sa ba ya da lokaci, kullum aikin Edita na New Nigerian Newspapers ya sha masa kai. Kuma galiban duk ni na ke bashi bayanan wasu da Shatan ya yi ma waka da kuma wakokin su, don bai sansu ba. Watau al'amarin sa na Shata bai yi nauyi kamar nawu ba. 

Kwaram tun ma ba a je ko'ina ba bayan watanni 9 sai Allah Ya yi ma Shata rasuwa ran Juma'a 18/6/1999. Hakazalika Sheme ya kirkiri wallafa mujallar FIM a cikin Mayun 1999. Ga kuma aikin wallafa tarihin Shehu Musa 'Ya'aduwa da sabuwar gwamnatin Obasanjo ta bashi. Duk abubuwa su ka rincabe masa. A lokacin an sallame ni daga Kwalejin Kimiyya ta Kaduna ta hanyar rage ma'aikata, saboda haka ina zaune a Kaduna ba ni aikin komi (na zama abin tausayi) saidai rubuce-rubucen da ba za a rasa ba. Ganin haka, sai na dukufa, kuma muka shirya ni da Sheme, ina ta nemo labaru daga jama'a. Kuma ya kan tura ni ya bani kudin mota da na abinci zuwa Musawa. Dama tun cikin Maris 1998 ya tura ni Gombe da Bauchi don ganawa da mutanen Shatan na can wajen. A takaice ba a gama aikin littafin nan ba sai ina da kashi 65 na aikin littafin. Sheme ya bada gudunmuwar kashi 25, sauran abokan mu daga Kano sun bada gudunmuwar kashi 10. Allah Shi ne shaida ta, idan na yi masu karya zan hadu da Allah. Ni fa dalibin kimiyya ne ina da ilimin kididdiga ko statistics. Tuni na yi wannan lissafin na fitar da sakamakon. 
Game da wakokin Shata da na bada shawarar a tattara su a bangare daya na karshen littafin, shi da kan sa Sheme ya bani aikin nemo su. Gaba dayan wakoki 638 da aka sanya duk ni na bada su. Yanda aka yi na tattara su shi ne: da na ji wata waka ta Shata sai in rubuta ta a takarda in ofishin sa in bashi, koda ban tarar da shi ba sai in tura takardar a 'yar kafa ta karkashin kofa. Shi kuma da ya zo ya bude kofa sai ya gani. Sai ya dauka ya rubuta a kundin littafin. 

A littafin mu mai dauke da shafuka 604 ga dai gudunmuwar da na bada, watau wasu daga cikin wadanda na gana da su a lokuta daban-daban (kafin, da kuma bayan mun hade da sauran abokan aikin littafin): 
Hakimin Musawa, Inde Magajin Musawa, Sa'in Katsina Amadu Na-Funtuwa (oga kwata-kwata a zancen Shata), Wasu dattawan Musawa, Hauwa matar Sarkin Bori Sule, Babba Kofar Gabas, Maigarin Sayaya Yahaya Salmanu, Tijjani Hashim Kano, Walin Kano Mahe, Ada tela Daura, Ali Scorpion, Walin Kano Mahe, Dagacin Falgore, Shu'aibu Bada-Bada, Alaramma Sulen Shata, Ali Dankane Musawa da Mamman Tsalahu Musawa (da matan su), Hajiya Safiya Kumbula kanwar Shata, Danbaba makadi Musawa (makadin sa na farko), Balan Guzun kanen Shata, Bilkin Sambo, Sani Bakatoshi, Inuwa Dalibi, Uwawu Kano, Mairo Munari, Indo Musawa, Indon Danbaki, Garba Dan Ammani, Musa Dan Amare Musawa, Ayuba mai nama Musawa, Bala Abdullahi Funtuwa, Halle Jani, Garba Ja, Abba Na Titi, Sabo Dogarai Kano, Ahmed Kari Garkuwan Bauchi, Bappa Ahmed Gombe, Musa Usman tsohon gwamnan NW,  Hajiya Indo 'Yar Mamman Gombe, Magaji Mai Ido Daya, Amadu Doka mai kukuma, Alhaji Mayau Kaduna, 'Yayan Kungiyar makada da mawaka ta Kasa, Ali Dan Saraki 'Yankara, Musa Danbade, Sarkin Damben Hadejiya, Sankira Isiyaku Usman Galo, Abashe Yaro maihoto, Dauda Mani da Garba (Yaro) Na-Gwandu mai nama, Ado Kankiya, Garba Kwagira, Salisu Bangul Dandaudu, Yahaya Dandaudu, Shehu Tsatso,  Abubakar Kashe-kura na kofar Kaura. 
