Na
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Ni
kaina da abin ya faru a kaina na yi mamaki, amma daga baya sai na sami kaina a
wani yanayi na rashin madafa ko fitar da sakamako na hakika, ba mamaki in sami
wanda/wadda za ta sama min mafita.
Masoyiyata
mai suna Abida Aliyu Barau mun dade da ita kmuna soyayya, tana sona don Allah
nima ina sonta don Allah, iyayenmu da 'yan uwa da abokan arziki duk sun san
wannan soyayya tamu kuma suna sa mana albarka a ciki, suna taya mu son junanmu,
na zama dan gida a gidansu, itama ta zama 'yar gida a wurin iyayena da 'yan
uwana. Tana son abin da nake so, nima ina son abin da take so.
Wannan
tasa har aka amince min ina fito don aurenta a gidansu. Na fito din, na aika
iyayena aka sa rana.
Saura
wata daya da kwanaki goma sha uku a lissafe a daura aurenmu, muna zance Abida
ta yi bakuwa, mai suna Surayya, wadda kai tsaye wurinmu ta nufo, suka gaisa da
Abida, nima muka gaisa, suka dan yi hira kafin ta shiga da ita gida.
Tun
zuwan Surayya da muka hada ido da ita na ji wani yanayi a zuciyata, wanda na
rinka kokawa da shi, a karshe na tabbatar da mene ne a zuciyar tawa, wato so
ne. To, a lokacin na lura, ita ma Surayya ta ji abin da na ji, irin kallon da
na yi mata shi ta yi min.
Surayya
babbar kawar Abida ce da suka yi karatu tare, sun rabu tsawon shekaru uku da
suka wuce, ita ta tafi Misira, sai a wannan satin ta dawo.
Abu
kamar wasa, karamar magana ta zama babba, kawai sai soyayya ta kankama
tsakanina da Surayya, abin mamaki yadda na ganta ina sonta haka itama take
sona. Kar ka yi tunanin cewa akwai wani dalili da ya sa na sota, sam babu, kawia zuciyata ta ji tana son ta.
Domin ba ta fi Abida komai ba, kai in takaita maka labari kyau da fari duk
Abida ta fi ta.
Wani
babban abin mamaki shi ne da na nutsu sai na ga cewar ban fifita son kowacce a
kan kowacce ba a zuciyata, wato yadda nake son Abida haka nake son Surayya
(wato 50-50) bambancin daya ne kawai, na riga son Abinda kuma mun fi dadewa da
ita.
Wata
rana na je gidan su Surayya muna hira, ta ke tambayata "Yanzu kana ganin
babu matsala idan Abida ta gane muna soyayya? Ka san ni dai ba zan iya rabuwa
da kai ba."
Na
yi shiru kafin na ce, "Kar ki damu, zan tuntubeta game da hakan. Kin san
dai yadda nake son Abida haka nake sonki." A zahiri kuma haka ne.
Washegari
ranar da na je gidan su Abida da maganar, sai da ta yi jim tsawon lokaci kafin
hawaye ya fito daga idanunta, ta ce "Kana ganin hakan ya yi daidai Suraj,
shin kana ganin ka yi min adalci kenan. Ka san yadda kishi yake a zuci, ka san
yadda zuciya take da kissime-kissime..." Ta kasa ci gaba saboda kuka da
tasa.
Na
ji matuka tausayinta a raina, ji na yi kamaar nima in tayata kukan. A wannan
lokacin bamu kara cewa komai ba tsakanin ni da ita, abin yana damuna, ya zame
min goma da ashirin.
Ya
ya zan yi da wannan hali da na shiga? Kuma ya ya zan yi da soyayyar kawaye biyu
aminan juna?
Kaka-kara-kaka. Wannan shine, ' gaba Kura baya Sayaki. '
ReplyDeleteGaskiya ka tafka ganganci