MAI LABARAN ZAI GUDU
Wani Danfillo ne ya ajiye rediyonsa ya tafi daji kiwo tsawon
watanni bai dawo ba, har bera ya huda rediyon ya shiga ciki ya lalata wayoyin
cikin rediyon, da ya ga ba a damu da ita ba, sai ya sami mazauni a ciki ya
zauna.
Ranar da Danfillo ya dawo gida, ya dauki rediyo ya kunna,
rediyo ta ki yi, don haka ya dauketa, ya kai ta wajen mai gyara.
Mai gyara yana kwance rediyo domin gyarawa sai ga wani dirkeken
bera ya fito da gudu yana neman matsera, Danfillo na ganin haka ya yi zumbur ya
bi beran nan yana ihu yana cewa.
“Jama’a a taimaka a taro min shi mai labaran ne zai gudu, a
tare min mai labarai zai gudu.”
No comments:
Post a Comment