Wadanda kuma su ka rasu,  na tattauna da iyalan su, kamar su: Sarkin Katsina Nagogo, Haruna Kasim, Maude Tabako, Ali Bagobiri, Mati 'Yammama, Dan Lagai-Lagai, Sani Audi, Sule Dan Wazifa, Sani Stores, Mamman Da, Garba 'Yammama, Alhaji Abdulwahabu Malumfashi, Sani Dankwara Malmfashi, Ahmadun Gaya, Ciroman Gombe Umaru, Adamun Pankshin (Ladi), Garba Sarkin malamai. 
Na kuma ziyarci RTK sau da yawa na yi hira da ma'aikatan su kamar su: Ofishin kasuwancin su, Dakin ajiye faya-fayi, Lawal Yusuf Saulawa, Nasiru Maiwada Malumfashi, Ahmed Aja, Rashida Bello, Shafi'u Zangon Aya, Yakubu Gombe, Ladan Kontagora, Ibrahim Bako, Ahmed Girei (Dan uwan Dahiru Modibbo) Nine kuma na yi hira da wasu 'ya'ya da matan Shata kamar su: Binta Mami, Magaji, Salisu, Sanusi, Amina, Mamuda, Binta Iya, Asabe (Zuwaira), Hurera Yamai, Hadiza Falgore, Amina Dikke, Nasara Musawa, Yalwa, Binta Kankara, Hajiya Kulu Kaduna, Halima, Jamila. 

Wasu ma mutanen da na gana da su na manta da su.  Amma duk aikin nan da aka yi, na rantse da Allah ko kwabo ban samu ba, na tashi a tutar asara. An kaddamar da littafi, amma bisa ga amana, ya dace mu zauna mu 4 mu kasafta dan abin da aka samu, kowa a bashi ko da a hannu ne. Sai ba a yi haka ba. Shi dai Sheme shi ne shugaba na, su kuma su biyu daga Kano sai Tijjani ya ke wakiltar su.  Kudin da ba a amso ba daga mahalarta taro da su ka yi alkawari sai Sheme ya ce ya ranci gudunuwar Sarkin Zazzau ta N200, 000 ya gyara mota. Ganin haka, sai Shima Albasu, da ya amso kudin Badaru Babura (gwamnan Jigawa na yanzu, N100, 000) ya ranta shima ya gyara mota. Amma da Albasu ya fada mani sai ya ce Sheme ya kwabe shi ya ce kada ya fada mana, mu sauran biyun. Zancen kenan har yau ba a kara tada shi ba. Ni kuma na sa masu hajar mujiya. Gudunmuwar Alhaji Dahiru Mangal ta N250, 000 na ke tababa ko sun amsa koko ba su amsa ba? Tunda na ji shiru itama ba a rasa amsar ta. 
A lokacin wannan hidima ta tarawa da kuma kasafta kudin ina can Daudawa, wani lungu cikin daji ina koyarwa a Makarantar 'Yammata, su kuma abokaina su na Kano da Abuja a inda wadanda za a amshi kudn daga wurin su su ke. Haka su ka yi kumuiniyar su ta kudin ni ban sani ba. Sai daga baya daya daga cikinsu ke fada mani. Har inda yau ta ke ban yi masu magana ba saboda kawaici da hakuri. 
