Thursday, August 30, 2018


 Hausa novel

SANADIN KENAN!

Dr. Turaki ya yi murmushi yana duban Amina a tsanake, cikin kwantaccen sauti ya ce da ita "As a doctor, ba sai na gaya miki yadda zaki yi da patients dinki ba, but wannan patient din....needs extra more.....  Saboda marainiya ce. Sannan lafiyarta (matters a lot to her Dad)."
Zai nutsu ne kadai wajen aikin al'ummarsa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu, kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa da kafafuwanta. "Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye zaki dinga magana da His Excellency in kuna buqatar wani abu ko sanar dashi wani abu daya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and the best physiotherapist as we know... Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa".
Tunda ya fara bayanin Dr. Amina bata ce komai ba, tunani kawai take cikin zuciyarta, ta mika masa wayar, ya karba ya sanya, ya mayar mata ta adana lambar cikin wayarta. A ranta ta san ta karba ne kawai amma ba zata taba iya kiran MA'AROUF JI-KAS ba! Wani kwayan  mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, akan dalilin da ba zata ce mene ne shi ba. Duk da zasu kasance gida daya. Shi din dai  (Turakin) zata cigaba da baiwa jakadancin ko yana so ko baya so!!!

                                                            -Takori

1 comment:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...