Sunday, January 18, 2026

Alƙalancin Gasar Rubutu


 Alƙalancin Gasar Rubutu

Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkayi akwai abubuwan da za su amfani marubuta masu sha’awar shiga gasa don yin nasara.


Ɗabi’ar Karatu

Wannan a bayyane yake cewa, yanzu al’umma sun fi son su kalla ko su saurara fiye da karantawa. Idan haka ne, to kai marubuci kana da gagarumin ƙalubale rubuta labarin da zai sa alƙalan gasa ko suna so ko ba sa so za su karanta, wato ko ba don aikin da aka ba su na karanta labarin su yi alƙalanci ba, ko don salo da gwaɗare na labarun sai sun karanta.

Duk da yake akwai waɗanda daman aikinsu kenan su karanta labari su yi masa alƙalanci, amma duk da haka idan kai marubuci ka saɓa lamba, to za ka hayayyaƙa su.


Lokaci

Masu sanya gasa sukan sa lokacin fara karɓar labaran shiga gasa da kuma lokacin rufewa, kamar yadda muka sani wasu suna sa wata ɗaya, wasu biyu, wasu uku har zuwa watanni uku ko fi. Misali, za a fara karɓar labari daga ranar 1 ga watan Janairu 2026 zuwa 1 ga watan Fabarairu 2026, wannan yana nuna wata 1 cur kenan.

To kai marubuci ka lura da wani abu guda, mafi akasarin kintacen lokaci na rana da muke amfani da shi, shi ne daga ƙarfe goma sha biyu da minti ɗaya na dare shi ne wata sabuwar ranar ta shiga, misali ko ba a sa lokaci ba, idan masu gasa suka ce ranar 1 ga watan Janairu, 2026, za a fara karɓar labarai to wannan ranar za ta fara ne a Alhamis 1-1-2026, kuma za ta fara ne daga kan 12:01 na dare. Sannan ranar Lahadi 1-2-2026 da misalin ƙarfe 12:01 za a daina karɓa. Wasu masu sanya gasar suna sa alama (alert) na ƙin shigar saƙon da ya wuce wannan lokacin, wasu kuma suna duba lokacin da saƙon da marubuci ya aiko ya shigo, da sun ga ya wuce da minti 1, to duk kyan labarinka, ya fita daga tsari, babu shi, kuma za su jefa shi gefe ko kuma kwandon shara.

Mu kuma ‘yan Najeriya saboda rashin sanin darajar lokaci, sai mu ga cewar ai ba wani abu ba ne don mun tura da dare ko ya wuce sha biyun daren, ko ya kai karfe 4 na asuba muna ganin duk ɗaya ne, to wannan kuskure ne.

A shawarce ya kamata marubuci ya tsara labarinsa cikin isasshen lokaci, ya bibiye shi, ya yi gyara, ya bayar a duba masa duk a cikin lokacin da bai ƙure ba, sannan ya tabbatar bai karya duk wata ƙa’ida ta gasar ba, bayan ya tura kuma ya bi da addu’a. Wannan kenan.

Wani abu da yake ƙara kawo matsala ga masu shiga gasa a ƙurarren lokacin ba wai ga masu gasar ba ne, ga shi marubucin ne ma. Idan marubuci ya ƙure lokaci, yana hana shi bibiyar labarinsa ya gano wasu kurakurai da sukan iya hana labarin nasa ya kai bantensa, ƙure lokacin yakan sa ya tafka kuskure wajen gaza gyara wani abu da zai taimaka masa wajen samun nasara.

Wasu marubutan masu wayo sun rubuta labarai da yawa, sun ajiye su, ana sa gasa kaza, kawai za su ɗauko, su kakkaɓe su, su gyara, su sauya abin da za su sauya, su tura a kan lokaci.


Adadin Kalmomi

Sau tari a gasanni musamman na gajerun labarai akan ce ana so kalmomin labaran kar su gaza adadi kaza kuma kar su wuce adadi kaza, ko kuma kawai kalmomi kaza ake buƙata. Misali a ce kada kalmomin su yi ƙasa da dubu 1000 kuma kar su wuce 1500.