Sannan mu duka 4 mun yi alkawari wanda duk aka ba kofin littattafai ya kai wasu garuruwa, idan an sayar an bashi kudin to ya turo a asusun da aka bude ma littafin, kuma Sheme da Albasu kadai ke da sa hannun ko ikon fitar da kudi daga banki. 
Ni, na tafi Sokoto na kai littattafai, amma don tsoron kada a ce na saba alkawari, wadanda na sayas sai na tafi banki na aiko da kudin. Wadanda na kai Funtuwa kuma, da ba a samu kasuwa ba sai Sheme ya umurce ni da in kai su Kano in ba Ali Malami don ya kai BUK, haka kuma na yi. To tsakanin kudin kaddamarwa da na ciniki wallahi summa tallahi ban samu ko kwabo ba. Sai daga baya na fahimci kudaden an yi wani waje da su, bayan an sayar da littattafan. Yanzu an shirya mani gaskiya kenan? Kada fa ka manta kashi 65 na aikin littafin duk kokari na ne. 
Don saboda wahalar da na sha a littafin lokacin shirya shi, ranar da zamu tafi Arewa House bukin kaddamarwa, na kwana gidan marigayi Adamu Yusuf BBC, amma da mu ka zo za mu shiga motar sa, sai ya kada baki ya ce: 'za mu tafi kaddamar da littafin da Aliyu Kankara ya rubuta, ba su Ibrahim Sheme ba, domin su Sheme ba wata wahalar da su ka yi'. 
Na rantse da girman Allah abinda ya fadi kenan. Ya na lafira, na san zan bishi watarana. In na yi masa karya na san zamu hadu a gaban Allah. 

Dalilan Da Su Ka Sanya NaWare Na Sake Rubuta Littafin Shata Ni kadai Guda 8:

Duk da asarar da na yi na 'yan uwana sun rabe kudin littafi sun manta da ni, ban damu ba, don babana ya bani hakuri ya ce 'ba rabo na ba ne, rabon na nan tafe a gaba'. Na ce su zo a sake buga wani, sai su ka ce su sun gaji, idan ni ina da sarari in tafi in ci gaba. Kafin wannan lokacin, mun hadu a magana daya cewa kowannen mu na iya daukar littafin ko wani sashen sa ya rubuta wani abu game da Shata a gaba. Na rantse da Alkur'ani abinda Sheme ya bamu umurni kenan, kuma kowa ya yarda. Daga baya sai su ka yi mani gardamar maganar don sun ga ba rubutawa mu ka yi ba, ga kuma wani littafi ina ta kokarin fitarwa. Don sun ga littafin ne ya sa su ka canza magana. Ka ga hassada ta shigo ciki kenan. 
Amma dalilan da su ka sanya na ware na hada runduna ta ni kadai su ne:

Na sha wahalar Sheme a littafin farko. Bai cika daukar shawara ba, abin da kuma ya ga dama shi ya ke sanyawa ko ya ke cirewa ko da kuwa mu ba mu so hakan ba, alhali an ce tafiya ce ta mutum 4. Ai don ana so a samu idea ta kowa shi ya sanya aka game. To minene amfanin hadewar? A ce cikin mutum 4, mutum daya shi kadai za a dauki ra'ayinsa dole ? Ka ga ko tafiya ta tafi watarana sai an samu sabani. Duk labarin da na kawo masa sai ya tace ya zubar da fiye da rabi, sannan ya sanya sauran. Bangaren tarihin Shata da ya fi gardi da gishiri da nuna, sai na ga Sheme ba ya son nan wajen. Alhali abubuwan da ya zubda suma masu amfani ne. Mahaifin Shata mahalbi ne kuma gagararre, duk hatsabibancin sa Shata ya gaje su. Don haka komin iya yin mutum ba ya raba Shata da wannan hatsabibanci don gadon sa ne, saidai in ba ya son gaskiya, kamar kwatsam a ga ya bace ko a ganshi cikin fili ba tare da an ga isowar sa wurin ba. 
