Saturday, September 1, 2018

Hausa Novel: BAR RAINA ALLURA...






New Hausa Novel





BAR RAINA ALLURA...



YA FITO KASUWA



Salamu alaikum Zaemah. Da fatan kina lafiya? Kin dawo lafiya? Zaki yi mamakin me ya sa na ce Hajiya ta bari sai kin dawo, ban tura miki tun kina can ba, to kin san karatun shekara daya ne, amma gani nake kamar shekara goma, Zaemah ki yi min alfarma wanda babu dan adam din da zai yi min sai ke.

Zaemah na san Haidar na son Kuhayla, yana boye min ne saboda kar raina ya baci, sannan yana boye min ne don kar abotarmu ta lalace, amma Zaemah kin san wani abu? Kin manta tun muna yara idan aka siyo mana abu Haidar yakan tsani abin? Sai daga baya ya fara so? Kin tuna lokacin da aka ce Haidar ya karbi jaka blue da Umma ta siyo mana? Ya tsani jakar har kuka sai da ya yi? Daga baya ya zo yana bala'in son jakar? Kin tuna lokacin da kuka hadu dashi? A Islamiya? Ya tsaneki? Baya son wani abu ya hadaki dashi? Amma daga baya fa? Har iyaye sun fara zumunci a tsakaninsu saboda kaunar da shakuwar da kuka yi, to Zaemah ban manta ba, Haidar tunda muka je, na dauki Kuhayla, na dauketa da niyyar idan na ajiyeta ba zan kara komawa ba, amma yadda ya tsaneta ya sani kokonto na yi tunanin zai cigaba da tsanarta duk ranar da ya ganta har ya zo, ya fara sonta, to kuma a halin da na ganta na san idan bamu nemi hanya ba lalacewa zata yi, sanadin Haidar ya sa na dauki nauyin kowace rana nake zuwa nake kulawa da ita na bata abin bukata don kar ta shiga halin da yayarta take son sakata.

Na yi ta kulawa da ita ina janyo Haidar amma yana kara gwada min tsanarta, bai taba tsanar 'ya mace kamar yadda ya tsani Kuhayla ba, hakan ya bani tabbacin zai sota har kololuwar rayuwarsa, duk abinda na yiwa Kuhayla ban taba sonta ba, na dai shaku da ita ne, na yi hakan ne don na samu Haidar ya canja, to Alhamdulillahi kafin na bar garin, na ga ya fara taimakawa, bai yi tunanin na san cewa shi ya gyara musu gida ba, kuma ban nuna mishi ba, da farko na bi hanyoyi na duk ban gane ba amma watarana na shiga dakinsa na ga files da komai har da hotunan Kuhayla, hakan ya tabbatar min da cewa lallai Kuhayla ta fara shiga ransa as edpected.

Ban yi niyyar kara masters ba, amma na yi hakan ne don na tafi, na bashi guri domin ya shaku da ita, na je don na bashi amana amma ya ki karba dama na san ba zai karba ba domin yana tsoron kar na gane yana sonta, amma na kiraki, na baki, don haka na tafi ne don na samu su sasanta kansu kafin na dawo, idan ya so sai na bayyana gaskiya.

Ina so ki taimaka, ki hadasu, su sasanta kansu, ina son Kuhayla da Haidar domin Kuhayla mace ce iya mace, Haidar kuma a yadda yake da zaben mace, ita ce zata yi maganinsa, ni from day one Rahma nake so amma Haidar ya hana, ya nuna min watarana zan iya bata mata rai, zai shafi abotarmu bai yarda zan iya kula da Rahma ba, kuma na san Rahma ma tana sona, don haka ki samu please ki yi min hanya, ki sa mata ido kar wani ya zo ya kwace min ita, I love her loads of bunch, to the moon and back, don haka Zaemah my trusted fund, ki taimaka, ki cika min alkawarina, na tafi amma fa zan dawo soon so ki samu, ki cika alkawari kafin na dawo.

Your friend truly Sadik



Rike papern ta yi, ta fara wani zazzafan kuka, kuka ta yi sosai wanda tunda take a iya wayonta bata taba wannan kukan ba, ta yi kuka sosai har kanta ya fara ciwo, a ranta ta rike alkawari tare da cewa "Ya Sadik na yi maka alkawari in sha Allah Kuhayla zata auri Haidar, in sha Allah babu wanda zai nemeta bayan Haidar. Duk taurin kan Haidar zan san yadda Kuhayla zata juya shi."





MAZA NEMI NAKA/NAKI A KASUWA




1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...