Saturday, September 15, 2018

TARON BITA DA KWAS NA RUBUTUN GAJERUN LABARAI





Malumfashi Ibrahim 

Taron Bita Da Kwas Na Rubutun Gajerun Labarai Na Pleasant Library and Books Da Makarantar Malam Bambadiya



RANA: Asabar, 22 ga watan Satumba 2018.
WURI: Mazaunin Pleasant Library and Books, dab da hanyar zuwa Airport da ke kan Titin zuwa Daura, Katsina.
LOKACI: Karfe 10 na safe zuwa 1 na Yamma.

Ga zakarun gasar da za a yi wa kwas da bitar:

  1. Baki Abin Magana Na Umar Saleh Gwani Daga Jihar Bauchi
  2. Baya Ba Zane Na Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano
  3. Karambani Da Karambana Na Bello Hamisu Ida Daga jihar Katsina
  4. Keke Babbar Haja Na Danladi Zakariyya Haruna Daga jihar Kano
  5. Kilikinji Na Maryam Umar Daga Jihar Sokoto
  6. Lokaci Bako Na Abdullahi Hassan Yarima Daga Jihar Kano
  7. Riga-Kafi Ya Fi Magani Na Yazid Nasudan Daga Jihar Katsina
  8. Tubalin Toka Na Nafisa Abubakar Daga Jihar Katsina
  9. Tafiyar Marar Wuri Na Abdurrahaman Aliyu Daga Jihar Katsina
  10. Ina Matsalar Take? Na Bamai Dubawa Daga Jihar Jigawa

Wadannan zakakuran marubuta su ne za su halarci kwas na musamman don bitar yadda ake tsara gajerun labarai da suka shafi Ilimin kimiyya da Lissafi da Ingilishi, daga baya kuma su amshi awalajar da za su koma gida su rubuta cikakkun labarai da za a buga domin amfanin dalibai da malamai a makarantun Firamare da Azuzuwan Karamar Sakandare.

An tanadi wurin kwana ga mahalartan da za su zo daga wajen jihar Katsina. Ana sa ran su shigo ranar Juma'a, 21 domin halartar kwas din ranar Asabar, 22 ga Satumba 2018.
Don Allah wanda ya gani ya sanar da wadanda ba su gani ba.
Mun gode.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...