(Idan ana taron aikin gayya ko na mahalba, ba a ganin lokacin da mahaifin Shata za ya iso wurin, saidai a ganshi a tsakiyar fili, to shima Shata ya sha saidai a ganshi a fili ba a ga ta inda ya zo ba. Da mutum ya cire wannan a tarihin Shata to ya bata shi, kuma zancensa ya tashi daga tarihin makadin ya koma wani abu daban. Ka na iya raba mutum da abin da ya gada? An tabbatar Ibrahim Yaro ya na bacewa (ba mamaki ba ne saboda mahalbi ne) kuma ya na iya shiga cikin kukar gidan su ya kwana 2 bai fito ba. Ko kuma in ya shige ta sai a ga ya bulla a cikin tafkin Musawa. Daga gida kuma ya na kiran namun daji su zo wajen sa. Tsohuwar matar Shata da su ka zauna da shi a Musawa ta shaida mani haka, ta ce an yi abin a gabanta ba sau daya ba, ba sau biyu ba.Ya na kuma ba mahalba asirin kama dabba. Don na fadi tarihin mutum ai ba aibata shi na yi ba. To don dai labarin daga gare ni ya fito saboda hassada da kushe sai a karyata ni? Saboda ba'a kaunata ? Af, ba hatsabibancin su ka sanya shi ya yi kiwon kadoji har daga baya Shatan ya gaje su daga hannun sa ba? Tsofaffin da su ka bani labarin wasun su na nan da rai. Bangaren hatsabibancin Shata, Sheme babu ruwan sa da wannan, ni kuma bangaren da na fi so kenan. Ya ce wai babu scientific proof.  To Sheme ya je Musawa ya nemo tarihin Babu ya sha mamaki. In kuma an yi musun hakan, to a ce kiwon kadojin ma bai yi ba mana)  
Tun farko, yakamata a ce ra'ayin mu da akidar mu da tunanin mu, mu marubutan sun zo iri daya, sai aka samu akasin haka.  
A bangaren abubuwan da Sheme ke rubutawa akan Shata, akwai tawaya, saboda na rantse da Allah bai san Shata ba, ba ya kuma son ya san ko wanene shi. Tun a littafin farko, na jawo hankalin sa a kan matattun wakoki da basu samu gatancin da aka nade su a faya-fayin garmaho da Telbijin ba, cewa sun fi rayayyun wakokin sa (wadanda aka dauka a Rediyo da Telbijin) gardi da azanci da hikima tunda su ya riga yi, har ya zuwa tsakiyar shekarun 1960. To duk wakokin Shaa dodon hoto ne, ma'ana: su na da kanne ko yayye. Wadda duk ya yi, to watarana sai ya wanke ta ya yi samfurin wata irin ta. Amma Sheme bai yarda da wannan ba. Misali, Bakandamiya kala 130 ce, a cikin littafi na. Shi a wurin sa Bakandamiya ba ta fi kala 10 ba. A nan ma mun sha bambam. Da za a yi wa tarihin Sheme na Shata gwagwa za a gane cewa zunzurutun tarihin Shatan da ya sani ba wani abin a zo a gani ba ne. 

Irin fasalin intabiyu da Sheme ke yi ma mutanen Shata ya takaita su kurum ga wadanda ya yi wa waka. Shi ko wanda Shata ya yi wa waka bai san Shata ba kamar marok ko makadin Shata, don shi da shi ake yawo. Shi wanda aka yi ma waka ai zaune ya ke wuri daya sai randa aka iske shi. Ni kuma a intabiyu, na fi son in karkata ga maroka da Adamusawa ('ya amshin Shata) don su ke da tarihi. Su, sun yi ma Sheme nisa saboda a karkaru su ke zaune, su ko wadanda ya yi ma waka ga su nan ko'ina birjik har cikin Abuja. Don haka Sheme ya huta ba sai ya wahala ya tafi karkaru ba. Shi ya fi jin dadin ganawa da su akan Adamusawa. 
