MAKAHO MAI FITILA
Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wannan makaho, ka cika rigima! Me ya kai ka yawo da fitila? Dare da rana ba duk ɗaya su ke a gare ka ba?"
Makaho ya ce, "Duk ɗaya ne mana, Bala ɗan Jatau, ai har in da dare ne na fi ka ganewa. Fitilan nan na rike ta ba don kaina ba ne, amma domin irin ku ne marasa hankali, da ba ku da ido, kada ku hau ni."
Daga littafin Ka Koyi Karatu
No comments:
Post a Comment