Saturday, September 8, 2018


GWARZUWAR GASAR BBC TA 2018:
Safiyyah Jibril Abubakar (Ummu Abdoul)
Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana labarin ''Ya Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.
Wata malamar makarantar sakandire mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar Hikayata ta bana.
Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna 'Ya Mace.
Da take bayyana yadda ta ji bayan da ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, "Lokacin da aka kira ni a waya aka shaida min labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce.
"Sai da na sake duba wayata don na tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kira na aka yi aka shaida min na yi nasara."

Labarin 'Ya Mace' a takaice

'Ya Mace, labari ne na wata budurwa mai suna Halima wadda ta shiga tasku bayan ta kai shekara 17 babu wani tsayayye, alhali a bisa al'adar gidansu da yarinya ta kai shekara 14 ake aurar da ita.

Matsin lambar da take fuskanta daga iyayenta da sauran dangi ya sa ta amince ta auri Garba duk da cewa ba a gudanar da wani bincike a kan shi ba.
Ga shi kuma mahaifinta ya ja mata kunne cewa kada ta kuskura a sake ta don idan ta dawo gida ba shi da halin daukar nauyinta.

Alkalan gasar sun yaba da ingancin labaran da suka duba
Sanin hakan ya sa Garba yi wa Halima wulakanci iri-iri, har lamarin ya kai ga duka da zagi.
A karshe dai auren ya mutu; da ta koma gida mahaifinta ya kore ta bayan ya lakada mata duka, sannan ya sha alwashin tsine wa duk wanda ya ba ta masauki a cikin 'yan uwa.
Wannan ya sa Halima ta yanke shawarar tsayawa da kafafunta ta hanyar kama hayar daki a cikin gari da yin ayyukan hannu don ciyar da kanta.
Sai dai ba a jima ba mai gidan ya samu labarin cewa ba ta da miji, ya ba ta notis yana mai cewa bai kamata mace irinta ta zauna a tsakanin mutanen kwarai ba.

Dalilin zaben 'Ya Mace

A cewar alkalan gasar, wannan labarin ya ciri tuta ne saboda ya yi nauyi a galibin ma'aunan da aka yi amfani da su don tantance labarai 25 din da suka duba.
"Labarin ya tabo wata matsala da ke faruwa a wannan zamanin, inda iyaye ke Allah-Allah su aurar da 'ya'yansu mata.
Tun da aka fara labarin ake hawa, ake tashin hankali da jan hankalin mai karatu", inji Bilkisu Yusuf Ali, daya daga cikin alkalan.
Jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya kara da cewa, "Matsalar labarin daya ce kawai: tun daga farko har karshe ake hawa, ba sauka. To amma shi ma wata dabara ce ta marubuta".


Marubutan da suka yi nasara a gasar bana

Safiyyah Jibril Abubakar malamar makaranatr sakandare ce, kuma daliba mai karatun digiri na biyu, wato Master's, a fannin Kimiyyar Kasar Noma a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.
Ta yi makarantar firamare a birnin na Zariya, sannan ta yi karatun gaba da firamare a garin Gwandu na Jihar Kebbi.
An fi sanin ta da suna Safiyyah Ummu Abdoul a duniyar marubuta. Labarainta, 'Ya Mace, shi ne ya zo na daya a gasar Hikayata ta 2018.
An haifi Sakina Lawal ne a birnin Kaduna na arewacin Najeriya, inda ta karatunta na firamare da sakandire.
Tana da takardar digiri a fannin Harshen Hausa wadda ta samu daga Jami'ar Jihar Kaduna.
Ita ce marubuciyar labarin Sunanmu Daya, wanda ya zo na biyu a gasar ta Hikayata.
Ita kuwa wacce ta zo ta uku a gasar, Bilkisu Muhammad Abubakar, a birnin Kano na arewacin Najeriyar aka haife ta.
Yanzu haka daliba ce a Jami'ar Bayero ta Kano, inda take karatun Shari'a, wato Law. Labarin da ta rubuta wanda ya kai ta wannan matsayi shi ne Zaina.

Labarin da ya zo na biyu

 
Sakina Lawal ce ta rubuta labarin da ya zo na biyu
Labarin da ya zo na biyu shi ne 'Sunanmu Daya' na Sakina Lawal.
Shi ma labarin wata budurwa ne wadda kyawunta ya rude ta har take ganin duk yadda ta ga dama za ta yi da maza.
Da ta samu wani wanda take ganin ya dace ta aura shi kuma yana da mata, sai ta sa ya saki matar, amma bayan ta aure shi sai ta ga ashe dai kallon kitse ta yi wa rogo don haka ta fita.
Daga bisani ta sake samun wani mai matar, amma suna son juna tsakani da Allah.
Sai dai kuma bayan ta aure shi sai ta tarar ba wata ba ce matar illa wacce ta sa mijinta na farko ya saka.
Labarin da ya zo na uku

 
Labarin Bilkisu Muhammad Abubakar ne ya zo na uku a gasar Hikayata.
Labarin da ya zo na uku shi ne Zaina, wanda Bilkisu Muhammed Abubakar ta rubuta.
Shi kuma labari ne na wata mai suna Zaina wacce mijinta ya yi batan dabo bayan tashin bam.
Bayan ta shekara shida tana jiran tsammani iyayen mijin suka matsa mata lamba a kan ta sake aure.
A karshe dai ta ba da kai ba don tana so ba, ta auri abokin mijin.
Wata rana suna zaune sai ga mijin ya dawo ba zato ba tsammani.

A karshen watan Oktoba ne dai za a karrama marubutan uku yayin wani biki a Abuja.
Wannan ce shekara ta uku ta wannan gasa, wadda aka kirkira don bai wa mata damar fadin albarcin bakinsu.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...