Dama ni na yi wahala na shiga lunguna-lunguna da kauyuka na nemi zancen Shata daga hannn Adamusawa da wadanda ya yi zama da su. Na yi imanin cewa Sheme ba za ya iya yin wannan wahalar ba. 
Sannan intabiyun Sheme ba mai nauyi ba ce, kuma ba ta ba da wani abin kirki da ake son a samu, duk da ya ke shi Dan Jarida ne. Misli, mun je Zariya tare da shi wurin A'isha Yalwar Yakubi Shandam, amma saboda nawar sa da rashin yi mata allurar zakulo labarin dangantakar ta da Shata sai ma ta ce mana aiki ta ke yi kuma ta na da baki. Karshe mu ka tashi aka yi asarar hira da ita. Sheme ya cika nuna lallashin mutum in ya je intabiyu, ni kuwa da zafi zan afka ma mutum, wannan zafin shi za ya sanya mutum ya zabura ya ga lallai da gaske na ke. Shi Shatan, ba da zafi-zafi ya kai ga shaharar ba? Da ya nuna son jiki ko nawa ko lallashi da ya samu daukaka da shaharar da ya samu? Shi ya sanya ni ke da ideas masu yawa; idan na fara bayani mutane ba su so in daina, kuma sun a da tabbacin abin da duk aka tambayeni san bada gamsassar amsa, don na samo ta. Ina kua allurar yi a duk wanda na je wurin sa hira, ko bai so yin hirar ba dole ya tsaya ya saurare ni. Misali, Alasan Abdallah Dunu, da na same shi a Kano, da farko sai ya ce mani ba ya da lokaci. Amma ina ce masa 'ranka ya dade da Kwastan kwara ne ya zo da kan sa da ka ce ba ka da lokaci ?'Sai ya yi znnbur ya tashi zaune ya ce 'yaro ina ka samo labarin Kwastan ? Ai kawai sai ya ce mani zauna, na zauna, sannan mu ka dosa hira, ya shiga bani labari tun lokacin da ya yi tuki a gidan Kwastan din a Malumfashi, shi da su Bawa Janke. Wasu mutanen da barkwanci-barkwanci, allura-allura ake kamo su da zaren labari, amma shi Sheme ba ya da wannan salon. Shi ya sanya hira ta ta fi ta kowa yawa. Bugu da kari, wanda duk zan je wurinsa, dama na haddace wakar sa a bisa kai, da na je saidai in yi ta rero masa baituttukan ina yi masa tambayoyi a kansu. Jin ina yin wakarsa  za ta say a kara bada azama. 

Gaba dayan aikin, Sheme na da jan kafa, ba ya da sauri. Ga shi ayyuka sun yi masa yawa. Ba ya da lokacin aikin littafin Shata. Ya na wallafa mujallar FIM, don haka ya na da ofis a Kano da Kaduna, daga baya ya bude wani a Abuja. Ga aikin littafin Shehu 'Yar'aduwa. Kuma kullum ya na hanya, ba ya Kano ba ya Kaduna, ba ya Abuja. Gashi duk watan Duniya sai mujallarsa ta fito, kuma shi ke shirya ta yanda ya ke so, iyakaci ma'aikatan sa s nemo masa labaru. Amma saboda kwararren mai aikin jarida ne, kuma a Ingila ya yi kwas akan madaba'ar littafi, shi ke tsara yanda mujallar za ta kasance don ta fito da kyau da inganci, kuma haka ta ke din. Don haka, ya kasa zama ya tattara hankalinsa wuri daya ya gama mana aikin mu. Shi kuma ya ki yarda ya bamu aikin mu tama shi, ya tattara ya rike. Har ta kai an kai matsayin da ba mu ma san halin da ake ciki ba. Wannan ya sanya mu duka ukun mu ka ma bata da shi. Mun dade ba mu magana ma. Sauran biyun su ka rika lallashi na su na cewa 'mu rabi da shi, watarana in Allah Ya so ai dole ya gama aikin ya fiddo shi a buga'. A haka mu ka yi ta lallaba shi har 2006 da aka buga littafin. 