To wannan yana bai wa marubuta da yawa matsala wajen ƙidayawa, kuma yana da sauƙi kamar yadda zan kawo misalai na hanyoyi uku da ake rubutun da su a yanzu, wato (1) rubutawa da biro da takarda (2) rubutawa da kwamfiyuta (computer) (3) sai kuma rubutu da waya (hand set)

Kafin na kawo su, akwai abu na farko da ya sa marubuta suke samun matsala da adadin kalmomi, wannan abu kuwa shi ne; marubuci yana ji a ransa ta yaya ana son ya isar da saƙo amma za a ƙayyade masa adadin kalmomi? To ina shawartar marubuta in har kana son yin nasara ka cire wannan tunani daga ranka, domin baiwar da kake da ita, ita ke sa ka tattara labaran shekaru hamsin ka rubuta a rabin shafin littafi, idan haka ne don an ce ka yi labari a adadin kalmomi 100 kawai ka ɗauki hakan a matsayin shan ruwa ya fi shi sauƙi, wannan kenan.

Yanzu ga hanyoyin ƙidaya kalmomi a rubutun.

(1) Rubutun biro ko fensir ko alƙalami a kan takarda

Da farko, ai a matsayinka na marubuci, ka san mene ne kalma ko? Kalma ita ce haɗakar sauti ko haruffa waɗanda suke ba da ma’ana, kuma ake magana ko rubutu da su. A kalmomin nan akwai na suna (misali: Ali, littafi, rago, saniya, labule, keke dss), sannan akwai aikatau (misali: tafi, ci, sha, tsalle, dara dss), akwai sifa (misali: baƙi, dogo, ƙarami, sabo, mai kyau dss) akwai wakilin suna (misali: ni, mu, ku, su, shi, ita), akwai bayanau (misali: a guje, da sauri, jiya, sosai dss) akwai mahaɗi (misali: da, kuma, amma, ko dss) akwai alamar motsin rai (misali: kash! Wash! dss) da sauransu. To idan ka san cewa waɗannan kalmomi ne, don haka lokacin da ka rubuta labarinka za ka bi ka ƙirga su ɗaya bayan ɗaya ka san adadin su. Misali, sai ka rubuta labari a layin farko kamar haka:

“Bayan da Musa ya shiga ɗakin, ya tarar da Hindu da wata yarinya a zaune suna kuka...” Idan ka zo ƙidayawa za ka yi su kamar haka:

(1) bayan (2) da (3) Musa (4) ya (5) shiga (6) ɗakin (7) ya (8) tarar (9) da (10) Hindu (11) da (12) wata (13) yarinya (14) a (15) zaune (16) suna (17) kuka...

Ka ga a nan kana da kalmomi guda (17) ka yi lissafinka daidai.

Wasu suna tafka kuskure wajen tunanin wasu ba kalmomi ba ne masu zaman kansu kamar dirka “ne” da “ce” ko “a” da “e” duk sai su haɗe su, ko su tsallake su.

Wasu kuma rashin bin ƙa’idojin rubutu ne yake haifar musu da matsalar rashin daidaita adadin kalmomin. Wani sai ka ga ya rubuta:

“Za’a” ko “shine” ko “mune” ko “gaka” “emana” kuma duk a harhaɗe maimakon a rarrabe, kalmomi bibiyu ya mayar da su ɗai-ɗai a lissafe.

Ko kuma kalmomi ɗai-ɗai ya mayar da su bibiyu, kamar “ya na” ko “dai dai” ko “mana” da sauransu.

To idan ka kiyaye waɗannan abubuwa kuma ka bi wancan tsarin da na kawo, za ka ƙirga adadin kalmominka cikin sauƙi.


(2) Kwamfiyuta

Kwamfiyuta tana da tsarin ƙidaya duk adadin kalmomin da marubuci ya shigar cikinta, akwai a farfajiyar wajen tafin (typing) ɗin MS Word, wajen da ake kira “Status Bar” ko kuma kai tsaye ka shiga wajen “Review” za ka ga wajen “Word Count” kana shiga za ka ga adadin kalmomin ka, kai har da adadin shafuka da adadin sakin layi da adadin layukan jimloli da adadin sarari (space) da ka bayar.


(3) Wayar Hannu

Haka a wayoyin hannu a kan WPS, kana shiga wajen “tools” sai ka je “view” za ka ga “word count” kana taɓawa zai kai ka wurin da za ka ga yawan kalmominka har da sararin da aka bayar (spaces) da wanda ba a bayar ba. Idan adadin ya yi yawa ko kaɗan sai ka daidaita.


Jigo

Masana sun sha yin bayani a kan jigo a mabambantan rubuce-rubucen ƙagaggun labarai daga gajeru zuwa cikakken littafi. Shi dai jigo, shi ne manufa ko saƙo na labari.

