Saturday, September 29, 2018

LITTAFIN SHATA: NA SHA WAHALAR SHEME A LITTAFI NA FARKO - Dr. Aliyu Ibrahim Kankara




NI NA FARA WALLAFA LITTAFIN SHATA A DUNIYA - DR. ALIYU IBRAHIM KANKARA
-Na sha wahalar Sheme a Littafi na farko

Na fara son Alhaji Shata da wakokinsa tun cikin 1974 lokacin ina tare da iyayena a Angwan Kanawa, Kaduna, mahaifina ya na koyarwa a Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Sa'ilin ban wuce shekaru 6 da haihuwa ba. Tun lokacin son da na ke ma Mamman Shata na musamman ne. Tun iyaye na ba su fahimta har su ka gane. Ko a Telebijin aka nuno shi ya na waka na kama murna kenan, da zaran kuma an dauke wuta kafin ya ida wakar, to har kuka na ke yi kuma na dinga fushi kenan har safe. 
Ni babana ba ya da wata alaka da Shata, amma ganin ina son sa ya kan zaunar da ni ya bani labarin sa, na zuwan da ya ke yi a RTK Kaduna (watau BCNN da kuma daga bisani NBC) a tsakanin 1969 da 1972 lokacin mahaifin nawu na aiki a can, da kuma ziyarar da ya kan kai ma amininsa Alhaji Hamza Kankara har Musawa lokacin ya na aiki a gonar mahaifin Shata Malam Ibrahim Yaro. 

MATA-MAZA


MATA MAZA
Daga Fauziyya D. Sulaiman


Na taso cikin wani yanayi na matukar tsaro da mahaifana su ka dorani akai, duk wani wasa da maza tsarakuna ke yi mahaifana kan hana ni shiga, yayin da su ke taka tsantsan da ni gurin zama kusa da mata, sannan mahaifiyata ta na sanar da ni kar na sake ko da wasa na bar jikina a waje kowa ya gani, idan na yi hakan zan iya mutuwa, wannan tsoron na tashi da shi cikin raina matuka, don haka bana jin ban da mahaifana ba wani da ya taba ganin al'aurata.
sai dai na fahimci wani abu bayan na fara girma, akwai wani abu da na ke da shi irin na halittar kannena maza, sannan kuma ina da na halittar kannena Mata, da abin ya dame ni sai na tambayi mahaifiyata ni me ya sa na ke da guda biyu. A lokacin da na yi mata wannan tambayar na ga matukar tashin hankali a tattare da ita, amma sai ta ce min kar na kara yin irin wannan maganar idan na kara zan mutu.
kasancewar tunda na tashi ake tsorata ni da mutuwa ya sa duk wani abu da ya dangance ta ina tsoransa. Bayan na shekara goma shadaya mahaifina ya tattarani ya kaini almajiranci binni, duk da na san ni namiji ne kamar yanda iyayena suka sanar da ni, amma yanayin jikina ba shi da kwari irin na maza, hatta muryata da tafiyata irin ta mata ce, hakan ya sa tun ina garinmu ake tsokanata idan na yi magana har kawo zuwan almajiranci.
Lokacin dana kai shekaru goma sha biyar sai na ga kirjina yana dagawa irin na mata, amma sai na ci gaba da boyewa kamar yanda mahaifiyata ta sanar da ni. Watarana na je ganin gida ina kwance a daki ina bacci sai na ji kamar na yi fitsari a kwance, na tashi cikin gigita sai na ga duk jini ya bata jikina, na fara kuka da ihu ina kiran mahaifiyata, lokacin da ta shigo ta ga abin da ya faru hankalinta ya tashi kwarai da gaske, don haka ta kira mahaifina ta gaya masa, shima ya shiga damuwa, sai suka bani tsumma da wando karami suka ce na saka, anan ma sun kara gargadina da kar na sanar da kowa, sannan mahaifiyata ta sanar da ni duk wata zan dinga yin wannan abin kar na damu.
Na ci gaba da rayuwata a haka ina boye kaina ga yan'uwana maza, sai dai watarana ina cikin bara a cikin binni bakin hanya wata mota ta kwasheni ta yi watsi da ni, na ji mummunan ciwo a kafafuna da ta kai sai da aka kaini asibiti ranga-ranga.
Bayan taimakon gaggawa da likitoci suka bani da taimakon wasu bayin Allah aka yi min aikin da na sami saurki, sai dai tun da aka kawo ni asibiti likitoci suka sanar dani ni Mata-Maza ne, dole sai an yi min aiki an mayar dani daya.
Na shiga damuwa da tashin hankali, duk da mahaifina yana ta min nasiha da kwantar min da hankali, Amma ranar da likitoci suka tattauna da mahaifina su ka tabbatar min da cewar kwan halittun mace sun fi karfi a jikina, don haka dole mace za mayar dani .
Tun ranar da na ji wannan maganar na kasa bacci saboda tashin hankali sai kuka, ta yaya zan koma mace bayan na yi tsahon shekaru ashirin da daya a matsayin namiji, amma bayan ganin irin halin da na shiga na tashin hankali ya sa likitoci suka kara zama suka tattauna, sun ce zan iya komawa namiji amma sai dai a fitar da ni kasar waje domin yi min aiki, amma mahaifina ba shi da ko kudin motar da zamu iya komawa garinmu balle abin da za a yi min aiki. Ina jin yanzu kamar na gudu na bar garin nan, domin ta yaya zan kalli abokaina bayan an mayar dani mace? Shin waye ke da laifin kasancewar rayuwata a haka ne? Shin iyayena sun so na kasance namiji ne kawai domin ace suna da da namiji ko me ya sa suka min haka? Wannan sune tambayoyin da ke damuna babu kuma mai bani amsarsu har zuwa yanzu da na ke sanar da ku damuwata.