Wasu Abubuwan Takaici ma su ne: 

A. wasu hirarrakin da na fassara a takardu na bashi na Hajiya Yalwa (matar) Shata da ta Musa Musawa da Laila Dogonyaro da Sidi Mijin Hotiho su ka bace ko salwanta a tsakanin kayansa saboda takardun sa sun yi yawa, kuma bai maida hankali ga aikin ba; ga na FIM ga na Tarihin 'Yar'aduwa. Saidai ni na dawo na sake rubuta wasu na bashi tunda su na cikin kai na na haddace su. 
B. Hotunan da mu ka dauka da Shata lokacin wannan ziyara ta tarihi kala 12, da kyamarar Sheme mu ka dauke su, wadda ya sawo a Ingila. Amma an kai wata 3 ina fama da shi ya kai ta a zare dodon hoton a wanke mana hotunan nan, kada mu yi wasa da su don a tarihi ne. Har na ke kwatanta masa cewa kyamara sumatsi ke gare ta. Karshe ya ki, har abinda ba a so ya faru ya faru. Rannan ya shigo Kaduna daga Zariya, a daidai NDA wani mutum ya tsayar da shi, ya dauko shi, jikkar da kyamarar ke ciki ta na a bayan mota (tunda da ita ya ke yawo) Wannan tsinannen mutumen ya zage jikkar ya dauke kyamarar, duk da fim din da ke ciki na hotunan mu da Dodon waka. Su na kai wa junction  na Unguwar Sarki mutumin ya sauka. Sheme na kara gusawa gaba sai ya tuna, ya tsaya ya duba jikka ya ga mutumin nan ya sace wannan kyamara. To ka ga duk sakaci da nawar Sheme ta jawo mana haka. Yakamata Sheme ya bamu hakuri akan wannan abin da ya yi mana. Nan dai wauta ce da sakaci. 
To tunda an rabu da kyar kai ka yi karambanin koma ma mutum a yi wani littafin tare ? Idan ka koma ka sake hadewa da mutum, duk abinda ya biyo baya kai ka ja ma kan ka kada ka yi kuka da wani. 
C. Lokacin da na tafi Katsina, bayan rasuwar Shata da wata 5, watau cikin Nuwamba 1999 sai na zarce Daura don in gana da Sarkin Daura, kan zancen yiwuwar daukar dawainiyar bugawa. Tunda a lokacin babbar matsalar mu ita ce kudin buga littafin. A fadar Sarki, aka ce mani ya na ciki ba za ya fito ba. Na gabatar da abin da ya kawo ni ga fadawa. Amma wani dogari ya ce mani idan na san wani mutum babba a Daura in je in samo takarda daga gare shi in kawo za su kai ma sa. Ana cikin maida magana sai su ka ji na ambaci Kankara (gari na). Sai wani daga cikin su ya ce 'ai kuwa dazu da safe Ibrahim Tukur Kankara manajan (tsohon almajrin mahaifi na ne a Karamar Firamare ta Kankara) Bankin Union na Daura ya zo su ka gaisa da Sarki, don mutumin sa ne. Sai su ka bani shawarar in tafi in same shi ofis. Na ruga na same shi, mu ka gaisa. Da na fada masa abinda ke tafe da ni, wallahi summa tallahi,na rantse da Alkur'ani mai tsarki nan take ba bata lokaci ya dauko wayar teburi ya buga ma Sarkin Daura Bashar. Su ka yi magana, ya gabatar da ni ya kuma ce ina son inga Sarki akan littafin,  Sarki ya ce ya fada mani in zo ranar talata mai zuwa da karfe 12 na rana in kuma zo da littafin, don Litinin ya na da taro a Kano. Ibrahim Tukur kuma ya tabbatar mani cewa shi za ya sanya Sarki ya biya kudin buga littafin. Tunda na bar Daura (ran Alhamis ne) na tafi Kaduna, ba zullumin da na ke shi ne yanda zan raba Sheme da littafin nan, don na san da kyar za ya yarda ya bani littafin. Kuma haka ta faru, don da na je na bshi labarin yanda mu ka yi da Sarkin Daura, amma wallahi summa tallahi ya hana ni littafin. Na ce masa ran Lahadi na ke son in koma Katsina, in kwana ran Litinin in tafi Daura, wanshekare in tafi in ga Sarki. Da ya dauki zancen har zucci da ya bani shi tun Lahadin. Amma har Litini bai ba ni ba, ina ta da lallashin sa. 
