Tuesday, September 18, 2018

A DALILIN GULMA


A DALILIN GULMA
(c) Deejah Sharubutu


Unguwarmu irin sabuwar unguwar nan ce ta amare, duk yawancinmu amare ne sai masu yara daya, biyu zuwa uku.

Washe garin da aka kai ni wajen goman safe na ji an kwankwasa min gida, na bude na ga matasan mata wadanda ba su gaza shekaruna ba dauke da murmushi a fuskarsu, don haka nima na saki nawa murmushin tare da fadin "Maraba, ku shigo." Na yi gaba, suka bi ni a baya, muka shiga falon.
Angon nawa yana zaune bai gama karyawa ba, tun kafin in nuna musu gurin zama kowacce ta yiwa kanta mazauni, tare da gaida maigidan. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa, ina kallon fuskarsa da yanayin da ya yi na nemu guri na zauna tare da gaishe su, suka amsa a sake kamar irin sun sanni, sai suka cigaba da hirar da suke wanda ban fahimta ba, gaba daya na dai fuskanci suna maida abinda ya wuce ne.
Daya daga cikinsu ta ce
"Au mun zauna, muna ta zuba daga shigowar mu ko gabatar miki da kanmu ba mu yi ba; makotanku ne nan, ni sunana Larai, gidana shi ne wanda yake kallon gidan ki."

Ta kusa da ita ta ce "Ni kuma Rakiya, gida biyu ne ya rabamu da na ki...".
"Ni kuma sunana Nafisa gidana yana daga dan gaba amman daga kofar gidan ki ana gano nawa."
Tana gyara zama ta ce "Ni kuma sunana Fatima gidana na daga daman naki."
Ta karshen ta ce "Ni kuma sunana Saratu amman an fi kirana da Maman Abul."
Duk ba wani gane bayanansu na yi ba, ta karshen ta ce "Na zaci ita na ji kukan yaro a kusa damu na ce ko nan kusa damu ne na ji yaro dazu yana kuka."
Ta biyu suka hada baki, "Wannan uwar girman kan ce zata shigo miki, bayan yanda take ji da kanta tana takamar ita ubanta mai kudi."
Saroro na yi ina kallonsu, da na kasa fassara irin kallon na su.
Wadda ta kira kanta da Fatima na ji tana cewa "Ai sai kin dage don bata da mutumci."
Ai sai na ji sun cafe sun fara sukar ta, ina ta jinsu cikin raina ina ashe sai na shirya. Ina shirin yin magana na ji angona yana kwalan kira 'Ramla! Ramla! Ramla!"
"Na'am." na amsa tare da duban su "ina zuwa dan Allah.".
Na shiga ciki, "Gani." na ce da dan risinawa kamar zai yi magana kuma sai ya ce "Fita zan yi, ki san irin maganar za ki dinga yi da mutane bana son surutu don Allah."....

*BAYAN NA ZAMA YAR GARI*
Ai ba a dauki lokaci mai tsawo ba na zama nima daya daga cikin su, ai tuni mun saba)m da zarar maigida na ya fita nima nakan fita in shiga makota na ai ta zuba, mu zagi wannan, mu soki waccan wanda rana dai-dai ne zamu zauna ba mu age Maman Abul ba, duk da ta yi kokarin ta ga ban yi sabo da wadannan 'yan unguwa ba, ta yi kokarin nuna min amman na ki sakin jiki da ita, saboda yanda suka 6ata sunanta a guna dan haka ta tattara ta kyale ni ta kama karatunta.

Nafisa ta gayamin ai Saratu muguwar barauniya ce in yi a hankula da ita.
Ni ko abin ya ban mamaki don haka sai nake gayawa Larai, ashe ta kwashe ta gayawa Saratu.

