Saturday, September 22, 2018

KABIRU YUSUF YA LASHE GASAR RUBUTU TA PLEASANT DA MMB 2018



A ranar Juma'a 21-9-2018 a dakin karatu na PLEASANT LIBRARY AND BOOK CLUB dake Kaita Road jihar Katsina aka bayyana Kabiru Yusuf Fagge (wanda aka fi sani da Kabir Anka) a matsayin wanda ya lashe gasar gajerun labarai ta shekarar 2018.
Anka tare da sauran marubuta sun karbi kambin gasarsu tare da kyautuka nan take a hannun manyan shaihunan malaman da suka halarci taron.
Tun da farko Malam Mai Bazazzagiya ne ya bude taron da addu'a, sannan kai tsaye aka wuce da Jawabin Maraba ga bakin da suka halarci bikin bayar da kyautukan, inda Dr Abu Sabe Malami a Jami'ar Katsina ya tarbi bakin da maraba.

Shaihun Malami, Professor Ibrahim Malumfashi ya gabatar da makasudin taron, inda ya bayyana cewar abubuwa biyu zuwa uku ne suka assasa wannan gasa ta rubutu, na farko dawowar Makarantar Malam Bambadiya, wanda shi Professor din yake jagoranta da kuma irin ayyukanta na kokarin kyankyashe jajirtattun kuma gwarazan marubuta da rubuce-rubuce a kasar Hausa da arewacin Nijeriya. Sannan sai goyon baya da hadin gwiwa da aka samu daga wannan shahararriyar cibiya ta Pleasant karkashin jagorancin shugabanta wato Engr. Dr. Muttaka Rabe. Malamin ya sha alwashin in sha Allah yana fatan hakansa ya cimma ruwa.
A nasa jawabin, shugaban PLBC, wato Engr Dr. Muttaka Rabe Darma ya bayyana wannan taro a matsayin wani danba na:- Samar da hanyoyi da mafita daga tarnakin da ke damun al'umma (wato social issue) - Da kuma samar da fikira, fasaha da basira musamman ga matasa Hausawa. Sannan kamar yadda cibiyar take da wannan burin, Engr. Dr. Muttakan ya yi alkawarin jajircewa don cimma wannan buri da manufa tasa.
Daga baya Prof. Malumfashi ya sake dawowa, ya yi 'yar takaitacciyar lakca a kan sirrin gudanar da gasar rubutu da matakan cin nasara. Duk da rashin lokaci, Prof. din ya kawo wasu 'yan hanyoyi a takaice da zasu taimakawa duk wani marubuci da yake da sha'awar shiga gasa, kuma har ya ci.
Bayan 'yar takaitacciyar lakcar Professor Malumfashi, an fara karramawa tare da mikawa kyaututtuka ga gwarazan marubuta 15 da suka samu nasara. Kafin a fara mika kyautukan, Prof. Malumfashi ya bayyana cewar samar da marubuta 280 ne suka shiga gasar, kafin a tace su dawo 50, sannan aka sake tacewa zakarun gasar suka dawo su 15 kamar yadda haka:-

  1. Kabir Yusuf Fagge Daga Jihar Kano, Taken Labari Matalauciyar Rayuwa, ya samu kyautar N55,000.
  2. Hassana Abdullahi Hunkuyi Daga Jihar Kaduna, Taken Labari A Sasanta, ta samu kyautar N35,000.
  3. Zakariya Haruna Danladi Daga Jihar Kano, Taken Labari Da Sandar Hannunka, ya samu kyautar N25,000.
  4. Ibrahim Babangida Suraj Daga Jihar Katsina, Taken Labari Hangen Dala, ya samu kyautar N12,500.
  5. Kabiru Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Ragguwar Dabara, ya samu kyautar N12,500.
  6. Fadila H. Kurfi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Rayuwar 'Ya Mace, ta samu kyautar N12,500.
  7. Na'ima Abdullahi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Zagon Kasa, ta samu kyautar N12,500.
  8. Jamila Muhammad Lawal Daga Jihar Kaduna, Taken Labari Tsananin Talauci, ta samu kyautar N12,500.
  9. Amina Sani Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Balaguron Talauci, ta samu kyautar N12,500.
  10. Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano, Taken Labari Jamhuriyar Matalauta, ya samu kyautar N12,500.
  11. Fatima Husaini Ladan Daga Jihar Katsina, Taken Labari Kowa Ya Bar Gida, ta samu kyautar N12,500.
  12. Hamza Dawaki Daga Jihar Kano, Taken Labari Katantanwa, ya samu kyautar N12,500.
  13. Zaharadeen Nasir Daga Jihar Kano, Taken Labari Salmakal, ya samu kyautar N12,500.
  14. Usman Muhammad Alkasim Daga Jihar Katsina, Taken Labari Dangina, ya samu kyautar N12,500.
  15. Abubakar Yusuf Mada Daga Jihar Zamfara, Taken Labari Sauyin Rayuwa, ya samu kyautar N12,500.
Bayan kammala mika kyaututtuka da karramawa, Prof. Isah Mukhtar Malami a Jami'ar Bayero, ya bayyana farin ciki da gamsuwarsa ga yadda gasar ta gudana.
Kabir Yusuf ya wakilci sauran marubuta da suka lashe gasar domin jawabin godiya. Inda a nasa jawabin ya fara da fadin, "Hakika ni ba iya godiya zan yi ba a madadin marubuta, addu'a zan yi cewar Allah ya sakawa wannan cibiya ta Pleasant Library and Book Club (PLCB) da Makarantar Malam Bambadiya (MMB) da alheri, Allah ya basu dukkanin abin da suke nema, kuma Allah ya kara arziki, ya sanyawa rayuwa albarka." Sannan ya bayyana wannan gasa a matsayin abubuwa kamar:-
  • Wannan gasa ba iya gasa ba ce, taimakawa ne da samar da hanyar farfado da dabi'ar karatu a tsakanin dalibai dai sauran al'ummar Hausawa
  • Karfafawa da kuma farfado da darajar harkar rubuce-rubuce
  • Samarwa da matasa musamman masu fasaha madogara da kyautata rayuwarsu
  • Nunawa marubuta ainihin abubuwan da ya kamata su yi rubutu a kai.
A karshe ya rufe da fadin cewa, daman marubuta  suna rabe-rabe ne saboda rashin mafaka, amma yanzu sun samu matsugunni don sun samu Pleasant Library and Book Club, sannan Makaranta Malam Bambadiya, makaranta ce da kowanne marubuci ya kamata ya shigeta, idan bai samu shiga ba a wannan shekarar, ya jira wata shekarar ya shigeta koda kuwa da JAMB ne, domin nan ne gidan karatun marubuta.
A karshe marubucin ya yaba da kokarin Prof. Ibrahim Malumfashi, wanda shi ne a yanzu ya ragewa marubuta da yake koyar da su, yake duba lamuransu, kuma yake samar musu magani. Allah ya saka da alheri.

A karshe Malam Bukar Mada ya rufe taron da addu'a, da fatan Allah ya albarkaci abin da aka yi, Amin.


2 comments:

  1. Alhamdulillah. muna taya ku murna yayyenmu.

    ReplyDelete
  2. For this web site, you will see our account, remember to go through this info. sewer repair in Pleasant Hill

    ReplyDelete

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...