Tuesday, September 4, 2018

Short Story: BIRNI BA KAUYE BA


Short story



BIRNI BA KAUYE BA!

Labarin tafiyar Lado Gandameme Birni

Kabiru Yusuf Fagge (Anka)



Lokacin da Lado Gandameme ya fito daga bukkarsa ta kwana dauke da buhun algararar tsummokaransa aka, ya yi daidai da shigowar mahaifinsa, Malam Jamo. Uban da dan suka yiwa juna kallon-kallo, kafin uban ya ce.

‘Ina kuma za ka je da tsummokara haka?’

Cikin gaudanta Lado Gandameme ya ce ‘Ni tafiya zan yi wallahi.’

Malam Jamo ya ce ‘E, na ji tafiya za ka yi, to ina za ka je din?’

‘Birni.’ Gandameme ya fada yana kuma kokarin gifta mahaifin nasa.

Malam Jamo bai gajiya ba, ya riko gefen tsumman rigar ‘yar sharar da ke jikin Lado, har sai da rigar ta dan yage. ‘Amma ai ko za ka yi tafiya, ya kamata in san yadda aka yi, aka haihu a ragaya ko, na san dalili.’

Lado Gandameme ya washe baki da wani gurnanin abu da shi yake zaton dariya ce, ‘E wallahi Jamo ka gano…To, to ni dai yanzu nan da na yi barci na yi mafarki ga ni a birni, na shiga mato na hya hyayi na ga labi mai dabe, na je wajaje da yawa. Hyi ne na hye bari kawai in tafi binni wallahi.’

Mamaki bai yawaita ga Malam Jamo ba, domin ya san irin gaudanta da sokonci da wawanci na dan nasa, to bare kuma ga kauyanci, in banda haka ta ya ya daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zaki? Daga mafarki sai tafiya, ya kalle shi.

‘Kai wane irin dan balama ne, daga mafarki sai daukar hanya? Idan da don ta mafarki ne da tuni ai na zama Dagacin wannan kauye, ko kuma ai da tuni uwaka Uwale ta je Makka…’

Lado ya katse mahaifinsa ya ce ‘Tsaya ka ji Jamo, na hya maka Yasin, Alkur’an sai na tahi, yaushe zan tsaya a nan ina kallon ruwa kwaddo na sarkafa min kafa, alkur’an tahiya zan, kallo fa Muhutari dan Dagaci yadda ya zama saboda yana zuwa binni.’ Ya aza kayan bisa ka, ya fara tafiya buguzum-buguzum, ya nufi waje yana fadin sai ya dawo.

Malam Jamo ya bishi da kallo kawai yana jimanta abin, ya san halin dan nasa idan ya ce sai ya tafi, to kawai a kyale shi ya tafi din a zauna lafiya, domin idan aka hana shi, to babu kwanciyar hankali saboda halin gaudanci da wawanci.

Lado wani yaro ne da aka yi a kauyen Dankanjiba, mai shekaru sha takwas, gaude ne kuma gandandan da shi, domin Allah ya halicce shi da abki, ka yi zaton dankalin tamanin ne. Fari ne, mummuna, hanci kamar Botorami, baki sakatoto. Allah ya horewa Lado Gandameme abubuwa uku, gaudanci, wawanci ga kauyanci. Idan ya yanko magana sai ka ce da adda aka yanko ta, idan ya yi abu sai dai a rintse idanu. An taba kai shi kara wajen Dagacin kauyen a kan ya fiye dukan yara da karye wa mutane tumu, Dagaci ya sa a yi masa bulala. Lado Gandameme ya tubure cewar ba a isa a doke shi ba.

Abin ya baiwa kowa mamaki, domin a da idan aka kawo shi a kan wani laifi idan aka ce a doke shi ba ya yin musu yake bude baya a tsuttsula masa tsabga, ya tashi, ya kakkabe jiki ya tafi abinsa. Don haka Dagaci ya tambaye shi da cewa, “Lado me ya faru yau kuma?’