Ran Talata da safe na yi sammako na tafi gidan sa, na dade a falo bai tashi barci ba. Matarsa ta shaida masa na zo. Sai da na dade sannan ya fito ya bani littafin; don ya san bata yiwuwa. A lokacin karfe 9 na sfe ta yi kuma ina a Kaduna, yaushe na gane Daura a cikin awa 3 ?
Abinda Sheme ke nufi shi ne; duk wani yunkuri daga dayan mu a wurin sa aikin banza ne, ba mu isa ba, don ya raina mu. Ya na gani taimakon da za ya taso daga bangaren sa shi ne taimako, ba namu ba. Wai shugaban mu kenan a tafiyar Shata. Wallahi tallahi nan zance ya tsaya don ban ma tafi ba. Watarana nag a Ibrahim Tukur a Kankara, ya tambaye ni mi yasa ban koma ba? Na fada masa dalili. Ya ce 'Allah Shi kyauta'. 
D. Cikn Maris 2000, sannan dangantaka ni da Sheme ta yi yami, sai na same shi a gidan Shehu Musa 'Yar'aduwa da ke kusa da gidan gwamnati na Katsina, na same shi da dare. Ni na je ne don idan akwai rashin jituwa mu gyara barakar, mu ba juna hakuri, sannan a ga minene kuma za a dosa a gaba don a ci nasarar fitar wannan littafi. Amma sai Sheme ya same ni ya yi mani kaca-kaca, ya wulakanta ni ya ce 'littafi ba a baka, ka tafi duk inda za ka kai ni kara ka kai ni, kuma ni da kai har abada, kada ka kara zuwa inda na ke, ko ka ganni a wuri kada ka nuna ka sanni. Har ya na buga mani misali, ya ce a rayuwarsa mutum biyu ya taba yi ma haka saboda sun harzuka shi. Daga wani abokin sa (ya fada mani sunan sa, na manta) sai ni. Ya kuma ce:' littafi, idan Alla Ya hukunta za a wallafa shi, to sai a wallafa, idan kuma Bai nufa ba to. Ina fita kuma sai ya zo ya wuce ni a mota ya tafi cikin gari, ni ina ta tafiya kasa. Yanzu saboda Allah, mai karatu ka na ganin Sheme ya yi adalci a nan ?. Wai shugaba kenan. Shi shugaba, na yi tsammanin ya kamata a ce ya na da hakuri akan wanda yak e yi ma shugabanci, kuma idan an smu masala, ya kamata shi za a fara gayyatar mutane don a gyara, to ban da Sheme. Da haka ya yi mana shugabancin tafiyar Shata. Idan na yi masa karya kada Allah Ya bani abinda na ke nema Duniya da lafira.  