Friday, September 28, 2018

KARAIRAYI 16 A MARTANIN ALIYU IBRAHIM KANKARA Daga IBRAHIM SHEME

 

Ibrahim Sheme
 
A ranar Juma'a da ta gabata, jaridar Aminiya ta soma buga hirar da wakilin ta, Bashir Yahuza Malumfashi, ya yi da ni a kan sabon bugun littafin tarihin Alh. (Dr.) Mamman Shata Katsina mai taken "Shata Ikon Allah!" wanda ya fito kwanan nan. Za ta ci gaba da buga hirar a gobe Juma'a, in-sha Allah.

Jiya, sai ga martani ya fito daga Dr Aliyu Ibrahim Kankara, daya daga cikin mu hudu da mu ka yi binciken farko don a rubuta littafin. Ban so in yi cacar baki da Kankara kan wani abu da ya shafi littafin ba, shi ya sa ma na yi hirar da Aminiya gaba-gadi a bisa tunanin ko mutum ba ya kaunar Allah idan ya karanta zai yarda da cewar lallai hakikanin abin da ya faru kenan. Haka kuma akwai wadanda su ka ce mani, "Kada ka kula shi, domin ba matsayin ku daya a idon al'umma ba." 

To, ba maganar matsayi ba ce, magana ce ta menene mu ka bar wa tarihi; idan na yi shiru kan karan-tsayen da Kankara ya yi wa gaskiyar abin da ya faru, to ban yi wa tarihi adalci ba. Haka kuma ni ba irin mutanen nan ba ne da za su ga karya muraran su kyale saboda wani. Shi ya sa na ga dacewar in nuna wa jama'a cewa akwai karairayi jingim a rubutun na Kankara, wadanda na ke so a fahimta. Daga nan, idan mutum ya karanta, sai ya zabi na zabe!

Kafin in jero karairayin, ina so in yi shimfida da cewar ba wannan ba ne karo na farko da Aliyu ya fara shara karya game da tarihin Shata ko dangantakar da ya ce wai ya na da ita da mawakin. Tun a farkon haduwar mu, lokacin da ya kawo mani takardun da ya rubuta kan Shata don in gani, na ga dimbin abubuwan shaci-fadi da ya rubuta wadanda hankali ba zai iya dauka ba, wadanda ko d'an karamin bincike ma zai nuna wa mutum cewar karya ne. Irin wadannan abubuwan, na yi watsi da su a lokacin da na ke rubuta littafin "Shata Ikon Allah!" da aka kaddamar a cikin shekarar 2006. Na san Kankara bai ji dadin watsi da na yi da su ba, kuma hakan na daga cikin dalilan shi na warewa daga gare mu, mu "marubutan littafin Shata", ya tafi ya dauki littafin mu ya baddala shi ya fito da wani a matsayin nasa (zan yi magana kan wannan a nan gaba, ba a yau ba).

Na biyu, a zantuttukan sa a soshiyal midiya da hirarrakin sa a rediyo na sha jin irin yadda Kankara ya ke zubo karairayi game da Shata ko tarayyar da ya ke ikirarin ya na da ita da Shatan, ba tare da kawo hujjar da za ta tabbatar da hakan ba. Hasali ma dai, Kankara ya saba da sheka k'arya game da Shata ta yadda har akwai alamun ya yi amanna da cewa karairayin sa gaskiya ne. Shi ya sa a duk inda ya zauna, sai ya dinga zuba ratatata kan tarihin Shata da ba gaskiya ba ne, ya debo dahir ya gwamutsa da kirkira, ya fitar da wata magana wadda yawancin masu saurare ba za su kama ba. Har ta kai mutane da dama na mamakin yadda za a ce wai mutum mai PhD ne ke magana haka babu kangado, sai ka ce ko sakandare bai gama ba!

Irin wannan kame-kamen ne na gani a rubutun shi na jiya mai take irin na taken hira ta da Aminiya, wato "Ni Na Fara Rubuta Littafin Tarihin Shata", taken da shi kan sa ba daidai ba ne (kamar yadda na fada wa Bashir Yahuza bayan na karanta hirar da ya yi da ni).

Bari mu koma kan karairayin Kankara. Da farko, ban damu da yaushe ne Kankara ya soma kaunar Shata ba; ko tun ya na cikin ciki ya fara son sa, ba damuwa ta ba ce. Amma wace irin soyayyar ya ke yi masa har ta kasance iyalin marigayin ba su yarda da abubuwan da ya ke yad'awa game da mahaifin su ba? Sannan wace irin soyayya ce ya ke yad'awa a hirarrakin sa ta yadda duk manazarcin da ya bincika zai tarar da cewa zuk'i-ta-malle ce wadda ba ta iya tsayawa da kafafun ta? Misali, "sai da aljannu su ka yi wa wata 'yar bori bushara da haihuwar Shata!" "A ranar da aka haifi Shata, an ji kalangai su na tashi a sararin samaniyar garin Musawa!" "Kafin ranar sunan Shata, Shatan ya bace daga zanin goyon sa, ba a sake ganin sa ba sai bayan kwana uku!" "Kai, Shata ba mutum ba ne, aljani ne!" Da dai sauran su.

Bari mu duba martanin Kankara daki-daki.