Lado yana kada baki sai cewa ya yi, “Alkur’an gano wa na yi ba ka da kirki. Kawai ni don na bugi yara, kuma don na ci tumu na zakkar daji sai ka sa a rinka bugu na, kai kuma da ka ke sa wadannan kattan wofin su rinka bugun mutum fa, kuma ina gani kana sa a kawo maka tsaba ta mutane ai…’

Maganar ta baiwa yaran Dagaci haushi, suka taso masa. Dole Dagaci ya hana su, ya ce su kyale shi, ya sallame shi. Ya zai iya da sauran wuta, in ji kishiyar konanniya.



Can a bisa hanya, Lado Gandameme ne dauke da kayansa a ka, ya bi kan turbar da za ta sada shi da tashar motar zuwa birni. Idan ka ga yawan tafiyar da ya yi daga kauyensu zuwa tashar Gwadabawa, za ka yi mamaki, kilomitoci bakwai ya shanye a kasa, bai taba zuwa tashar don hawa mota ba, sai dai yawo da ya taba kai shi sau daya, bai taba hawa mota ba, sai dai jaki.

Wata tsohuwar kiya-kiya, karama ce ta rage a  tashar ba ta cika ba, Lado ya je ga kiya-kiyar ya shiga. Karen motar, ya yi – ya yi Lado ya ba shi buhun tsummokaran a sa masa a bayan motar, wajen ajiye kaya, Lado ya ki yarda, ya ce, “Na ki a rabani da kayana, tun a nan za a yi min binnin, wane dare ne ga jemage bai gani ba, kar muke ganinku macuta.” Dole aka kyale Lado ya shiga gaban motar dauke da buhun kayansa a hannu.

Mota ta rage saura mutum daya ta cika, can sai ga Dagaci ya zo shi ma za shi birni, matukin motar da karen mota lallami Lado Gandameme ya dawo tsakiya ya bai wa Dagaci wuri a gaba ya zauna, Lado ya ki, sai da kyar da sudin goshi ya yarda, ya dawo kujerun tsakiya ya zauna. Bayan da kowa ya gama shiga za a tafi, sai kowa ya yi gaisuwa ga Dagaci a motar nan amma banda Lado.

Karen mota ya yi wa Lado rada ya ce “Lado ba ka gaishe da hukuma ba.”

Lado da ya tashi mayar da amsa, sai ya bude baki kowa yana ji ya ce “Ni kam ba zan gaihe da Dagaci yanzu ba, sai Allah ya kaimu binni nan da mako guda. Ka san shi tun da yana gidan gaban mato sai ya yi mako da zuwa kafin mu mu isa.”

Kowa ya fahimci nufin Lado, suka yi gum domin kar su jawa kansu. Shi ma Dagacin ya fahimce shi, kawai ya yi shiru ne kar ya ja ya kuma yi masa kwaba.

Amma duk da haka Lado bai yi shiru ba, ya ce “Ka san na gaba shi ad da wauta, tun da ya ki bin sahu ga ‘yan uwanai, ya ware.”

Mota ta lula, masu barci suka fara, masu kallon titi na yi. Barci ya dauke Lado  Gandameme, a lokacin kunnuwan fasinjoji suka shiga tashin hankali domin wani gurnanin munshari da ya fara dole a rasa nutsuwa, ji ka ke “Gaarrrg! Girrrg!! Garrrgg!!”

Mutanen da ke waje, manoma ko makiyaya ko matafiyan da motar ke wucewa ma suna juyo wa bare na cikin mota. Wani manomi da motar su Lado ta wuce shi ya dubi dansa da ke zaune kusa das hi, ya ce “Tukuro ka ga wata mota can mai injin jirgin kasa.”

A cikin motar wadanda suka riga Lado yin barci suka tashi, direba ya yi kamkam da sitiyari don kada gurnanin Lado ya sa su yi hatsari, sannan ya yi gefe ya tsaya, kana ya sa aka tashi Lado, ya ce “Gaskiya yaro ko dai ka daina barcin nan naka ko kuma ka hakura mu ba ka kudinka, mu sauke ka a nan.”