Sau tari masu sanya gasa musammman ta gajerun labarai sukan bayar da jigon da suke so a yi rubutu a kansa, kamar gasar Ɗangiwa, duk shekara suna bayar da jigon da suke so a yi rubutu a kai, kamar gasar Jigawa da aka fara ta shekarar 2025 ta kasance da manufar ayyukan gwamnan jihar Jigawa, wato Malam Umar Namadi. Amma wasu ba sa bayar da tsayayyen jigo guda ɗaya, kamar gasar Hikayata ta BBC Hausa da Gusau Institute.

To ko ma dai mene ne akwai abin da nake son marubuta su gane a kan jigo a gajeren labari, kuma shi ma yana bai wa wasu matsalar samun nasara. Saboda rashin tantance jigo ko matsayinsa a yayin rubuta gajeren labari wasu sukan cunkusa manyan jigogi sama da ɗaya ko biyu ko ma uku har huɗu, su lafta a rubutunsu.

A zahiri jigo ɗaya ake buƙata a gajeren labari, wanda wasu ‘yan ƙananan saƙonni marasa yawa suke tallafarsa.

Gajeren labari ba kamar dogon labari ba ne bare marubuci ya cunkusa masa manyan saƙonnin da ake gaza tantance wanne ne jigon labarin. Wasu marubuta sukan sami kuskure, su yi ta sako saƙonni ba adadi, waɗanda ba za su iya warware su a cikin ɗan labarin da suka rubuta na gajeren labari ba, kuma wannan sai ya sa a yi haihuwar guzuma, wato labarin ya gaza kai bantensa, wannan yana faruwa ne har a gasannin da ake sakar wa marubuta mara su yi rubutu a kan jigon da suke so.

Misali an ce a yi rubutu a kan jigon ƙazanta, sai marubuci ya kawo kishi da tarbiyya da mugunta da bara duk ya ba su ƙarfi a labarin, to masu alƙalanci za su rasa gane wanne ne jigon naka.


Yawan Taurari

Haka, su ma wasu marubutan sukan sami matsala wajen saka taurari da yawa a labarinsu. A zahiri shi gajeren labari ba ya buƙatar yawan taurari, domin yawansu yana nuna zaren labarin yana da tsayi kuma ya wuce a iya ɗinke shi a gajeren labari.

Shi gajeren labari ana buƙatarsa kaɗan, kuma a fahimce shi cikin sauƙi amma idan ka zuba taurari da yawa, to ana buƙatar a fahimci manyansu, kuma za su rikitar da labarin.

- Ba za ka iya gamsar da rawar da taurari da yawa za su taka a gajeren labari ba.

- Sannan ana sa tauraro wanda labarin ya fi karkata gare shi.

- Sai kuma tauraron da yake taimaka wa tauraron (jarumi) labarin naka ko kuma mai ƙalubalantar sa.

- Sai kuma wani tauraron mai ƙara armashi a labarin ko ya kunno wata rigimar a labari.


Ƙa’idojin Rubutu

Alƙalan gasa sun zubar da labarai da yawa saboda dalilan rashin bin ƙa’idojin rubutu.

(1) Wasu alƙalan suna ganin rubutun marubuci a hargitse za su ajiye shi gefe su ce marubucin bai san me yake yi ba, ko da kuwa labarinsa ya yi daɗi. (idan ya yi daɗin ma ba za a sani ba sai an iya karantawa)

(2) Rashin bin ƙa’idojin rubutu na sa adadin kalmomi a labari su ƙaru. Misali za ka rubuta “Muna sane da duk irin rigingimun da suke faruwa a cikin unguwar da kuma masu haifar da su.” Sai ka rubuta “Mu na sa ne da duk irin rigingimun da su ke faruwa a cikin unguwar da ku ma ma su haifar da su.”

Ko kuma ya rage adadin kalmomin cikin labari, misali za ka rubuta “Shi ne ya zo ɗazu amma na san ba a gan shi ba.” Sai a rubuta “Shine yazo ɗazu amma nasan ba’a ganshi ba.”

(3) Haka an samu marubutan da suka rinƙa rubuta “x” a matsayin “z” ko “s” su ma sun shiga tasku, domin an watsar da labarai masu yawa a kan waɗannan abubuwa. Marubuci zai rubuta “zama” sai ya rubuta “xama” da sauransu.

(4) Kuskure rubuta Hausar baka a wajen da ya kamata a rubuta rubutacciyar Hausa da sauransu.


Shawara a Dunƙule

Akwai abubuwan da marubuta ya kamata su kula da su a yayin rubuta gajeren labarin gasa, kafin rubutun ya je hannun alƙalai, waɗannan abubuwa su ne:

1. Jigo (saƙo)

-Marubuci ya tabbatar labarinsa yana da jigo bayyananne.

-Ya tabbatar saƙon yana da ma’ana.