1.
Cewar Kankara: "Cikin 1990 na ya kai wa Shata littafin da na rubuta": 

Wannan maganar, da makamantan ta da ya yi a baya, ba gaskiya ba ce. Ba zan ce Kankara ba ya son Shata kafin haduwa ta da shi ba, amma wallahi shi da Shata ba su san juna ba sai da na kai shi wajen Shatan a Funtuwa bayan hadewar mu. Zurfin hulda ta da Kankara, tare da zurfin sanayya ta da Alhaji Shata da yaran shi, ta isa ta sa in san idan Kankara da mawakin sun san juna kafin haduwa ta da Kankara. Babu wani lokaci da wani daga cikin su ya fada mani ya san dayan. In da Kankara ya san Shata kafin in kai shi wurin sa, to da ya fada mani. Haka kuma in da Kankara ya yi wani littafi kan Shata har ya kai masa, to da ya fada mani lokacin da na ce mu je in gabatar da shi ga Shata a cikin 1997. Kuma in da Kankara ya yi littafi kan Shata, to da ya ba ni shi lokacin da mu ka hade, mu ka shiga fafutikar tattara tarihin Shata domin yin littafi.

2. 
"Wai a 1994 Kankara zai tafi NYSC, ya kai wa Shata littafi". 

Wannan ma karya ce ya shirya. Ban san wani labarin Kankara ya nemo izinin Shata don ya rubuta wa wata kungiya a Kano tarihin Shata ba, wanda har ya rubuta ya kai masa da zai tafi bautar kasa. A rubutun shi, Kankara ya ce har ya kammala littafin a 1994, to ya aka yi a 1997 da ya ba ni warkokin da ya rubuta na ga ba su fi shafi 15 na rubutun hannu ba? Shi ne littafin? Ya aka yi bayan haduwar mu, mu ka dinga fadi-tashin bincike don fito da littafin, abin da ya dauke mu shekaru? Sannan idan har a 1994 ya rubuta littafin, to daga 1991 da na fara binciken tarihin har zuwa lokacin babu shakka da na samu labarin sa a wajen Shata ko Ya'u Wazirin Shata ko wani yaron Shata. A gaskiya, Kankara bai rubuta littafi ba a lokacin.

3. 
"Wai Shata ya umarci Kankara da ya yi hira da wasu mutanen Legas da ya wak'e". 

Wannan magana ba gaskiya ba ce, domin in da an yi hakan to babu shakka da Kankara ya je ya yi wadannan hirarrakin. Tun da mu ka fara bincike kan tarihin Shata har mu ka gama a 2006, Kankara bai kawo mana hira ko da kwaya daya da ya yi da daya daga cikin mazauna Legas da Shata ya yi wa waka ba.

4. 
"Wai a 1995 Ya'u Wazirin Shata ya yi wa Kankara maganar Ibrahim Sheme". 

A cikin 1995 ba mu hadu da Kankara ba, ban san shi ba. Hasali ma dai, sai bayan haduwar mu da na dauki Kankara na kai shi wajen Shata sannan ne ya san Ya'u Wazirin Shata. Ni ne na dauki Kankara a mota ta, bayan mun bar gidan Shata, na kai shi gidan Alh. Ya'u na gabatar da shi ga Ya'un. Ko kadan Ya'u Waziri da Kankara ba su nuna wa juna sanayya ba lokacin da na sada su. In da a ce an san Kankara a fadar Shata, to da shi mawakin da shugaban 'yan amshin nasa sun nuna haka lokacin da na kai Kankara wajen su.

5. 
"Wai Ibrahim Sheme ya zauna gida daya da wani Kabiru Dan'azumi Kankara a unguwar Badikko, Kaduna". 

A Badikko, na kama hayar gida sukutum ne (2-bedroom flat da garejin mota da filin tsakar gida). Ban zauna da kowa a gidan ba sai mata ta. Wannan magana shirme ce.

6. 
"Wai ba Ibrahim Malumfashi ya hada Kankara da Ibrahim Sheme ba". 

Babu shakka, ban taba jin ko sunan Kankara ba sai a bakin Malumfashi lokacin da ya bukace ni da in hadu da shi in ga abin da ya rubuta kan Shata. Farfesa Malumfashi na da rai, zai iya tabbatar da wannan magana ko akasin haka.

7. 
"Wai a 1995 Sheme da Kankara su ka hadu har Sheme ya nuna masa aikin littafin da ya yi. Daga nan ba su sake haduwa ba sai a 1997." 

Wannan ma wata karyar ce. A 1995, ban taba jin sunan Kankara ba, sai a 1997 lokacin da Ibrahim Malumfashi ya hada mu. Kuma tun da mu ka hadu ba mu taba rabuwa ba har lokacin da aka kaddamar da "Shata Ikon Allah!" a cikin 2006.

8. 
"Wai Sheme ya ziyarci Kankara a ofis din sa a Kaduna Polytechnic a 1997 inda ya nemi su hade su yi littafi daya".

Wannan ma karya ce. Tun lokacin da Malumfashi ya sada ni da Kankara, ba a yi ko mako daya ba na amince mu ka hade. Sannan ban taba zuwa ofishin Kankara a Kaduna Polytechnic ba; wani zuwa da na yi sau daya rak, na je ne domin in taimaka masa kan wata wuta da ya kunno wa kan sa. Matsalar ita ce wata yarinya daliba ta kai Aliyu Kankara ga hukumomin makarantar, har an kafa kwamitin musamnan ana bincike. Na je ne bisa bukatar Kankara in ga ko zan iya sasanta lamarin, a matsayin sa na abokin aiki na kan littafi. A karshe, ba mu samu nasara ba, domin kwamiti ya bada shawarar a kori Kankara daga aiki. Haka kuwa aka yi, aka kore shi daga aikin koyarwa bisa koken da dalibar sa ta yi. Wannan ne ya sa ya koma aiki a wani kamfanin wasu 'yan kasar Chaina masu hakar ma'adinai a yankin Sakkwato (aikin da Saleh Abu Katsina ya sama masa). Daga can ya kukuta aka dauke shi aiki a matsayin malamin makarantar sakandare (GDSS) ta garin Daudawa da ke Faskari LGA a Jihar Katsina. Malamin Polytechnic ya koma malamin sakandare kenan! Daga nan ne, bayan shekaru, aka dauke shi aiki a Jami'ar Umaru Musa Yar'Adua a Katsina. Nan gaba zan dawo kan ainihin kes din nan da ya sa aka kore shi daga Kadpoly da matsalar da ya samu da Chanis din nan da yadda aka yi ya koma Jami'ar Tarayya da ke  Dutsin-ma, musamman ma yadda wadannan matsalolin su ka kawo mana cikas wajen kammala littafin "Shata Ikon Allah!"

