Ibrahim Sheme
A ranar Juma'a da ta gabata, jaridar Aminiya ta soma buga hirar da
wakilin ta, Bashir Yahuza Malumfashi, ya yi da ni a kan sabon bugun
littafin tarihin Alh. (Dr.) Mamman Shata Katsina mai taken "Shata Ikon
Allah!" wanda ya fito kwanan nan. Za ta ci gaba da buga hirar a gobe
Juma'a, in-sha Allah.
Jiya, sai ga martani
ya fito daga Dr Aliyu Ibrahim Kankara, daya daga cikin mu hudu da mu ka
yi binciken farko don a rubuta littafin. Ban so in yi cacar baki da
Kankara kan wani abu da ya shafi littafin ba, shi ya sa ma na yi hirar
da Aminiya gaba-gadi a bisa tunanin ko mutum ba ya kaunar Allah idan ya
karanta zai yarda da cewar lallai hakikanin abin da ya faru kenan. Haka
kuma akwai wadanda su ka ce mani, "Kada ka kula shi, domin ba matsayin
ku daya a idon al'umma ba."
To, ba maganar
matsayi ba ce, magana ce ta menene mu ka bar wa tarihi; idan na yi shiru
kan karan-tsayen da Kankara ya yi wa gaskiyar abin da ya faru, to ban
yi wa tarihi adalci ba. Haka kuma ni ba irin mutanen nan ba ne da za su
ga karya muraran su kyale saboda wani. Shi ya sa na ga dacewar in nuna
wa jama'a cewa akwai karairayi jingim a rubutun na Kankara, wadanda na
ke so a fahimta. Daga nan, idan mutum ya karanta, sai ya zabi na zabe!
Kafin
in jero karairayin, ina so in yi shimfida da cewar ba wannan ba ne karo
na farko da Aliyu ya fara shara karya game da tarihin Shata ko
dangantakar da ya ce wai ya na da ita da mawakin. Tun a farkon haduwar
mu, lokacin da ya kawo mani takardun da ya rubuta kan Shata don in gani,
na ga dimbin abubuwan shaci-fadi da ya rubuta wadanda hankali ba zai
iya dauka ba, wadanda ko d'an karamin bincike ma zai nuna wa mutum cewar
karya ne. Irin wadannan abubuwan, na yi watsi da su a lokacin da na ke
rubuta littafin "Shata Ikon Allah!" da aka kaddamar a cikin shekarar
2006. Na san Kankara bai ji dadin watsi da na yi da su ba, kuma hakan na
daga cikin dalilan shi na warewa daga gare mu, mu "marubutan littafin
Shata", ya tafi ya dauki littafin mu ya baddala shi ya fito da wani a
matsayin nasa (zan yi magana kan wannan a nan gaba, ba a yau ba).
Na
biyu, a zantuttukan sa a soshiyal midiya da hirarrakin sa a rediyo na
sha jin irin yadda Kankara ya ke zubo karairayi game da Shata ko
tarayyar da ya ke ikirarin ya na da ita da Shatan, ba tare da kawo
hujjar da za ta tabbatar da hakan ba. Hasali ma dai, Kankara ya saba da
sheka k'arya game da Shata ta yadda har akwai alamun ya yi amanna da
cewa karairayin sa gaskiya ne. Shi ya sa a duk inda ya zauna, sai ya
dinga zuba ratatata kan tarihin Shata da ba gaskiya ba ne, ya debo dahir
ya gwamutsa da kirkira, ya fitar da wata magana wadda yawancin masu
saurare ba za su kama ba. Har ta kai mutane da dama na mamakin yadda za a
ce wai mutum mai PhD ne ke magana haka babu kangado, sai ka ce ko
sakandare bai gama ba!
Irin wannan kame-kamen
ne na gani a rubutun shi na jiya mai take irin na taken hira ta da
Aminiya, wato "Ni Na Fara Rubuta Littafin Tarihin Shata", taken da shi
kan sa ba daidai ba ne (kamar yadda na fada wa Bashir Yahuza bayan na
karanta hirar da ya yi da ni).