-Ya tabbatar ya nuna jigon labarin ta hanyar labari, ba wai kai marubucin ka faɗa kai tsaye ba.


2. Tsarin Labari

-Marubuci ya buɗe labari da jan hankali.

-Marubuci ya tabbatar da rikici ko matsala a tsakiyar labari.

-Marubuci ya tababtar ƙarshen labarinsa ya zama mai gamsarwa.

-Sannan ya tabbatar tun daga farkon labarin ya tafi tiryan-tiryan har zuwa ƙarshe ba tare da zarmewa ba.


3. Taurari

-Marubuci ya tabbatar taurarin da ya sa a labarinsa, sun taka rawar da ya ba su yadda ya kamata.

-Marubuci ya tabbatar halayen taurarin sun bayyana a labarin.

-Ya tabbatar ayyukan da ya bai wa taurari sun tafi daidai da jigon labarin.


4. Salo/Sarrafa Harshe

-Marubuci ya tabbatar ya yi amfani da salo mai jan hankali (mai armashi)

-Ya tabbatar da ingantacciyar Hausa da zaɓin kalmomi.

-Marubuci ya guji maimaita wani abu ko tsawaita magana ko bayani (sai in dole ne)


5. Ƙirƙira

-Marubuci ya tabbatar shi ya ƙirƙiri labarinsa ba wanko shi ya yi ba, ko AI (ƙirƙirarriyar basira) ya bai wa, ya rubuta masa.

-Tunanin ya zama sabo ba gama-gari ba.

-Salon rubutun ya zama na daban.


6. Tsawon Labari

-Marubuci ya tabbatar ya bi ƙa’idar yawan kalmomin da aka buƙata.


7. Tasirin Labari

-Marubuci ya tabbatar labarin zai zama mai tasiri ga duk wanda ya karanta shi.

-Ya tabbatar ya zama mai kama zuciya.


8. Sunan Labari

-Marubuci ya tabbatar sunan labarinsa ya dace da abin da labarin ya ƙunsa.

-Ya zama mai jan hankali.


9. Tsari

-Marubuci ya tabbatar rubutunsa yana cikin tsari ba kura-kurai, cikin nau’in rubutu na Hausa.

-Kar marubuci ya cusa abubuwa da yawa marasa kan gado a labarin.

-Yana da kyau marubuci ya bar taurari su ba da labarin ta hanyar ayyukansu da maganganunsu. Kar marubuci ya shiga yana ta sharhi ko bayani.

-A ƙarshe, marubuci ya tabbatar ya yi gyara sosai a labarinsa.


Na gode

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Ɗalibi

Sunday, December 14, 2025

AN HORAR DA MARUBUTAN KANNYWOOD









MARUBUTAN KANNYWOOD 


Ranar Asabar 13-12-2025 aka gudanar da horo (training/workshop) ga marubuta 53 na masana'antar Kannywood wadda ta guda a ƙarƙashin Nigeria Film Corporation wadda Dr. Ali Nuhu yake jagoranta.


Horon ya gudana ne domin ƙara ƙwarewar wasu marubutan tare ƙyanƙyashe sababbin marubuta a masana'antar.


An gudanar da horon a ɗakin taro na Sarari Media and Telecommunications Hub da ke kan titin jami'ar Northwest Kano. 

Ƙwararrun malamai masana rubutun fim daga tashar Arewa 24 kamar Nazir Adam Salih da Fauziyya D. Sulaiman da Zuwairiyyah Girei da Nasir NID su ne, suka bayar da wannan horo.

Yayin da Kabiru Anka da Nura Nasimat suka kasance masu kula da gudanar da horon.

Bayan kammala horon, an bayar da gwaji don tantance marubutan tare da ba su shaidar kammala ɗaukar horo.

 

Tuesday, August 26, 2025

JAM'I A HAUSA (ADADI)


 

Adadi (Jam'i)

Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Adadi shi ne hanyar fayyace yawan abu, wato ɗaya ne ko kuma fiye da daya (jam’i) A harshen Hausa ana amfani da wasu ɗafofi don fayyace adadin abu ko kuma a ninka kalma. Wato idan ana so a nuna jam’in abu (idan ya fi ɗaya) a Hausa, akwai wasu ɗafofi da ake ƙara wa tushen kalma, ko kuma a ninka kalmar. Fagge (1992) (1993).