9. 
"Wai matar Kankara na shaidar...!" 

To, ni ban sani ba idan maganar Kassu Zurmi gaskiya ce ba da ya ce "mutum ba ya shaidar dan'uwan shi ko hwada" da kuma fadar Shata a wakar Dambu Dan Mamman cewa "wace shaidar d'an ka za yai ma, in ka hada duka duk dai Dambu ne?"

Wallahi, ban taba zawarcin Kankara don mu hade mu yi littafi ba. Kamar yadda na fada, mun hade da Kankara tun a satin farko na haduwar mu a cikin 1997. Idan na taba zuwa gidan shi, hakan bay a rasa nasaba da aikin da mu ka tsunduma yi ne, ba domin mu hade ba tunda mun riga mun hade. Amma shi ya kan zo gida nay a fi sau shurin masaki, idan za mu yi tafiya ko idan zai karbi kudi a waje na. Saboda haka maganar wai ina zawarcin sa domin mu hade ba gaskiya ba ce.

10. 
"Wai Sheme ya fito 'sabon-huji', ya fito fes, ya kammala karatu na biyu".

A 1997 lokacin da na fara ganin Kankara har mu ka hade mu yi littafi, ni ba sabon yanka rake ba ne wajen kammala karatun digiri na biyu. Na samu M.A. Journalism Studies daga Cardiff University, a U.K., tun cikin 1994 (shekaru 3 kafin in fara ganin Kankara a rayuwa ta). A 1997 ina daga cikin manyan editoci a kamfanin jaridar New Nigerian.

11. 
"Wai Sheme na tura Kankara ya yi masa hira da jama'ar Shata saboda shi ba ya da lokaci".

Kamar yadda na fada, na fara hira da Shata a 1991 domin rubuta tarihin shi. Shekaru 6 kenan kafin in fara ganin Kankara. A tsawon wannan lokacin, na yi hira da mutane masu yawan gaske. Misali: Garban Bichi, Indon Musawa, Sa'in Katsina Amadu Nafuntuwa, Amadu Doka, Tukur Othman, Turi Muhammadu, Musa Musawa, Munari Jikar Mairo, Nagwandu Mainama, Laila Dogonyaro, Amadu Doka, Danmaraya Jos, Hakimin Bakori Alhaji Tukur Idris Nadabo, Shehu Maigidaje, Halilu Ahmed Getso, Bala Maikaka, da sauran su da dama. Kuma na yi hirarraki da yaran Shata da su ka hada da shugaban 'yan amshi Alhaji Ya'u Wazirin Shata da shugaban makadan kalangun Shata, wato Bawa Dungun Mu'azu. Sannan na je Musawa na yi hira da 'yan'uwan Shata da abokin sa irin su Mal. Ali  Dankane. Duk wannan ya faru ne KAFIN in ma san wani wai shi Aliyu Kankara. Sannan bayan haduwar mu da shi, na ci gaba da yin wasu hirarrakin. Saboda haka maganar ba ni da lokaci ma karya ce.

Tura Kankara da na yi zuwa wasu garuruwan, kamar Bauchi da Gombe, da kuma Musawa saboda ya yi mana hira da Magajin Gari Malam Abdullahi Inde da wasu mutanen, duk cikin raba aiki da mu ka yi bayan mun hade mun zama mu 4 a aikin. Ko ya manta cewar mun raba aiki ta yadda su Yusuf Albasu da Ali Malami su ma za su samo mana wasu hirarrakin, musamman a Kano? Wannan shi ne dadin hadewar ai, wato wannan ya kama nan, wancan ya kama can. Hakan ne ya sa ni ne na yi hira da mutane irin su Dauda Mani da Sarki Jinjiri da Goshin Dangude ba tare da Kankara ya sani ba sai daga baya na fada masa. Abin lura shi ne duk da yake ina yin hirarrakin nan kamar yadda na lissafa a sama, ai kuma ni ne mai rubuta littafin; ni ne wanda ke karance duk abin das u Kankara su ka yayumo, ya fitar da ma'ana daga ciki, ya jera bayanan a cikin littafi inda ya dace; shin ko wannan bai isa aiki ba?

12. 
"Wai Kankara ya hada Sheme da wasu mutanen Shata a Kaduna tunda shi bai san su ba".

Hankali zai iya daukar wannan maganar kuwa? Mutum ne ya same ka ka na bincike domin rubuta littafi, har ka shafe shekara shida ka na yi. Kuma a Kaduna ka ke zaune. Ka yi tafiye-tafiye a wasu garuruwa. To ya za a ce ba ka ma san mutanen da su ne ka ke samo bayani a wajen su ba? 

Kankara ya ambaci Alh. Nagwandu Mainama, wai shi ya hada ni da shi. Wannan ba gaskiya ba ce. Na yi hira da Nagwandu a mayankar da ke Tudun Wada, Kaduna, ba tare da Kankara ba.

