A short story
ASARAR SO BAYAN AURE
Kabir
Yusuf Fagge (Anka)
Zuwa ga
masoyiyata matata, Rukayyatu
Da fatan
kina cikin koshin lafiya kamar yadda na bar ki.
Kafin in
kai ga bayyana miki dalilan rubuto miki wannan wasika, zan fara da ba ki hakuri
dangane da kaurace miki da na yi na kwanaki biyu, alhalin kina amarya ta wata
biyu da kwanaki takwas a gare ni, alhalin kuma ina garin. Wannan ya faru ne ta
dalilin amfani da wata kissa ta wani bawan Allah da ya kauracewa matarsa saboda
gallaza masa da take yi, wanda kauracewar tasa gare ta, ta kawo masa mafita,
matar ta gane kurenta suka sasanta junansu suka zauna lafiya.
To
dalili na farko, na rubuto miki wannan wasika ne domin in yo miki karatun baya,
karatun haduwarmu da yin soyayyarmu tsawon shekaru biyu da watanni, kafin kuma
in hade da zaman aurenmu na watanni biyu da kwanaki takwas.
Ya
zinaren rayuwata cikon numfashina (sunan da nake gaya mata kenan a baya) idan
ba ki manta ba mun fara haduwa wata ranar Litinin a kofar makarantar ku wato
F.C.E. wanda tun daga kallon juna da murmushin alfarma da muka yiwa juna,
zukatanmu suka amince da samun dacen amintakar soyayyar juna, wanda zukata suka
kasa hakkuri a lokacin har sai da muka yi sauyin kalaman neman yardar soyayyar
juna, sai da muka samu sannan hankulanmu suka kwanta, soyayya ta kullu a
tsakani.
Daga nan
ya zumar zuciyata (daya sunan da nake gaya mata) soyayya ta kankama kamar yadda
ki ka sani, ta kai ta kawo kin zama ni, nima na zama ke kamar yadda muke fadawa
juna, kuma zukatanmu suka amince da hakan. Mun kasance a al'amura kamar haka:-
-Tsawon
shekarun nan da watanni ba mu taba gaza ganin juna ko jin muryar juna ba na
tsawon awa ashirin da hudu (kwana daya), idan haka ta faru har rashin lafiya
muke yi, kamar yadda ni da ke muke fadawa juna, in har ba karya muke yiwa juna
a lokacin ba.
Sau tari
a wancan lokacin ba ma wuce awa daya ba tare da daya ya kira daya a waya ba, ya
ji halin da ya ke ciki, idan na farin ciki ne mu taya juna, idan na bacin rai
ne mu damu, haka nan sakon na soyayya na waya (text message) baya yankewa.
Idan na
zo gidan ku muka hadu ba ma son rabuwa, sai da kyar kuma sai dole, wani lokaci
har kuka muke yiwa juna, idan muka rabu din kamar ba mu rabu ba, hankulanmu na
ga juna, muna yin waya ko sako, ga hotunan juna mun sa a gaba muna kallo, kuma
idan an yi barcin ma mafarkin juna ake yi. Idan na farka daga barci ba na fara
yin magana da kowa sai ke, kamar yadda ke ma ba kya iya magana da kowa sai ni,
kin zama ni, na zama ke.
-Mun
zamo masu gayawa juna kalaman soyayyar da muka gamsu duk duniya babu mahalukin
da ya taba gayawa wata ko wata ta taba gayawa wani. Na ce "ke ce
rayuwata" ke ma kin ce "ni ne rayuwarki," mun ce muna kama da
juna saboda soyayya. Na sha siffanta kyawunki da babu wata 'ya mace a duniya da
ta kai ki kyau, na sha siffanta ki da Balarabiya alhalin kina Bahaushiya. Duk
da kina wankan tarwatsa amma na sha cewa kin fi madara fari, nakan gwada
haskenki da hasken wata daren goma sha hudu ko sha biyar. Haka kema ki ke min,
ki nuna na fi kowa, kuma mu yarda da hakan a zuciyarmu.
-Kalaman
soyayyar da na sha gaya mikin sun fi malala gashin tinkiya, musamman idan ki ka
yi la'akari da wasikun da na aiko miki ba su da adadi, ki duba littattafan
kalaman soyayya da na cika na turo miki, tun ina kirga dari biyu da tamanin a
shekara guda, har lissafin ya kwace min. Kema na ki suna nan jibge a turakata.
Ba a batun katunan ‘happy sallah, happy maulud, happy Rajab, happy candy, happy
birthday, happy valentine’, happy kaza da kaza. Fulawoyi, zobba da ire-irensu
ba a magana.
-A bangaren
kyauta kuwa duk wani abu da idanuna ya ga kyawunsa, kamar sutura, takalma,
littattafai, da sauransu sai na siyo na kawo miki, haka kema duk wani abu da na
gani na ce ina so sai kin bani, idan na zo wurinki na ce ina son shan ruwa, to
ruwan roba da lemon kwali ki ke kawo min na sha. Idan kuma na ce zan ci abincin
gidanku, to kaji da wainar kwai za ki kawo mini na ci.
Kai
abubuwan dai gasu nan jimgin wasu ma na dade da mantawa.