Jam’inta Suna

Ɗaiɗaiku Jam’i

arne arna

fansiri fansira

ma’auri         ma’aura

mabaraci mabarata

maharbi maharba

mahaukaci mahaukata

majemi           majema

maraƙi maraƙa

mayaƙi mayaƙa

shebur shebura

takalmi         takalma

takobi takubba

teburi tebura

yaro yara

*

bango bangaye/bangwaye

baƙi baƙaƙe


fari        farare

gado gadaje

gida gidaje

kara karare

kifi         kifaye

kwalba kwalabe

kwali kwalaye

maza mazaje

ƙasa ƙasashe

ƙuda ƙudaje

riga        rigage

shuɗi shuɗaye

wuƙa wuƙaƙe

wuri wurare

*

gona gonaki

kwana kwanaki

kunya kunyaki

tsara tsaraki


rana ranaku

tsara tsaraku

zana zanaku


alhaji alhazai

almajiri          almajirai

amini aminai

azzalumi azzalumai

fasiƙi fasiƙai

kafiri kafirai

kwabo kwabbai

madubi         madubai

magirbi         magirbai

makulli makullai

mataki matakai

sharifi sharifai

wakili wakilai

waliyi waliyai

wanzami wanzamai

waziri wazirai


*

banza banzaye

bene benaye

boka bokaye

dogo dogaye

ganye ganyaye

gwani gwanaye

gaula gaulaye

guntu guntaye

kifi         kifaye

kura kuraye

mugu mugaye

rimi rimaye

soro soraye

tandu tandaye

ɓera ɓeraye

wawa wawaye

zomo zomaye


dodo dodanni

wata watanni

fure furanni

wasa wasanni

kaka kakanni

shugaba         shugabanni

baba babanni

manzo manzanni

mako makwanni

sa’a         sa’anni


gardi gardawa

bature Turawa


kogo kwaggwai

biri          birrai

ɗalibi ɗalibai

malami          malamai

tajiri tajirai

jaki         jakai

jarumi jaruma

sabulu sabulai

dami dammai

faranti farantai

labule labulai

burtali burtalai

surutu surutai

kawali kawalai

shaƙiyi shaƙiyai

waziri wazirai

waliyi waliyai

kwabo kwabbai

fasiƙi fasiƙai

sahabi sahabbai

matashi          matasai

matsefi          matsefai

magirbi          magirbai

mataki matakai

maratayi maratayai

madubi          madubai

makami         makamai

mazagi mazagai

majanyi         majanyai

ma’auni         ma’aunai

mayafi mayafai

matoyi matoyai

mashimfiɗi mashinfiɗai

mazunguri mazungurai

makari makarai

mataji matazai

mashaƙi mashaƙai

makankari makankarai


nono nonna

goro gorra

zobe zobba

shuɗi shuɗɗa

mugu mugga

ƙato ƙatta (ƙatti)

tsoho tsoffi

reshe rassa

mummuna munana

kyakkyawa kyawawa

faffaɗa          faɗaɗa

kakkaura kaurara

zazzafa         zafafa


tsiro tsirrai

kwabo kwabbai

tudu tuddai

biri         birrai (birai)

jaki         jakkai (jakuna)

dubu dubbai

sama sammai

ƙasa ƙassai


ƙwaro ƙwari

tsako tsaki

zabo zabi

baƙo baƙi

fara         fari

ɓarawo        ɓarayi

ɗorawa        ɗorayi

hankaka hankaki

bawa bayi

makaho          makafi

tauraro           taurari


zana zanaku

mara maraku

tsara tsaraku

raga ragaku

rana ranaku


kaka kakanni

dodo dodanni

fure furanni

wasa wasanni

mako makonni

kasuwa         kasuwanni

sa’a         sa’anni

kada kadanni

manzo manzanni


shehu shehunnai


kamfani         kamfanoni

tinkiya tinkiyoyi

ƙaguwa          ƙaguwoyi

igiya igiyoyi

rijiya rijiyoyi

taguwa         taguwoyi

kanta kantoci

ƙofa ƙofofi

mota motoci

taga tagogi

ƙugiya ƙugiyoyi

tatsuniya tatsuniyoyi

tirela tireloli

tsabga          tsabgogi

dukiya dukiyoyi

waƙa waƙoƙi

lugga luggogi

hanya hanyoyi

buta butoci

bita         bitoci

tuta        tutoci

bata batoci


gatari gatura

sasari sasura

al’amari          lamura

haɗari haɗura

darasi darusa

wasali wasula

kabari kabura

magani         maguna (magunguna)