Kuma ya ambaci Alh. Amadu Doka mai kukuma, wai shi ya hada mu. Ka ji tantagaryar k'arya! Kankara ya manta cewa Amadu Doka amini na ne na tsawon shekaru tun kafin mu hade, sannan ni din nan ni ne na fara kai shi wajen Amadu Dokan har gida, na gabatar da shi? A nan ma dai, karya ce ya yi wa kwalliya domin ya sayar da ita ga wanda bai ankara ba!

Na yi hira da Amadu Doka domin sakawa a littafin Shata tun a cikin 1993 (shekaru 4 kafin in fara haduwa da Kankara). An buga hirar a mujallar Rana ta ranar 19 ga Oktoba, 1992. A lokacin, ni ne Editan mujallar, kuma ban san wani  Aliyu Kankara a duniya ba.

13. 
"Wai cikin 1998 Sheme ya tafi Funtuwa ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano".

Ban samu Shata domin ya kwanta a asibiti ba. Kamar yadda na sha fadi, a matsayi na na jagoran rubuta tarihin Shata, na sha zuwa in same shi kan wani abu da ya danganci aikin. Kuma ba lallai ba ne sai na je tare da Ali Kankara. Lokacin wannan ziyarar da Kankara ke magana, na je ne domin in yi wata sabuwar hira da Shata kan wasu abubuwa da na lissafa wadanda jama'a ke magana a kan su, misali batun cewar wai Sule Jikan Korau ya taba marin Shata, da batun wai Shata ne ya yi wa Ali Dansaraki makaru ya kasa waka, da batun Garba Goga ne ya fara kai Shata garin Funtuwa kamar yadda mawakin ya ke ambata a Bakandamiya. Kaset din hirar, na ba Kankara ya rubuta shi a takarda, kuma har yau din nan ya ki dawo mani da kaset din. To, a wannan zuwan ne Shata da kan shi ya ba ni labarin su Yusuf Tijjani Albasu da Ali Malami. A lokacin, ni dai ban taba jin wai an kwantar da Shata a asibiti ba.

14. 
"Wai Sheme ya dauki Kankara tare da wani abokin Shemen mai suna Aimana Datti Usman, su ka tafi Funtuwa".

Ban taba yin aboki mai wannan sunan ba. Ina jin dai Aimana abokin Yusuf Albasu ne da su ka je Funtuwa taro lokacin da na gayyato su daga Kano. Ni Yahaya Umar na dauka a Zariya.

15. 
"Wai Shata ne ya ce a hade a yi littafi daya".

Wannan ba gaskiya ba ne. Makasudin kiran su Albasu da Malami shi ne a kwace littafin su, a kore su, bisa hujjar cewa ba a ba su izinin rubuta littafin ba. Da ni aka yi wannan shiri, ba a gaban Kankara ba. Ni ne na bada shawarar a yi littafi daya, bayan mun fita waje na duba aikin da su ka yi, na ga ya burge ni matuka domin sun yi hirarraki da wasu mutane da mu ke so mu yi hira da su, irin su Abubakar Uwawu, Hassan Hadi, Delun Kunya, Hauwa Maituwo, da sauran su. Shawarar  da na bayar cewa a hade, ta ba kowa mamaki, har shi kan sa Shatan, domin ba ta cikin shirin da aka yi a makon da ya gabata. Sannan ko kadan Kankara ba ya goyon bayan hadewar, kawai dai don babu yadda zai yi ni ne a matsayi na na shugaban shi.

16. 
"Wai Shata ya manta da littafin da Kankara ya rubuta wa kungiya, shi kuma kawaici ya hana shi magana".

Wannan ma wani soki-burutsu ne. Lokacin da mu ka je taron da mu ka hade da su Ali Malami da Yusuf Albasu a Funtuwa, an fi shekara daya da hadewa ta da Kankara. Wato kenan Shata ya san ni da Kankara, saboda haka ya yi maganar wani littafin kungiya ai bai taso ba. Me ya sa ma a lokacin da na fara kai Kankara wajen Shata, na ce masa ga wani wanda za mu yi aikin rubuta littafin da shi, ba su nuna sun san juna ba? Dalili shi ne babu wata sanayya tsakanin Shata da Kankara, sannan Kankara bai taba kai wa Shata littafin da ya ke ikirarin ya rubuta ba. In da akwai littafin, kuma in da sun san juna, to da tun tuni na sani. Wannan maganar, kawai kirkira ce aljannun da ke damun kwakwalwar Aliyu Ibrahim Kankara su ka ba shi, shi kuma ya hau kai ya na kokarin yaudarar mutane da ita.

Ina kira ga Aliyu Kankara da ya nuna guntun rikodin ko kwaya daya da ya taba yi da Shata, wato wata hira da su ka yi, ko wani hoto da su ka taba dauka tare, a matsayin nuna sanayyar da ya ke karyar sun yi wa juna shi da mawakin. Na san babu. Dalili shi ne, Kankara da Shata ba su san juna ba kafin in kai Kankara wajen sa, kuma ko da na kai shi din, babu wata sanayya da Shata ya yi masa, domin bai taba zuwa wajen Shata ba tare da ni ba, sai idan na kai shi. Hasali ma dai, Kankara bai taba hyin hira da Shata domin yin littafi ba. Duk abin day a ke fada a bayan rasuwar Shata, kirkira ce irin ta marubucin da kwakwalwar sa ta motsu, ya na ganin dodon wani abu da ya ke ganin kamar ya taba faruwa a rayuwar sa bayan kuwa bai taba faruwa din ba.

