Monday, September 17, 2018

Kaima Ka Dara: KA TURO MIN DA KUDI


KA TURO MIN DA KUDI

 
Wata rana wata budurwa ta zo wucewa a cikin taksi sai ta hango saurayinta a jikin ATM (wajen cire kudi na banki) yana zarar kudi, sai ta tsayar da mai taksi din ta bugawa saurayin nata waya, ta ce.

“Hello My Sweetheart ina cikin shaukinka, idan barci kake yi ka turo min da kyakkyawan mafarkinka, idan abinci kake ci ka turo min da tsokar nama idan hira kake yi ka turo min da kyakkyawan zance, idan a kasuwa kake ka turo min da tsarabar kasuwa, idan kuma a ATM kake ka turo min da kudi.”

Saurayin ya yi nishi ya ce, “Hmmmm, my lovely a toilet nake, ina kashi.”


No comments:

Post a Comment

MAKAHO MAI FITILA

MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...