shagali shagula


gari         garuruwa

ɗari ɗaruruwa

ƙashi ƙasusuwa

buki bukukuwa

itace itatuwa

ƙirare ƙiraruwa

ƙafa ƙafafuwa


rami ramuka

layi                 layuka

launi launuka

tsani tsanuka

ƙauye          ƙauyuka

ƙwauri ƙwauruka

rauni raunuka

kare karnuka

tsauni tsaunuka

rafi         rafuka

taro taruka

kwano kwanuka


keke kekuna

tafki tafkuna

rago raguna

ƙoƙo ƙoƙuna

bante bantuna

kwando        kwanduna

bargo barguna

warki warkuna

kogi koguna

riga         riguna

wando wanduna

kanti kantuna

ɗaki ɗakuna

hula huluna

banki bankuna

sanda sanduna

doki dokuna

jaki         jakuna

lardi larduna

randa randuna

agogo agoguna

kambu kambuna

kumbo kumbuna


ma’auri          ma’aura


fata          fatu

laya layu

maye mayu

takarda         takardu

wasiƙa wasiƙu

shigifa shigifu

rigima rigimu

katifa katifu

kafaɗa kafaɗu

kunama         kunamu

ƙorama         ƙoramu

fitila fitilu

fitina fitinu


makaranta makarantu

masana’anta     masana’antu

maƙabarta      maƙabartu

masaƙa              masaƙu

maƙera         maƙera

majema          majemu

marina marinu

masussuka masussukai

mazauna mazaunu (mazaunai = ɗuwawu)