Zan yi zango a nan. Zan kawo ci-gaban wannan raddi nan gaba kadan, domin wannan magana yanzu na fara ta.

Bissalam.

Wednesday, September 26, 2018

Book cover: READING & WRITING NUMBERS FOR BEGINNERS


PLEASANT LIBRARY DA MMB SUN KARRAMA MARUBUTA


PLEASANT LIBRARY DA MMB SUN KARRAMA MARUBUTA

A ranar Juma'a 21-9-2018 a dakin karatu na PLEASANT LIBRARY AND BOOK CLUB dake Kaita Road jihar Katsina aka bayyana Kabiru Yusuf Fagge (wanda aka fi sani da Kabir Anka) a matsayin wanda ya lashe gasar gajerun labarai ta shekarar 2018.

Anka tare da sauran marubuta sun karbi kambin gasarsu tare da kyautuka nan take a hannun manyan shaihunan malaman da suka halarci taron.

Tun da farko Malam Mai Bazazzagiya ne ya bude taron da addu'a, sannan kai tsaye aka wuce da Jawabin Maraba ga bakin da suka halarci bikin bayar da kyautukan, inda Dr Abu Sabe Malami a Jami'ar Katsina ya tarbi bakin da maraba.

Shaihun Malami, Professor Ibrahim Malumfashi ya gabatar da makasudin taron, inda ya bayyana cewar abubuwa biyu zuwa uku ne suka assasa wannan gasa ta rubutu, na farko dawowar Makarantar Malam Bambadiya, wanda shi Professor din yake jagoranta da kuma irin ayyukanta na kokarin kyankyashe jajirtattun kuma gwarazan marubuta da rubuce-rubuce a kasar Hausa da arewacin Nijeriya. Sannan sai goyon baya da hadin gwiwa da aka samu daga wannan shahararriyar cibiya ta Pleasant karkashin jagorancin shugabanta wato Engr. Dr. Muttaka Rabe. Malamin ya sha alwashin in sha Allah yana fatan hakansa ya cimma ruwa.

A nasa jawabin, shugaban PLBC, wato Engr Dr. Muttaka Rabe Darma ya bayyana wannan taro a matsayin wani danba na:- Samar da hanyoyi da mafita daga tarnakin da ke damun al'umma (wato social issue) - Da kuma samar da fikira, fasaha da basira musamman ga matasa Hausawa. Sannan kamar yadda cibiyar take da wannan burin, Engr. Dr. Muttakan ya yi alkawarin jajircewa don cimma wannan buri da manufa tasa.

Daga baya Prof. Malumfashi ya sake dawowa, ya yi 'yar takaitacciyar lakca a kan sirrin gudanar da gasar rubutu da matakan cin nasara. Duk da rashin lokaci, Prof. din ya kawo wasu 'yan hanyoyi a takaice da zasu taimakawa duk wani marubuci da yake da sha'awar shiga gasa, kuma har ya ci.

Bayan 'yar takaitacciyar lakcar Professor Malumfashi, an fara karramawa tare da mikawa kyaututtuka ga gwarazan marubuta 15 da suka samu nasara. Kafin a fara mika kyautukan, Prof. Malumfashi ya bayyana cewar samar da marubuta 280 ne suka shiga gasar, kafin a tace su dawo 50, sannan aka sake tacewa zakarun gasar suka dawo su 15 kamar yadda haka:-

Kabir Yusuf Fagge Daga Jihar Kano, Taken Labari Matalauciyar Rayuwa, ya samu kyautar N55,000.
Hassana Abdullahi Hunkuyi Daga Jihar Kaduna, Taken Labari A Sasanta, ta samu kyautar N35,000.
Zakariya Haruna Danladi Daga Jihar Kano, Taken Labari Da Sandar Hannunka, ya samu kyautar N25,000.
Ibrahim Babangida Suraj Daga Jihar Katsina, Taken Labari Hangen Dala, ya samu kyautar N12,500.
Kabiru Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Ragguwar Dabara, ya samu kyautar N12,500.
Fadila H. Kurfi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Rayuwar 'Ya Mace, ta samu kyautar N12,500.
Na'ima Abdullahi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Zagon Kasa, ta samu kyautar N12,500.
Jamila Muhammad Lawal Daga Jihar Kaduna, Taken Labari Tsananin Talauci, ta samu kyautar N12,500.
Amina Sani Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Balaguron Talauci, ta samu kyautar N12,500.
Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano, Taken Labari Jamhuriyar Matalauta, ya samu kyautar N12,500.
Fatima Husaini Ladan Daga Jihar Katsina, Taken Labari Kowa Ya Bar Gida, ta samu kyautar N12,500.
Hamza Dawaki Daga Jihar Kano, Taken Labari Katantanwa, ya samu kyautar N12,500.
Zaharadeen Nasir Daga Jihar Kano, Taken Labari Salmakal, ya samu kyautar N12,500.
Usman Muhammad Alkasim Daga Jihar Katsina, Taken Labari Dangina, ya samu kyautar N12,500.
Abubakar Yusuf Mada Daga Jihar Zamfara, Taken Labari Sauyin Rayuwa, ya samu kyautar N12,500.

Bayan kammala mika kyaututtuka da karramawa, Prof. Isah Mukhtar Malami a Jami'ar Bayero, ya bayyana farin ciki da gamsuwarsa ga yadda gasar ta gudana.