Lado Gandameme ya yi wura-wura da idanun barci, yana kallon waje ya tabbatar a jeji suke ba su zo birni ba, ya dubi direba ya ce, “Taudan uwa, kana nufin ka baro ni da kauye ba ka ijje ni zuwa binni ba kuma ka ajje ni a dawa, Alkur’an ko Dagaci bai isa yi min wannan danyen aikin ba.”

Direba ya yi dif, kafin daga baya ya ce “To za ka daina barci bare ka yi gurnanin hana mu kwanciyar hankalin ko kuwa?”

“E to zan gwada yin haka.” Cewar Lado yana hararar shi.

Mota ta kara diba bisa kan kwalta. Amma sai al’amarin ya sauya salo, Lado ya koma yin kallo, sai ka ga ya zura kansa ta tagar motar yana kallon bishiyoyi suna gudu, ya kasa yin shiru, ya buge da surutu. Idan ya zura kai, sai Karen mota ya mayar da shi. Da abin ya yi yawa, sai Lado ya ce da Karen mota “Yaron mato in yi maka tambaya mana. Do Allah su kuma bishiyoyin ga ina suka nufa, ko suma binnin za su?”

Karen mota ya yi dariya “Me ka gani Lado?”

Lado ya ce, “Gani na yi suna ta falfala gudu kamar yadda mahaukacin mai motar nan namu ke yi da mu yana son wuce su.”

Yaron mota ba shi da amsa. Kafin ma ya yi magana direba ya ce masa ya karbi kudin motar kowa, amma ban da kudin Dagaci.

Fasinjojin suna rinka dauko kudi suna biya, amma Lado ya ki, aka yi – aka yi ya ce shi sam ba zai biya ba. Direba ya tsaya da mota, ya dube shi ya ce, “Me ya sa ba za ka ba da kudin mota ba?”

Lado ya ce, “Ka ji ka dan nema da batu, kai fa ka ce kada Dagaci ya biya kudin mato din nan, kuma a bisa kujera ta yake zaune, ka ga ai kudin kujera ta ce, ka ce ka da a bada, to don mi zan biya kuma ni da kujera ta.”

Haushi ya ishi Dagaci ya cewa direba su je kawai shi zai biya. Haka direba ya ja mota suka ci gaba da tafiya.

Mota ta fara shiga birni, suka fara riskar motoci suna wuce su da gudu ko su gifta su, a nan hankalin Lado ya tashi yadda yake gani mota na zabgowa da gudu, suma suna gudun kamar za su hadu, sai ya ga kowacce ta wuce. Hankalinsa dai bai kwanta ba duk da rintse ido da yake yi, ya daga kafafu sama wai zai kare. Wata tirela tana hon tana gunji da ta danno da gudu daga daya bangaren, Lado ya kurma ihu, wanda sai da kowa ya gigita a cikin motar, karen mota ya yi saurin duban Lado ya ce, “Me ya faru kuma?”

Lado ya nuna waje ya ce “Haka kawai ahe, idan za a zo binni sai an yi wasan karo da ganganci da ran mutane. Haka kawai mato za ta taho wata ta taho kamar za a kwamutsa a ragargaje kuma sai a kauce!”

Mutanen mota suka yi dariya, sannan karen motar ya yi kokarin kwantar masa da hankali da cewa ba komai. Ya dai hakura, amma idonsa daya a rufe daya a bude wai shi ba zai kalli gangancin da ake yi ba.

An fara shiga birni sosai, Lado ya fara ganin hayaki, da sauyin iska daga mai kamshi mai dadi ta bishiyoyi zuwa ga mai yaji mai zafi ta injina da gas ko fetur.

Nan surutu ya barke daga bakin Lado kamar an sunce kan famfo, idan ya ga wani gida sai ya yi magana ko mota ko wani abin. Da abu ya yi yawa sai ya fara kirga gidaje da motocin da suke wucewa, tafiya ta kara nisa sai ya fara kirga fararen motoci daban bakake daban jajaye daban, haka shudaye, wai yana son ya bambance wadanda suka fi yawa. Gidaje kuwa dogaye da gajeru yake bambancewa, haka babura masu goyo da marasa goyo.

