WACCAN MAKABARTAR CE BA TA YI MIN BA
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
W
|
ani mutum ne mai siyar da makara aka nemi ya kawo makara za a
siya, to da yake inda zai dauko makarar da nisa, sai hakan ya sa ya yi dare a
hanyarsa ta tafiya.Yana cikin tafiya dauke da makara a kai, sai ya hadu da
‘yansanda a hanya suka daka masa tsawa suna cewa “Daga ina kake haka?”
Sai mutumin nan ya kada baki ya ce, “Yallabai daga makabarta
nake.”
Daya daga cikin ‘yansandan ya harareshi, ya
ce “Daga makabarta da daddaren nan?”
Mutumin ya ce “E wallahi, ni gawa ne, waccan makabartar da
aka binne ni ne na ga bata yi min ba, shi ne zan sauya wata.”
‘Yansandan nan suka tsorata suka juya a guje, wani na karo da
wani.
No comments:
Post a Comment