Bari mu koma kan
karairayin Kankara. Da farko, ban damu da yaushe ne Kankara ya soma
kaunar Shata ba; ko tun ya na cikin ciki ya fara son sa, ba damuwa ta ba
ce. Amma wace irin soyayyar ya ke yi masa har ta kasance iyalin
marigayin ba su yarda da abubuwan da ya ke yad'awa game da mahaifin su
ba? Sannan wace irin soyayya ce ya ke yad'awa a hirarrakin sa ta yadda
duk manazarcin da ya bincika zai tarar da cewa zuk'i-ta-malle ce wadda
ba ta iya tsayawa da kafafun ta? Misali, "sai da aljannu su ka yi wa
wata 'yar bori bushara da haihuwar Shata!" "A ranar da aka haifi Shata,
an ji kalangai su na tashi a sararin samaniyar garin Musawa!" "Kafin
ranar sunan Shata, Shatan ya bace daga zanin goyon sa, ba a sake ganin
sa ba sai bayan kwana uku!" "Kai, Shata ba mutum ba ne, aljani ne!" Da
dai sauran su.
Bari mu duba martanin Kankara daki-daki.
1.
Cewar Kankara: "Cikin 1990 na ya kai wa Shata littafin da na rubuta":
Wannan
maganar, da makamantan ta da ya yi a baya, ba gaskiya ba ce. Ba zan ce
Kankara ba ya son Shata kafin haduwa ta da shi ba, amma wallahi shi da
Shata ba su san juna ba sai da na kai shi wajen Shatan a Funtuwa bayan
hadewar mu. Zurfin hulda ta da Kankara, tare da zurfin sanayya ta da
Alhaji Shata da yaran shi, ta isa ta sa in san idan Kankara da mawakin
sun san juna kafin haduwa ta da Kankara. Babu wani lokaci da wani daga
cikin su ya fada mani ya san dayan. In da Kankara ya san Shata kafin in
kai shi wurin sa, to da ya fada mani. Haka kuma in da Kankara ya yi wani
littafi kan Shata har ya kai masa, to da ya fada mani lokacin da na ce
mu je in gabatar da shi ga Shata a cikin 1997. Kuma in da Kankara ya yi
littafi kan Shata, to da ya ba ni shi lokacin da mu ka hade, mu ka shiga
fafutikar tattara tarihin Shata domin yin littafi.
2.
"Wai a 1994 Kankara zai tafi NYSC, ya kai wa Shata littafi".
Wannan
ma karya ce ya shirya. Ban san wani labarin Kankara ya nemo izinin
Shata don ya rubuta wa wata kungiya a Kano tarihin Shata ba, wanda har
ya rubuta ya kai masa da zai tafi bautar kasa. A rubutun shi, Kankara ya
ce har ya kammala littafin a 1994, to ya aka yi a 1997 da ya ba ni
warkokin da ya rubuta na ga ba su fi shafi 15 na rubutun hannu ba? Shi
ne littafin? Ya aka yi bayan haduwar mu, mu ka dinga fadi-tashin bincike
don fito da littafin, abin da ya dauke mu shekaru? Sannan idan har a
1994 ya rubuta littafin, to daga 1991 da na fara binciken tarihin har
zuwa lokacin babu shakka da na samu labarin sa a wajen Shata ko Ya'u
Wazirin Shata ko wani yaron Shata. A gaskiya, Kankara bai rubuta littafi
ba a lokacin.
3.
"Wai Shata ya umarci Kankara da ya yi hira da wasu mutanen Legas da ya wak'e".
Wannan
magana ba gaskiya ba ce, domin in da an yi hakan to babu shakka da
Kankara ya je ya yi wadannan hirarrakin. Tun da mu ka fara bincike kan
tarihin Shata har mu ka gama a 2006, Kankara bai kawo mana hira ko da
kwaya daya da ya yi da daya daga cikin mazauna Legas da Shata ya yi wa
waka ba.
4.
"Wai a 1995 Ya'u Wazirin Shata ya yi wa Kankara maganar Ibrahim Sheme".
A
cikin 1995 ba mu hadu da Kankara ba, ban san shi ba. Hasali ma dai, sai
bayan haduwar mu da na dauki Kankara na kai shi wajen Shata sannan ne
ya san Ya'u Wazirin Shata. Ni ne na dauki Kankara a mota ta, bayan mun
bar gidan Shata, na kai shi gidan Alh. Ya'u na gabatar da shi ga Ya'un.
Ko kadan Ya'u Waziri da Kankara ba su nuna wa juna sanayya ba lokacin da
na sada su. In da a ce an san Kankara a fadar Shata, to da shi mawakin
da shugaban 'yan amshin nasa sun nuna haka lokacin da na kai Kankara
wajen su.
5.
"Wai Ibrahim Sheme ya zauna gida daya da wani Kabiru Dan'azumi Kankara a unguwar Badikko, Kaduna".
A
Badikko, na kama hayar gida sukutum ne (2-bedroom flat da garejin mota
da filin tsakar gida). Ban zauna da kowa a gidan ba sai mata ta. Wannan
magana shirme ce.
6.