Kabir Yusuf ya wakilci sauran marubuta da suka lashe gasar domin jawabin godiya. Inda a nasa jawabin ya fara da fadin, "Hakika ni ba iya godiya zan yi ba a madadin marubuta, addu'a zan yi cewar Allah ya sakawa wannan cibiya ta Pleasant Library and Book Club (PLCB) da Makarantar Malam Bambadiya (MMB) da alheri, Allah ya basu dukkanin abin da suke nema, kuma Allah ya kara arziki, ya sanyawa rayuwa albarka." Sannan ya bayyana wannan gasa a matsayin abubuwa kamar:-

Wannan gasa ba iya gasa ba ce, taimakawa ne da samar da hanyar farfado da dabi'ar karatu a tsakanin dalibai dai sauran al'ummar Hausawa
Karfafawa da kuma farfado da darajar harkar rubuce-rubuce
Samarwa da matasa musamman masu fasaha madogara da kyautata rayuwarsu
Nunawa marubuta ainihin abubuwan da ya kamata su yi rubutu a kai.

A karshe ya rufe da fadin cewa, daman marubuta suna rabe-rabe ne saboda rashin mafaka, amma yanzu sun samu matsugunni don sun samu Pleasant Library and Book Club, sannan Makaranta Malam Bambadiya, makaranta ce da kowanne marubuci ya kamata ya shigeta, idan bai samu shiga ba a wannan shekarar, ya jira wata shekarar ya shigeta koda kuwa da JAMB ne, domin nan ne gidan karatun marubuta.

A karshe marubucin ya yaba da kokarin Prof. Ibrahim Malumfashi, wanda shi ne a yanzu ya ragewa marubuta da yake koyar da su, yake duba lamuransu, kuma yake samar musu magani. Allah ya saka da alheri.

A karshe Malam Bukar Mada ya rufe taron da addu'a, da fatan Allah ya albarkaci abin da aka yi, Amin.

Tuesday, September 25, 2018

PLEASANT LIBRARY & BOOKS CLUBS & MMB AWARD NIGHT 2018 IN PICTURES


Prof. Ibrahim Malumfashi, shugaba kuma jagoran Makarantar Malam Bambadiya yayin tattaunawa da 'yan jarida jim kadan bayan kammala taron bayar da kyautukan Gwarzon Rubutu 2018

 Gwarzon Marubuci Kabiru Yusuf yayin da yake karbar kyautarsa daga hannun Engr. Dr. Muttaka Rabe Darma tare da Prof. Ibrahim Malumfashi


 Kabiru Yusuf (gwarzon marubuci na 1) da Prof. Ibrahim Malumfashi da Hassana Hunkuyi (Gwarzuwar Marubuciya ta 2) a yayin taron


Bello Idah (Gwarzon Marubuci na gasar Gusau Institute) tare da Danladi Haruna (Gwarzon marubuci na 3) a gasar PLBC & MMB

Marubuta: Kabiru Yusuf, Balannaji da Fatima El-Ladan, jim kadan bayan taro



Manyan Malamai da Marubuta goma da suka haye matakin rubutu akan Kimiyya Da Lissafi Da Turanci, yayin taron Bitar Makamar Aiki, don rubuta labarai akan wannan jigo da za a yi littafi.


  Marubuta: Fatima El-Ladan, Zubairu Balannaji, Kabiru Yusuf, Fatima Muhammad, Bilkisu Sulaiman

Zahraddeen Nasir, Danladi Haruna da Bukar Mada, suna hutawa kafin zuwa wajen taro a ranar ta 2


Hamza Dawaki, Abdullahi Hassan Yarima da Balannaji a gaban otal

Prof. Ibrahim Malumfashi yana jawabi a taron sanin makamar rubutu, Ado Gidan Dabino da Prof. Isah Muktar suna sauraro

Abdurrahman kenan ya karbi satifiket dinsa daga hannun Engr. Dr. Muttaka Rabe Darma


Marubuciya Nafisa Abubakar Marnaf tana karbar nata satifiket din 


Maryam (Queen Mermue) yayin karbar nata satifiket din 


Danladi Haruna kenan yake karbar satifiket dinsa a rana ta biyu na taron Kwararrun Marubuta 10 a kan rubuce-rubucen Lissafi,  Kimiyya da Turanci

Marubuci Dan'Azumi Gwarzo kenan yake karbar nashi satifiket din

Gwani yana karbar satifiket dinsa

 Ida yana karbar satifiket dinsa
Bamai yana karbar satifiket dinsa.

Sada Malumfashi yana karbar satifiket dinsa. 

Prof. Isah Muktar yana karbar satifiket dinsa. 

Ado Ahmad Gidan Dabino yana tattaunawa da dan jarida

A rana ta biyu, Professor Ibrahim Malumfashi tare da Kabiru Yusuf 




 







 



Sunday, September 23, 2018

Funny short story: A SA MIN KIRAN SALLAH





A SA MIN KIRAN SALLAH
Na
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Wani Danfulani ne ya dauki azumi, kuma gashi a ranar ana yin rana sosai, don haka azumin yana baiwa Danfullo wahala sosai. Yana zaune ya yi jugum, ya kunna rediyo sai ya ji ana yin ZABI-SONKA, kowa yana buga waya ya gaishe da mutane uku, sannan ya fadi wakar da yake so a saka masa.

Saturday, September 22, 2018

New Hausa novel: 'YAR FIM (LABARIN ZAHRA)


‘YAR FIM
 
Sunanta Zahra, babban burinta shi ne ta zama tauraruwa a cikin taurarin finafinan Hausa. A wajenta fim duniya ne!

Lokacin da aka kama Zahra da laifin satar amsa a dakin jarrabawa sai saurayinta Mahadi ya tari aradu da ka, laifin ya dawo kansa, ya dawo gida yana zaman jiran ta kammala ta zo su yi aure, amma Zahra ta manta da halaccinsa, kuma ta sanar masa ya manta da ita, ya goge ta har a zuciyarsa, kuma kar ya sake nemanta ko a waya.