Mijina ya ji ana ta bugun gida da safe duk da ya saba ya yi kokarin ya hanani, sai in hau fushi ni zai rabani da masu kaunata, kullum kafin ya fita sai ya gindaya min kar in sake in fita, wuyarta ya sa kafa, yana fita ai zan fice in tafi yawon tsegumi.
Yana bude kofa na ji ana magana haka sama-sama zuwa can ya shigo ransa a bace ya ce sai ki "Dauko hijabi mu tafi"
"Ina zamu?"
"Ban sani ba." Ya fada da tsawa.
Hijabin na lalubo, shi kuma ya sauya kayan jikinsa ya yi gaba, na bi shi a baya.
Gabana ne ya fadi da gani 'yansanda mata guda biyu sanye da kayan aiki, na kalle shi, ya zuban harara da fadin "Shige mu je mana, ko ma mene ne ki je, ki ji mana."

Zuwanmu gun hukuma, na ga Saratu a tsaye tana cika tana batsewa, sai gabana ya sake faduwa, nan da nan jikina ya hau rawa.
Jim kadan aka karanto min laifina.
Na ce "Wallahi nima gaya min aka yi."
"Wa ya gaya miki?"
Na ce "Nafisa!"
Take aka ce aje a kira Nafisar.

Nafisa da ta zo ta ce ita fa sam ba ita ta gaya min ba, har da rantsuwa a dauko Alkur'ani zata dafa.
Nan dai mijina ya sa baki, aka kashe maganar. Muka zo gida, ya din ga yi min fada, hadi da nasiha, har ya dauke wuta na kwana biyu bai sauko ba, sai da ya ga alamun na yi hankali.
Ban daddara ba, aka kuma gaya min ai abinda ya sa Maman Abul bata shiga cikin mutane ai mayya ce ai ban yi mamaki ba,saboda na dada kwarewa a gun gulma na je ina ta fesawa.
Duk wanda aka tambaya, sai ya ce ni na fada, zance har ya koma mata.
Da rana tsaka aka zo da motar 'yansanda guda aka jefa ni a ciki, na yi wiki-wiki da ni.

Muka je, aka karanto min laifina na ce "Nima fa Rakiya ce ta gaya min."
Ita ma Rakiya da aka kawo ta, ta yi, ta rantsuwar cewa karya nake yi mata."
Mijina na tsaka da kasuwa kira ya same shi, ya taho, da ya zo, ya ji maganar bai ce komai sai bayan dan lokaci sannan ya ce "Duk abinda zaku yi mata, ku yi mata, ku tsare ta ba ruwana." Ya yi tafiyarsa.
Nan na saka kuka, ina kwala masa kira, ko jiyo ni bai yi ba.
Da ya koma gida, ya yi ta bai wa Baban Abul da Maman Abul baki su hakura a kashe maganar don Allah kar aje kotu. Da kyar suka amince.
Ina ji, ina gani haka na kwana a bayan kanta, na sha kuka da takaici da dana-sani ga laulayin ciki da nake fama dashi, har garin Allah ya waye ban rintsa ba, da safe aka kashe case tare da jan kunne mai tsanani.
MAI HALI BAYA FASA HALINSA
Ran nan kam dadin hira ya debe ni a majalisar da muka kafa ta unguwa bayan gidana na rabu da tawagar su Saratu na sake wata saboda sun mun munafurci.

Na kalli 'yanmatan da suka dawo daga makaranta su uku, babbar ce mace, maza na bin ta, babansu ne ya rufe motar ya shiga ciki.
Na dawo da kallo na gurin 'yan majalisar tamu na ce "Kai ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, ace tunda matar shi ta mutu ya ki aure, sai dai ya sa yara a gaba, kai sai dai in 'yar nan tashi yake nema, ba ku ga duk ta cika ba."
Wasu sun tofa ta su, wasu ba su tofa ba, na ga alamun tsoro ma suke ji, ashe wai soja ne!

Wayyo ni gulma bata yi ba, na manta ma da an yi maganar na dawo daga awo na ga motar sojoji a kofar gidana, nan da nan na ji gabana na faduwa, har na juya na ga an biyo ni, "Shiga!" Haka na ji an ce min, ba yanda na iya haka suka rattabani a ciki suka lula dani, sai dana kwana kusan bakwai ana hora ni sannan aka kinkime ni aka kai ni kotu!

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...