"Wai ba Ibrahim Malumfashi ya hada Kankara da Ibrahim Sheme ba".
Babu
shakka, ban taba jin ko sunan Kankara ba sai a bakin Malumfashi lokacin
da ya bukace ni da in hadu da shi in ga abin da ya rubuta kan Shata.
Farfesa Malumfashi na da rai, zai iya tabbatar da wannan magana ko
akasin haka.
7.
"Wai a 1995 Sheme da
Kankara su ka hadu har Sheme ya nuna masa aikin littafin da ya yi. Daga
nan ba su sake haduwa ba sai a 1997."
Wannan
ma wata karyar ce. A 1995, ban taba jin sunan Kankara ba, sai a 1997
lokacin da Ibrahim Malumfashi ya hada mu. Kuma tun da mu ka hadu ba mu
taba rabuwa ba har lokacin da aka kaddamar da "Shata Ikon Allah!" a
cikin 2006.
8.
"Wai Sheme ya ziyarci Kankara a ofis din sa a Kaduna Polytechnic a 1997 inda ya nemi su hade su yi littafi daya".
Wannan
ma karya ce. Tun lokacin da Malumfashi ya sada ni da Kankara, ba a yi
ko mako daya ba na amince mu ka hade. Sannan ban taba zuwa ofishin
Kankara a Kaduna Polytechnic ba; wani zuwa da na yi sau daya rak, na je
ne domin in taimaka masa kan wata wuta da ya kunno wa kan sa. Matsalar
ita ce wata yarinya daliba ta kai Aliyu Kankara ga hukumomin makarantar,
har an kafa kwamitin musamnan ana bincike. Na je ne bisa bukatar
Kankara in ga ko zan iya sasanta lamarin, a matsayin sa na abokin aiki
na kan littafi. A karshe, ba mu samu nasara ba, domin kwamiti ya bada
shawarar a kori Kankara daga aiki. Haka kuwa aka yi, aka kore shi daga
aikin koyarwa bisa koken da dalibar sa ta yi. Wannan ne ya sa ya koma
aiki a wani kamfanin wasu 'yan kasar Chaina masu hakar ma'adinai a
yankin Sakkwato (aikin da Saleh Abu Katsina ya sama masa). Daga can ya
kukuta aka dauke shi aiki a matsayin malamin makarantar sakandare (GDSS)
ta garin Daudawa da ke Faskari LGA a Jihar Katsina. Malamin Polytechnic
ya koma malamin sakandare kenan! Daga nan ne, bayan shekaru, aka dauke
shi aiki a Jami'ar Umaru Musa Yar'Adua a Katsina. Nan gaba zan dawo kan
ainihin kes din nan da ya sa aka kore shi daga Kadpoly da matsalar da ya
samu da Chanis din nan da yadda aka yi ya koma Jami'ar Tarayya da ke
Dutsin-ma, musamman ma yadda wadannan matsalolin su ka kawo mana cikas
wajen kammala littafin "Shata Ikon Allah!"
9.
"Wai matar Kankara na shaidar...!"
To,
ni ban sani ba idan maganar Kassu Zurmi gaskiya ce ba da ya ce "mutum
ba ya shaidar dan'uwan shi ko hwada" da kuma fadar Shata a wakar Dambu
Dan Mamman cewa "wace shaidar d'an ka za yai ma, in ka hada duka duk dai
Dambu ne?"
Wallahi, ban taba zawarcin Kankara
don mu hade mu yi littafi ba. Kamar yadda na fada, mun hade da Kankara
tun a satin farko na haduwar mu a cikin 1997. Idan na taba zuwa gidan
shi, hakan bay a rasa nasaba da aikin da mu ka tsunduma yi ne, ba domin
mu hade ba tunda mun riga mun hade. Amma shi ya kan zo gida nay a fi sau
shurin masaki, idan za mu yi tafiya ko idan zai karbi kudi a waje na.
Saboda haka maganar wai ina zawarcin sa domin mu hade ba gaskiya ba ce.
10.
"Wai Sheme ya fito 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatu na biyu".
A
1997 lokacin da na fara ganin Kankara har mu ka hade mu yi littafi, ni
ba sabon yanka rake ba ne wajen kammala karatun digiri na biyu. Na samu
M.A. Journalism Studies daga Cardiff University, a U.K., tun cikin 1994
(shekaru 3 kafin in fara ganin Kankara a rayuwa ta). A 1997 ina daga
cikin manyan editoci a kamfanin jaridar New Nigerian.
11.
"Wai Sheme na tura Kankara ya yi masa hira da jama'ar Shata saboda shi ba ya da lokaci".
