Short Story
MATA MA NA SON SABO
(c) Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Lokacin da Alhaji Bukar ya zo
yiwa matarsa Sakina bayanin zai kara aure, sai ya fito kuru-kuru ya gaya mata
gaskiya, koda yake sun taba yin yarjejeniya shi da ita cewar su rinka gayawa
juna gaskiya, shi ne zaman aurensu zai yi karko.
Duk da haka, a wannan karon bai
kamata Alhaji Bukar ya fadi gaskiyar ba, ya kamata ya sakaya, amma ya zabi
fadar gaskiyar, ya ce.
"Kamar yadda na gaya miki Sakina,
aure zan kara. Zan auri 'yar wajen Ado Rasha, yarinyar nan da ta kammala
sakandare a wannan satin."
Sakina ta ce, "Na ji, ba sai
ka yi wannan dogon bayanin naka ba, tambayarka na yi mene ne dalilin kara auren
naka?"
Alhaji Bukar ya kalleta, sannan
ya kada baki ya ce, "Kin san dan adam yana son sabon abu, maganar gaskiya,
kin ga ke kin dan kwana biyu, ni kuma ina son sabuwar amarya."
Sakina ta yi shiru tana tunani,
sannan ta dube shi a sanyaye, "Alhaji kamar yadda ka fada, yanzu kana son
sabuwar mata kenan?"
Yana wage baki ya ce "Kwarai
kuwa, ke ya ki ka gani, na gaya miki dan Adam yana son sabon abu."
Sakina ta girgiza kai, ta ce,
"To Alhaji kamar yadda kake son sabuwar mata ba ka tsammanin nima ina son
sabon miji?"
Ya kalleta da sauri cikin mamaki,
"Wanne hauka ki ke fada ne Sakina, kina son sabon miji fa ki ka ce, kina
da miji fa, ke fa mace ce."
"Na sani Alhaji, amma kamar
yadda ka ce dan Adam na son sabon abu, maza da mata ai duk 'yan adam ne, kuma
kowannensu yana son sabon abun."
Ya yi shiru yana tunanin, lallai
Sakina ta raina masa wayo, me ya kamata ya yi mata?
No comments:
Post a Comment