Friday, September 14, 2018

Kaima Ka Dara: GWAJIN DARASI



Kabiru Yusuf Fagge (Anka)


Malam Garba ya kammala darasinsa a ajin su Manu akan KALMA DA KISHIYARTA da kuma jimla itama da kishiyarta, sai ya fara tambayar dalibai don fahimtar ko sun gane darasin na yau.

Malam Garba ya dubi dalibai ya ce, “Zan rinka kawo kalma da jimla waye zai iya kawo min kishiyar duk wata kalma da jimla da zan kawo?”

Suruf! Manu ya daga ya ce “Zan iya Alagafarta Malam.”

Malam Garba ya yi murmushi ya ce, “To bari mu fara.”

Malam Garba ya ce “Sama.”

 

Manu ya ce “Kasa.”

Malam Garba ya ce “Ruwa.”

Manu ya ce “Wuta.”

Malam Garba ya ce “Malami.”

Manu ya ce “Dalibi.”

Malam Garba ya ce “Maikudi.”

Manu ya ce “Talaka.”

Jin dadin haka ya sa Malam Garba ya yi murmushi yana kallon Manu ya ce, “Amma kana da kokari.”

Manu ya ce “Amma kai dakiki ne.”

Malam Garba ya ce “To ya isa haka.”

Manu ya ce “Bai isa haka ba.”

Malam Garba ya ce “Kana da hankali kuwa?”

Manu ya ce “Mahaukaci ne kai.”

Malam Garba ya ce “Don gidanku ka yi shiru.”

Manu ya ce “Don kasuwarka ka yi magana.”

Malam Garba ya kara cewa “Na ce kai shiru”

Manu ya ce “Na ce ka yi magana.”

Malam Garba ya ce “Lallai yau zan ci gidanku.”

Manu ya ce “Lallai gobe zan ci kasuwarku.”

1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...