Kamar
yadda na fada, na fara hira da Shata a 1991 domin rubuta tarihin shi.
Shekaru 6 kenan kafin in fara ganin Kankara. A tsawon wannan lokacin, na
yi hira da mutane masu yawan gaske. Misali: Garban Bichi, Indon Musawa,
Sa'in Katsina Amadu Nafuntuwa, Amadu Doka, Tukur Othman, Turi
Muhammadu, Musa Musawa, Munari Jikar Mairo, Nagwandu Mainama, Laila
Dogonyaro, Amadu Doka, Danmaraya Jos, Hakimin Bakori Alhaji Tukur Idris
Nadabo, Shehu Maigidaje, Halilu Ahmed Getso, Bala Maikaka, da sauran su
da dama. Kuma na yi hirarraki da yaran Shata da su ka hada da shugaban
'yan amshi Alhaji Ya'u Wazirin Shata da shugaban makadan kalangun Shata,
wato Bawa Dungun Mu'azu. Sannan na je Musawa na yi hira da 'yan'uwan
Shata da abokin sa irin su Mal. Ali Dankane. Duk wannan ya faru ne
KAFIN in ma san wani wai shi Aliyu Kankara. Sannan bayan haduwar mu da
shi, na ci gaba da yin wasu hirarrakin. Saboda haka maganar ba ni da
lokaci ma karya ce.
Tura Kankara da na yi zuwa
wasu garuruwan, kamar Bauchi da Gombe, da kuma Musawa saboda ya yi mana
hira da Magajin Gari Malam Abdullahi Inde da wasu mutanen, duk cikin
raba aiki da mu ka yi bayan mun hade mun zama mu 4 a aikin. Ko ya manta
cewar mun raba aiki ta yadda su Yusuf Albasu da Ali Malami su ma za su
samo mana wasu hirarrakin, musamman a Kano? Wannan shi ne dadin hadewar
ai, wato wannan ya kama nan, wancan ya kama can. Hakan ne ya sa ni ne na
yi hira da mutane irin su Dauda Mani da Sarki Jinjiri da Goshin Dangude
ba tare da Kankara ya sani ba sai daga baya na fada masa. Abin lura shi
ne duk da yake ina yin hirarrakin nan kamar yadda na lissafa a sama, ai
kuma ni ne mai rubuta littafin; ni ne wanda ke karance duk abin das u
Kankara su ka yayumo, ya fitar da ma'ana daga ciki, ya jera bayanan a
cikin littafi inda ya dace; shin ko wannan bai isa aiki ba?
12.
"Wai Kankara ya hada Sheme da wasu mutanen Shata a Kaduna tunda shi bai san su ba".
Hankali
zai iya daukar wannan maganar kuwa? Mutum ne ya same ka ka na bincike
domin rubuta littafi, har ka shafe shekara shida ka na yi. Kuma a Kaduna
ka ke zaune. Ka yi tafiye-tafiye a wasu garuruwa. To ya za a ce ba ka
ma san mutanen da su ne ka ke samo bayani a wajen su ba?
Kankara
ya ambaci Alh. Nagwandu Mainama, wai shi ya hada ni da shi. Wannan ba
gaskiya ba ce. Na yi hira da Nagwandu a mayankar da ke Tudun Wada,
Kaduna, ba tare da Kankara ba.
Kuma ya ambaci
Alh. Amadu Doka mai kukuma, wai shi ya hada mu. Ka ji tantagaryar
k'arya! Kankara ya manta cewa Amadu Doka amini na ne na tsawon shekaru
tun kafin mu hade, sannan ni din nan ni ne na fara kai shi wajen Amadu
Dokan har gida, na gabatar da shi? A nan ma dai, karya ce ya yi wa
kwalliya domin ya sayar da ita ga wanda bai ankara ba!
Na
yi hira da Amadu Doka domin sakawa a littafin Shata tun a cikin 1993
(shekaru 4 kafin in fara haduwa da Kankara). An buga hirar a mujallar
Rana ta ranar 19 ga Oktoba, 1992. A lokacin, ni ne Editan mujallar, kuma
ban san wani Aliyu Kankara a duniya ba.
13.
"Wai cikin 1998 Sheme ya tafi Funtuwa ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano".