Da suka shigo birni sai wasu suka fara sauka don sun zo inda ya kamata su sauka din, duk wanda ya sauka da dariya yake sauka. Lado ya yi tunanin ko shi ma ya sauka, amma sai ya ga cewar ya kamata ya ga karshen birni kuma ya more dadin mota.

Da direba ya ga ya sauke wasu fasinjojin, sai ya fara daukar wasu don ya kara samun kudi. A cikin haka ya dauki wani Dancaburos mai shan taba da ya ke zukar abar sa a cikin motar kusa da Lado.

Abin ya ishi Lado, ya dubi mai shan tabar nan ya ce “Malam kai ma mato ne kai ko baburi ne ko kuma murhu ne na ga kana hyan wuta kana fitar da hayaki kana damunmu?”

Dancaburos ya ce “Ni uwaka ne.”

Abin ya ba Lado haushi, ya daga wafcecen hannunsa mai kama da faranti ya wankawa Dancaburos mari. Tabar ta yi sama, ta fada waje. Suka kaure da rigima, dole direba ya tsayar da motar a gefe suka firfito, karo da dama kenan Lado na sa direba ya tsaya a dole.

Dancaburos ya tubure sai ya kai Lado wurin ‘yansanda don ya yi a bi masa ba’asin kumbura masa kumatu da ya yi.

Lado ya dubi karen mota ya ce “Yaron mato su waye ‘yansanda kuma?” Nufinsa idan ya ji zai je sai ya je.

Karen mota ya ce “Yan doka.”

Tab, Lado fa yana da labarin ‘yan doka sune masu wuri kulle mutum, da harbe mutum. Shi ko me ya kai shi daga baro kauyensu a yi shela an harbe shi. Kawai sai ya fashe da kuka ya dubi Dancaburos ya ce “Alkur’an ba za ka kaini ga ‘yan doka ba, sai dai gurin Dagaci ga hyi nan. Ko banza ma gahi bai tawo da kattai masu tsabga ba.”

Abin ya baiwa kowa dariya har Dagaci, wanda da kyar ya baiwa Dancaburos hakuri, ya hakura amma bai koma cikin motar ba. Su Lado suka shiga, suka fara tafiya karen mota ya ce “To ai yanzu sai ka yi mana shiru ko don a nan duk abin da mutum ya yi ‘yan doka ake kaiwa shi.”

Lado ya kama baki, alamu babu sauran magana. Sai da kowa ya sauka daga motar, direba ya gaji da yawo da Lado ya ga alamun ba zai sauka ba, kawai sai ya nemi wuri ya tsaya, ya ce “Yaro nan ne inda za ka sauka.”

Lado ya sauka, direba ya ja ya tafi. Lado yana ajiye kayansa a kasa don hutawa wasu ‘yan dako murtuka-murtuka guda biyu suka yo wajen da gudu suna rige-rige don daukar dako. Lado na hango su ya dadimi buhun tsummokaransa ya saba a kafada, ya diba a guje, yana dafe hula.

‘Yan dakon nan suka lura da abin da ya faru, suka rinka dariya, daya daga ciki ya ce, “Da alama wannan tumu ne, saukar yau.”

Lado yana maka gudu, wani yaro yana tafiya, ya gan shi ya dauka barawo ne aka biyo, kawai sai ya daga murya ya shiga cewa “Barawo! Barawo!!”

Ai kuwa sai wasu ‘yan gaza-gani, ‘yan da a-bani-labari, suka rufa wa Lado baya da gudu suma suna cewa “Barawo! Barawo!!”

Lado yana gudu takataf! Takataf!! Takataf!!! Yana waiwaye, sai ya ga kamar rabin mutanen birnin ne suka biyo shi. Ya kurma ihu, ya kara fallawa. A ransa yana cewa “wai me ya kawo ni binni ne? Daman hakan binni yake, ana cewa ana jin dadi ashe wajen tashin hankali ne.”

Ku biyoni wata mai zuwa mu ji labarin rayuwar Lado a birni.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...