KU TAYA SHI
Wani manomi ne mai suna Sule Kankan, ya sabi
fartanyarsa ya tafi gona don yin noma, yana zuwa, ya tattare hannun riga zai
fara yin noma, sai ya ji kamar daga sama an ce.
"KU TAYA SHI!"
Ya bude baki yana mamaki, kafin ya juyo da
hankalinsa, kawai sai ya ga an nome masa gonar. Ya tsaya yana mamaki, amma
cikin jin dadi.
Washegari Sule Kankan ya dawo gona zai yi shuka, nan
ma yana shirin fara aiki, sai ya ji an ce "KU TAYA SHI!" Take ya ga
har an gama yi masa shuka.
Sule ya cika kuma ya ci gaba da rayuwa cikin mamaki,
har zuwa lokacin yin huda, Sule ya nufi gona don yin huda, nan ma kafin ya fara
aiki sai ya ji an ce "KU TAYA SHI!" Sule yana tsaye aka yi masa huda
aka gama.
Abin mamaki har zuwa lokacin cire amfanin gona don
kaiwa gida, Sule ya zo don tattare amfanin gona ya kai gida, kawai sai ya ji an
ce "KU TAYA SHI!"
Hankalin Sule ya tashi lokacin da ya riski an kwashe
amfanin gonar gaba, ai take ya fashe da kuka yana fadin, "DON ALLAH KAR KU
TAYA NI!"
No comments:
Post a Comment