Ko an samu kuskure ko gyara, misali: a kan shekaru na faruwar wani abu, Sheme ba za ya gyara ba, ko da mun lurar da shi akan hakan. Ga hujja amma sai a yi ta gardama da shi. Da na fahmci haka, ko da na ga kuskure sai in yi shiru in kyale shi. Misali, a bukin 'Yan Sarki na su Ado Bayero, na ce Disamba 1952 ((tunda Galadiman Kano da Walin Kano da Sabo Dogarai da Inuwa Dalibi duk sun tabbatar mani haka) ne aka yi, shi kuma Sheme sai ya tsaya akan dole 1954 ne wai don ya ji Shatan na cewa '… a zamanin Sanusi Mamman' Na ce masa ai sannan Sanusi bai kai ga zama Sarki ba, ya na Ciroman Kano, amma shi ya yi hidimar bukin, shi ko Shata babu ruwansa, wanda ya ga ya na karakaina a buki shi a wurinsa shi ke da zamani. Misali na biyu shi ne ba Garba Goga ya fara kai Shata Funtuwa ba, don ya fadi haka a waka ba dole ba ne a ce daidai ne, shi ya san abinda ya ke nufi da Kalmar. Bature makadi Bakori shi ya fara kai Shata Funtuwa cikin Yuli 1943, sannan bai kai ga sanin Goga ba ma. Ba yanda ban yi ba da Sheme ya canza wannan zancen amma ya ki.  

Tarihin da Sheme ya fi so na Shata shi ne gama-gari wanda kowa ya sani. Ni kuma tarihin Shata da na fi so ya fito a littafin mu shine boyayye, wanda ya yi nisa, wanda Duniya ba ta san da shi ba. Ka ga nan dole mu raba gari. Don abinda mutanen Duniya ba su sani ba game da Shata shi su ka fi son su ji. Shi ya sanya ake matukar son hirarraki na na Rediyo da Telbijin fiye da kowanne mai bada tarihin Shata. Wannan ya sanya Idan Sheme bai san mutum ba ko bai taba jin labarin sa ba, ko na yi masa intabiyu na kawo masa ba ya sanyawa sai ya zubas. Kada Sheme ya manta, tarihin Shata ya fi karkata ga wadannan kaskantattun mutane maroka da makada (tunda karkara ya tashi) da ya ke ganin shi ya raina. 

Ina son idan za a yi hira da mutum, to a yi hira mai zafi, doguwa. Saboda ni mutum ne mai zafin hannu, mai azama, kamar dai yanda Shatan ya ke, watau tsaitsaye askin doki. To duk hirarrakin da abokaina su ka yi ba su gamsar da ni ba, don ba masu nauyi ba ne. Sabili da haka, galiban duk sai da na koma daga baya na sake hira da mutane, ba ma dai a nan kwaryar Kano. A baya kafin mu hade, abokanmu sun yi hira da su Umaru da Uwawu da Hassan sarkin Dogarai, da Liman 'Yalleman, da sauran su, amma da ban gamsu ba sai da na bi su na sake ganawa da su, saboda ni abin na cikin jini na. Dama a rayuwata na fi son zama cikin dattawan mutane ba yara ba, shi ya sanya in na yi magana a rediyo sai a yi ta mamaki, ana cewa 'mun dauka tsarar Shata ne ma ashe ma yaro ne'. To zama da tsofaffi ya kawo haka. Kuma hira daya tilo da wanda Shata ya yi ma waka wallahi ba ta isa, sai an yi da yawa don a samu abinda ake so. Ta yiwu shi wanda ka je  wurinsa tsoho ne, ya manta wasu abubuwa da yawa, to in ka koma sai ka kara samun abin da ya tuna kuma. Su abokaina da sun yi hira sau daya shikenan, ni kuma naci ke gare ni, yawan zuwa na wurin mutum ke sanyawa mu ma zama kamar 'yan uwa ma. 
Saboda wannan takardar yarjejeniya da mu ka rubuta shi ya sanya Sheme za ya yi ta yi mani cin kashi, kuma in yi ta hakuri ba zan balle in samu 'yanci na ba? Ba zan yarda takarda ta tauye ni in rasa 'yanci na ba. 
Za mu dora a gaba insha Allahu.


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...