Hankulanmu
ba su kwanta ba sai ranar da aka ce ga shi an daura mana aure, inda rayuwa ta
ci uban ta da, farin ciki da begen juna kamar a garemu aka fara yinsu, kullum
kamar ma hadiye juna, har tsawon sati uku, inda ko waje bana lekawa duk abin da
nake so sai dai in buga waya a kawo min har cikin gida.
A tsawon
sati ukun nan muna like da juna saboda soyayya, ko waya bana son a bugo min. Ya
cikon numfashina na san ba za ki manta irin tarairayar da ki ke mini ba, kamar
wani jariri, kafin in tashi daga barci kin yi min daddadan girki, kin hada
ruwan wanka, kin yi komai domin ni, ki bani abinci ki shayar dani, abin ba a
cewa komai.
Ba zan
manta ba ranar da na fara fita har kuka muka yi saboda zamu rabu da juna na dan
lokaci, wanda idan na fita karfe daya na rana, nakan dawo karfe hudu da kwata.
Yau da
gobe asarar mai rai, wata daya da 'yan kwanaki takwas ko tara ne? Na manta,
amma na san ba a kai kwana arba'in ba, lamarin ya fara sauyawa, ban san dalili
ba, ko gajiya da juna ne, ko me ya faru, Allah masani.
A wannan
lokacin da safiyar wata Talata na tashi ina shirin in ga kin gabato gareni da
gaisuwa da batun wanka ko abinci kamar yadda ki ka saba, ashe kina can kina
barci abin ki. Na je gare ki, na tashe ki, da kyar ki ka tashi. Sannan a
lokacin na maku da yunwa kafin ki kawo kalacin, wanka kuwa ni na riski ruwan a
bandaki maimakon da, da ki ke kama hannuna ki kai ni, in yi.
Al'amura
dai suka fara kwabewa, suka kwabe din, ba murmushin nan da ki ke yi min na
soyayya, babu kallon kauna bare kallon kirki, babu tarairaya babu damuwa da
juna. Na san dai babu wanda ya zugaki a kan haka, kuma babu batun ko kin daina
sona ko kin gaji da sona, to mene ne ya faru, mene ne matsalar? Ko kuwa maganar
nan ce da Hausawa ke cewa soyayyar shekaru hudu a waje (ta saurayi da budurwa),
soyayyar watanni hudu a gidan aure?
Idan ko
haka ne kaiconmu, soyayyar saurayi da budurwa ta fi ta mata da miji karko!
Lallai mun yaudari kanmu. Abin abin tsoro ne, abin mamaki. A zahiri ni kaina a
lokacin muna soyayyar saurayi da budurwa a lokacin nake jin soyayya muke a
zuciyata, da muka yi aure kuma ban yi tunanin wata soyayya ba, wannan kuma
kuskure ne, wanda a lokacin ne (lokacin da muka yi aure) ya kamata in san yanzu
za a yi soyayya, a baya sharar fage aka yi.
A zahiri
a lokacin muna soyayyar saurayi da budurwa, ina matukar dokinki, ko sunanki na
ji sai na ji fari a raina, amma da muka yi aure na nemi wannan dokin da halin
na rasa.
Kamar
yadda ki ka sani ya matata masoyiyata, da tafiya ta yi tafiya a aurenmu kin
shiga raina min wayo, ki ka fara nuna rashin damuwa da ni, ki ka fara wulakanta
ni da gasa min aya a hannu, duk wani hakkina kika daina ba ni a cikin dan
lokaci.
A da na
sanki da daukar wanka da cancara kwalliya da sa turare kina kamshi, amma daga
baya wani lokacin har tsami ki ke yi saboda rashin wanka a kan lokaci bare yin
kwalliya.
A da
(lokacin kina gidanku, da kuma farkon aurenmu) ki kan yi min murmushin kwantar
da hankali da dariya mai kyau, amma yanzu kodayaushe a turbune ki ke, fuska
kamar ta shanu.
Kikan
gaida ni da yi min sannu a da, kikan killace kayana a da amma a yanzu duk kin
daina.
Anya a
lokacin da muke soyayyar saurayi da budurwa ba mu yaudari junanmu ba? Anya ba
mu shiga duhu na rashin sanin cewa soyayyar samartaka shimfida ce a kan
soyayyar aure ba. Kamata ya yi mu san cewa a aure shi ne tabbas, shi ne zaman
dindindin, shi ne karshen magana.
Ga shi
dai ta kai ta kawo ke da ki ke ta uku da nake so duk duniya, wato bayan uwa da
uba, amma kina matata kin sa na fita na bar gidana. A zahiri ina kan matsayi
guda biyu, idan har ni da ke ba mu gane cewar yanzu ne a matsayinmu na mata da
miji zamu yi soyayya ta har abada ba, mu sabunta soyayya nagartacciya ba, to
zan kara nisa, in yi nadamar yin soyayya a inda ba a nan ya kamata in yi ta ba,
wato soyayyar saurayi da budurwa.
Ina
fatan ki yi nazari, ki dauki mafita a garemu, ki gane yanzu ne ya kamata mu yi
soyayya ta kwarai, mu tarairayi juna, ki yi min murmushi, ki yi min dariyar
soyayya, ki yi min abincin soyayya, nima in yi miki.
Na gode,
masoyinki kuma mijinki.
No comments:
Post a Comment