maciya maciyu

makasa         makasu

mashiga         mashigu

mahaɗa          mahaɗu

ma’ajiya ma’ajiyu

mayanka mayanka

mafita mafitu

magama magamu

mahaifa         mahaifu

mazaɓa         mazaɓu

magudana magudanu

maraya        marayu

matata matatu

tattabara tattabaru

mafita mafitu

maraya          marayu

alkyabba alkyabbu

algaita algaitu

albasa albasu


ƙasida ƙasidu

dabara dabaru

gajere gajeru

katanga        katangu

jemage         jemagu

labari labaru

buƙata buƙatu

shekara         shekaru

makiyaya makiyayu

makwarara makwararu

magudana magudanu

matsera          matseru


hannu hannuwa

kunne kunnuwa

ido/idanu idanuwa

zane zannuwa

ƙafa ƙafafuwa

abu        abubuwa

aji          azuzuwa


bahaushe hausawa

baduku dukawa

bagobiri         gobirawa

badauri        daurawa

bayarbe         yarabawa

banufe nufawa

bakane kanawa

bafade fadawa

bakule kulawa

baƙauye ƙauyawa

basakkwace sakkwatawa

ba’indiye indiyawa


gurgu guragu

kunci kumatu

turke turaku

murhu murahu

murfi murafu


garma garemani

karfasa         karefashi

garwa garewani

fartanya faretani


damtse        damatsa

gunki gumaka

gwarzo gwaraza

kurtu kurata

kwarto kwarata

kwiɓi kwiyaɓa

ƙarfe ƙarafa

ƙirgi ƙiraga

ƙirji ƙiraza

sisi         siyasa

sirdi sirada


layi        layuyyuka

tsauni tsaununnuka

rami ramummuka

fata        fatattaki

gida gidaddaji

gawa gawawwaki


jaka jakankuna

magani         magunguna


gyara gyare-gyare

rubutu rubuce-rubuce

kuka koke-koke

fita         fice-fice

tambaya tambaye-tambaye

shiga shige-shige

kame kame-kame

sata         sace-sace

gurza gurje-gurje

roƙo roƙe-roƙe

taɓa taɓe-taɓe

shure shure-shure

aiki         aikace-aikace

wanki wanke-wanke

aski         aske-aske

kwas kwasakwasai

kure kurakurai


ajiyayye         ajiyayyu

ambatacce ambatattu

asararre asararru

ashararre ashararru

aurarre aurarru

bankaɗaɗɗe bankaɗaɗɗu

bayayye         bayayyu

binnanne binnannu

birkitacce birkitattu

biyayye         biyayyu

bokaɗaɗɗe bokaɗaɗɗu

buƙatacce buƙatattu

busasshe busassu

buɗaɗɗe buɗaɗɗu

cafaffe cafaffu

casasshe casassu

cakuɗaɗɗe cakuɗaɗɗu

camfaffe camfaffu

cetacce        cetattu

curarre curarru

cusasshe cusassu

cuɗaɗɗe cuɗaɗɗu

dafaffe dafaffu

dakakke         dakakku

dakatacce dakatattu

dakusasshe dakusassu

damamme damammu

daɗaɗɗe daɗaɗɗu

dirarre dirarru

dodadde dodaddu

fafakakke fafakakku

fahimtacce fahimtattu

fantsamamme fantsamammu

fararre fararru

farkakke farkakku

fasashsshe fasashsu

fasasshe  fasassu

fiƙaƙƙe fiƙaƙƙu

firgitacce firgitattu

fitsararre fitsararru

futacce    futattu

gafalalle gafalallu

gajiyayye gajiyayyu

gardamamme gardamammu

gasasshe gasassu

gawurtacce gawurtattu

ginanne  ginannu

gogagge  gogaggu

gotacce   gotattu

gudajje gudaddu

gurfananne gurfanannu

gurɗaɗɗe gurɗaɗɗu

gyararre gyararru

haguntacce haguntattu

haifaffe   haifaffu

halakakke halakakku

halitacce halitattu

hamshaƙaƙƙe hamshaƙaƙƙu

hananne hanannu

haramtacce haramtattu

harbabbe harbabbu

hargitsattse hargitsattsu

harɗaɗɗe harɗaɗɗu

hatsabibabbe hatsabibabbu

haɗaɗɗe haɗaɗɗu

hujajje hujajju

jarababbe jarababbu

jefaffe jefaffu

jemamme jemammu

jerarre jerarru

jinginanne jinginannu

jiƙaƙƙe jiƙaƙƙu

jirkitacce jirkitattu

jurarre jurarru

juyayye juyayyu

kafaffe kafaffu

kamamme kamammu

karkatacce karkatattu

kasasshe kasassu

keɓaɓɓe keɓaɓɓu

kewayayye kewayayyu

killatacce killatattu

korarre korarru

la’ananne la’anannu

lafaffe lafaffu

lalatacce lalatattu

lamintacce lamintattu

lanƙwasasshe lanƙwasassu

lasasshe  lasassu

lauyayye lauyayyu

laɓaɓɓe  laɓaɓɓu

liƙaƙƙe liƙaƙƙu

lotsattse  lotsattsu

makakke makakku

miƙaƙƙe miƙaƙƙu

mokaɗaɗɗe mokaɗaɗɗu

motsattse motsattsu

murguɗaɗɗe murguɗaɗɗu

murzajje murzazzu

musayayye musayayyu

ninkakke ninkakku

nunanne nunannu

nuƙaƙƙe nuƙaƙƙu

nutsattse nutsattsu

ƙararre ƙararru

ƙerarre ƙerarru

ƙonanne ƙonannu

ƙyamamme ƙyamammu

rantsattse rantsattsu

rarakakke rarakakku

rinanne  rinannu

riɓaɓɓe   riɓaɓɓu

rumamme rumammu

samamme samammu

sananne sanannu

saƙaƙƙe  saƙaƙƙu

shafaffe  shafaffu

sirkakke sirkakku

tafassshe tafasassu

tatacce    tatattu

tatsattse  tsatsattsu

tsimamme tsimammu

ɓallalle ɓallallu

ɓalɓaltacce ɓalɓaltattu

ɓatacce   ɓatattu

ɓoyayye  ɓoyayyu

ɓulalle ɓulallu

wahalalle wahalallu

warkakke warkakku

watsattse watsattsu

zautacce zautattu

zamamme zamammu

zananne zanannu

zargagge zargaggu

zaɓaɓɓe  zaɓaɓɓu

zuƙaƙƙe  zuƙaƙƙu


zance zantuttuka

zaɓe zaɓuɓɓuka

kaya kayayyaki

gawa gawarwaki

daji  dazuzzuka

mashi masussuka

sule  sulalluka

sanda sanduna

layi  layuyyuka

batu batuntuna

tsari tsarurruka

magani   magunguna

ciwo ciwuwwuka

cuta cututtuka

gashi gasussuka

launi laununnuka

biri  birurruka

doki dokuna

jaki  jakuna

taro tarurruka

shafi shafuffuka

jari   jarurruka

kamfani  kamfanunnuka

hatsari hatsarurruka

rami ramummuka

ido   idonduna

rigima rigimammu

kabari kabarurruka

dutse duwarwatsu

gari  garuruwa

tsauni tsaununnuka

takara takarkaru

dama damammaki

baki bakunkuna

shagali shagalgula

zane zanunnuka

ƙuraje ƙurarraji

tabo tabunbuna

ƙwaro ƙwarurruka

ƙwauri ƙwaururruka

layu layuyyuka

hatsari haɗarurruka


Manazarta 

Fagge, U.U. (2013) "Ƙirar Kalma A Hausa." Samaru, Zaria, Jami'ar Ahmadu Bello.

Bargery, G.P. (1993) 'A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary; 2nd Edition. Zaria, ABU Press Limited.