Ban
samu Shata domin ya kwanta a asibiti ba. Kamar yadda na sha fadi, a
matsayi na na jagoran rubuta tarihin Shata, na sha zuwa in same shi kan
wani abu da ya danganci aikin. Kuma ba lallai ba ne sai na je tare da
Ali Kankara. Lokacin wannan ziyarar da Kankara ke magana, na je ne domin
in yi wata sabuwar hira da Shata kan wasu abubuwa da na lissafa wadanda
jama'a ke magana a kan su, misali batun cewar wai Sule Jikan Korau ya
taba marin Shata, da batun wai Shata ne ya yi wa Ali Dansaraki makaru ya
kasa waka, da batun Garba Goga ne ya fara kai Shata garin Funtuwa kamar
yadda mawakin ya ke ambata a Bakandamiya. Kaset din hirar, na ba
Kankara ya rubuta shi a takarda, kuma har yau din nan ya ki dawo mani da
kaset din. To, a wannan zuwan ne Shata da kan shi ya ba ni labarin su
Yusuf Tijjani Albasu da Ali Malami. A lokacin, ni dai ban taba jin wai
an kwantar da Shata a asibiti ba.
14.
"Wai Sheme ya dauki Kankara tare da wani abokin Shemen mai suna Aimana Datti Usman, su ka tafi Funtuwa".
Ban
taba yin aboki mai wannan sunan ba. Ina jin dai Aimana abokin Yusuf
Albasu ne da su ka je Funtuwa taro lokacin da na gayyato su daga Kano.
Ni Yahaya Umar na dauka a Zariya.
15.
"Wai Shata ne ya ce a hade a yi littafi daya".
Wannan
ba gaskiya ba ne. Makasudin kiran su Albasu da Malami shi ne a kwace
littafin su, a kore su, bisa hujjar cewa ba a ba su izinin rubuta
littafin ba. Da ni aka yi wannan shiri, ba a gaban Kankara ba. Ni ne na
bada shawarar a yi littafi daya, bayan mun fita waje na duba aikin da su
ka yi, na ga ya burge ni matuka domin sun yi hirarraki da wasu mutane
da mu ke so mu yi hira da su, irin su Abubakar Uwawu, Hassan Hadi, Delun
Kunya, Hauwa Maituwo, da sauran su. Shawarar da na bayar cewa a hade,
ta ba kowa mamaki, har shi kan sa Shatan, domin ba ta cikin shirin da
aka yi a makon da ya gabata. Sannan ko kadan Kankara ba ya goyon bayan
hadewar, kawai dai don babu yadda zai yi ni ne a matsayi na na shugaban
shi.
16.
"Wai Shata ya manta da littafin da Kankara ya rubuta wa kungiya, shi kuma kawaici ya hana shi magana".
Wannan
ma wani soki-burutsu ne. Lokacin da mu ka je taron da mu ka hade da su
Ali Malami da Yusuf Albasu a Funtuwa, an fi shekara daya da hadewa ta da
Kankara. Wato kenan Shata ya san ni da Kankara, saboda haka ya yi
maganar wani littafin kungiya ai bai taso ba. Me ya sa ma a lokacin da
na fara kai Kankara wajen Shata, na ce masa ga wani wanda za mu yi aikin
rubuta littafin da shi, ba su nuna sun san juna ba? Dalili shi ne babu
wata sanayya tsakanin Shata da Kankara, sannan Kankara bai taba kai wa
Shata littafin da ya ke ikirarin ya rubuta ba. In da akwai littafin,
kuma in da sun san juna, to da tun tuni na sani. Wannan maganar, kawai
kirkira ce aljannun da ke damun kwakwalwar Aliyu Ibrahim Kankara su ka
ba shi, shi kuma ya hau kai ya na kokarin yaudarar mutane da ita.
Ina
kira ga Aliyu Kankara da ya nuna guntun rikodin ko kwaya daya da ya
taba yi da Shata, wato wata hira da su ka yi, ko wani hoto da su ka taba
dauka tare, a matsayin nuna sanayyar da ya ke karyar sun yi wa juna shi
da mawakin. Na san babu. Dalili shi ne, Kankara da Shata ba su san juna
ba kafin in kai Kankara wajen sa, kuma ko da na kai shi din, babu wata
sanayya da Shata ya yi masa, domin bai taba zuwa wajen Shata ba tare da
ni ba, sai idan na kai shi. Hasali ma dai, Kankara bai taba hyin hira da
Shata domin yin littafi ba. Duk abin day a ke fada a bayan rasuwar
Shata, kirkira ce irin ta marubucin da kwakwalwar sa ta motsu, ya na
ganin dodon wani abu da ya ke ganin kamar ya taba faruwa a rayuwar sa
bayan kuwa bai taba faruwa din ba.
Zan yi zango a nan. Zan kawo ci-gaban wannan raddi nan gaba kadan, domin wannan magana yanzu na fara ta.
Bissalam.
No comments:
Post a Comment