Zahra ba Mahadi kawai ta sadaukar ba har da karatunta saboda ta zama ‘yar fim, kuma burinta ya sa ta bijirewa mahaifanta ta tsallaka katanga ta gudu a daren xaurin aurenta, ta kwana a otal ba da sanin kowa ba, ta bar danginta a cikin kuka, babanta ya ce ta je za ta gani.
Ta je, ta fara samun manyan ayyuka, furodusoshi suka fara rububinta kamar kudi, ta samu daukaka a babban farashin da ya janyo mata asarori.

Zahra ta fara cizon yatsa a makare lokacin da komai ya dawo yana ma ta gwalo, Mahadi ya fara dago mata hannu daga nesa yana dariya Zahra tana kuka.

KABIRU YUSUF YA LASHE GASAR RUBUTU TA PLEASANT DA MMB 2018



A ranar Juma'a 21-9-2018 a dakin karatu na PLEASANT LIBRARY AND BOOK CLUB dake Kaita Road jihar Katsina aka bayyana Kabiru Yusuf Fagge (wanda aka fi sani da Kabir Anka) a matsayin wanda ya lashe gasar gajerun labarai ta shekarar 2018.
Anka tare da sauran marubuta sun karbi kambin gasarsu tare da kyautuka nan take a hannun manyan shaihunan malaman da suka halarci taron.
Tun da farko Malam Mai Bazazzagiya ne ya bude taron da addu'a, sannan kai tsaye aka wuce da Jawabin Maraba ga bakin da suka halarci bikin bayar da kyautukan, inda Dr Abu Sabe Malami a Jami'ar Katsina ya tarbi bakin da maraba.

Tuesday, September 18, 2018

Book cover: WANDA KA RAINA


Hausa book cover: JAGORAN MAI ALWALA DA SALLAH


A DALILIN GULMA


A DALILIN GULMA
(c) Deejah Sharubutu

Short story: YA YA ZAN YI DA SOYAYYAR KAWAYE?


Na 
Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Ni kaina da abin ya faru a kaina na yi mamaki, amma daga baya sai na sami kaina a wani yanayi na rashin madafa ko fitar da sakamako na hakika, ba mamaki in sami wanda/wadda za ta sama min mafita.

Masoyiyata mai suna Abida Aliyu Barau mun dade da ita kmuna soyayya, tana sona don Allah nima ina sonta don Allah, iyayenmu da 'yan uwa da abokan arziki duk sun san wannan soyayya tamu kuma suna sa mana albarka a ciki, suna taya mu son junanmu, na zama dan gida a gidansu, itama ta zama 'yar gida a wurin iyayena da 'yan uwana. Tana son abin da nake so, nima ina son abin da take so.

Wannan tasa har aka amince min ina fito don aurenta a gidansu. Na fito din, na aika iyayena aka sa rana.

Saura wata daya da kwanaki goma sha uku a lissafe a daura aurenmu, muna zance Abida ta yi bakuwa, mai suna Surayya, wadda kai tsaye wurinmu ta nufo, suka gaisa da Abida, nima muka gaisa, suka dan yi hira kafin ta shiga da ita gida.

Tun zuwan Surayya da muka hada ido da ita na ji wani yanayi a zuciyata, wanda na rinka kokawa da shi, a karshe na tabbatar da mene ne a zuciyar tawa, wato so ne. To, a lokacin na lura, ita ma Surayya ta ji abin da na ji, irin kallon da na yi mata shi ta yi min.

Surayya babbar kawar Abida ce da suka yi karatu tare, sun rabu tsawon shekaru uku da suka wuce, ita ta tafi Misira, sai a wannan satin ta dawo.

Abu kamar wasa, karamar magana ta zama babba, kawai sai soyayya ta kankama tsakanina da Surayya, abin mamaki yadda na ganta ina sonta haka itama take sona. Kar ka yi tunanin cewa akwai wani dalili da ya sa na sota,  sam babu, kawia zuciyata ta ji tana son ta. Domin ba ta fi Abida komai ba, kai in takaita maka labari kyau da fari duk Abida ta fi ta.

Wani babban abin mamaki shi ne da na nutsu sai na ga cewar ban fifita son kowacce a kan kowacce ba a zuciyata, wato yadda nake son Abida haka nake son Surayya (wato 50-50) bambancin daya ne kawai, na riga son Abinda kuma mun fi dadewa da ita.

Wata rana na je gidan su Surayya muna hira, ta ke tambayata "Yanzu kana ganin babu matsala idan Abida ta gane muna soyayya? Ka san ni dai ba zan iya rabuwa da kai ba."

Na yi shiru kafin na ce, "Kar ki damu, zan tuntubeta game da hakan. Kin san dai yadda nake son Abida haka nake sonki." A zahiri kuma haka ne.

Washegari ranar da na je gidan su Abida da maganar, sai da ta yi jim tsawon lokaci kafin hawaye ya fito daga idanunta, ta ce "Kana ganin hakan ya yi daidai Suraj, shin kana ganin ka yi min adalci kenan. Ka san yadda kishi yake a zuci, ka san yadda zuciya take da kissime-kissime..." Ta kasa ci gaba saboda kuka da tasa.

Na ji matuka tausayinta a raina, ji na yi kamaar nima in tayata kukan. A wannan lokacin bamu kara cewa komai ba tsakanin ni da ita, abin yana damuna, ya zame min goma da ashirin.

Ya ya zan yi da wannan hali da na shiga? Kuma ya ya zan yi da soyayyar kawaye biyu aminan juna?

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...