Monday, August 18, 2025

HAMZA DAWAKI: GWARZON GASAR BASHIR TOFA 2025



 

HAMZA DAWAKI: GWARZON GASAR BASHIR TOFA 2025


Daga Kabiru Yusuf 

Kamar yadda ya gudana, an bayyana labarin "Ilimi Kogi" na Hamza Sadiq Adam a matsayin gwarzon gasar Bashir Tofa tare da bayar da kyaututtukan a gasar. Shin wane ne Hamza Dawaki?


An haifi Hamza Sadiq Adam, wanda aka fi sani da Hamza Dawaki, a fagen rubutu, a unguwar Dawakin Dakata, Ƙaramar Hukumar Nasarawa, a 22/02/1980. Kuma yanzu yana zaune da iyalinsa a unguwar Rangaza. 

Ya yi karatun allo a makarantun Malam Abdullahi da Malam Bahari da Malam Umar Basakkwace. Ya kuma yi yawon almajirci a ƙauyukan Daɗin Duniya da Tsalle da Ancau. Sannan ya yi karatun fiƙihu da hadisi da tafsiri da dangoginsu a wurin malamai irin su Malam Alfa Ma'aruf da Malam Zubairu Muhammad da Sheikh Aliyu Umar Chiromawa da sauransu. Tare da haka, Hamza ya ƙoƙarta ya riƙa zuwa makarantar boko. Har ya samu shaidar difiloma a Harsunan Hausa da na Turanci, a makarantar CAS, da ke titin zuwa filin tashin jirgin sama, a nan Kano. 

Hamza ya fara gwada rubuce-rubuce tun yana yaro ƙarami. Kuma a 2004 ya samu nasarar buga littafi mai suna Tubali, a lokacin yana aji biyar a makarantar sakandare ta Kawaji. 

Hamza ya halartar bitoci da tarukan ƙara wa juna sani a kan rubutu da dama, ciki har da Ibedi International Writers Residency, a Ibadan. 

Sannan ya samu nasarori a gasar rubutu da kyautuka da dama; kamar a gasar Gagara Gwari (ta waƙa) ta Taskar ALA 2012 sai gasar gajerun labarai ta Makarantar Malam Bambaɗiya, Jihar Kaduna 2014. Da gasar Labarun Yaƙi da Fatara, ta Pleasant Library Katsina, a shekarar 2017 da gasar Waƙoƙin Rashin Tsaro, ta Jami'ar Ɗanfodiyo, Sakkwato, 2021. Da sauransu.


Me labarin "Ilimi Kogi" ya ƙunsa?

Labarin wata jarumar mace ce, wadda suka rabu da mijinta, bayan sun haifi yaro ɗaya. Suka ɗauki shekaru suna zuwa kotu da mijin, a kan ta ba shi ɗan, ta hana. Alhali ita ba ta da ƙarfin samar wa yaron ingantaccen ilimin zamani. 

Don cike wannan giɓin, ta kasance takan fita da yaron, su bar unguwarsu. Wani lokacin su shiga gonaki, ta yi masa nuni da rayuwar tsirrai da ta dabbobi. Cikin hikima ta koya masa wani darasi. Misali, ta kwatanta masa yadda bishiyar giginya ta janye 'ya'yanta, can sama. Ba ta ba wa kowa, kuma kullum cikin jifan ta ake. Sai kuma bishiyar mangwaro, wadda ta bar 'ya'yanta a ƙasa-ƙasa, kusa da mutane. Suna tsinka ba tare da wahala ba. Sannan ta nusar da shi cewa, haka mutum mai rowa yake shan wahala da baƙin jini a cikin mutane. Kuma abin sa ba ya albarka.  Yayin da mai yawan kyauta ke samun farin jini, kuma kayansa ya yi albarka fiye da na mai rowar. 

Haka dai da sigogin darussa makamantan waɗannan ta ci gaba da koyar da shi, har zuwa lokacin da ta yi tsammanin yaro ya yi wa zaman duniya  kyakkyawar fahimta. Sai ta umarce shi cewa, duk ranar da suka koma kotu, ya ce shi babansa zai bi. 

Yayin da suka koma kotun ne, yaron ya amince da bin uban. Ya kuma  bayyana irin sigar da take bi don koyar da shi. Sai duk mutanen kotun suka cika da mamaki da irin hikima da jajircewar da ta nuna wurin koyar da shi! Har dai daga ƙarshe alƙalin da kansa ya nemar wa mijin biko. Ita kuma ta amince, aka mayar da auren nan take!

Alƙalancin Gasar Rubutu

 Alƙalancin Gasar Rubutu Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkay...