DABARUN RUBUTA KAGAGGUN LABARAI -1
Zamu rinka gutsuro muku daga cikin wannan littafi mai suna a sama da marubuta: Ibrahim Muhd. Indabawa da Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Hanyoyin Samun Nagartaccen Labari Don Marubuta
A nan, wasu matakai ne da sabon marubuci ya kamata ya sani kuma ya kula da
su don inganta labarinsa.
(1) Jigo
Yana da matuqar muhimmanci marubuci ya kula da jigo wajen
gina labarinsa. Jigo a labari na nufin abin da labarin ke xauke da shi, ko kuma
saqon da marubuci ke son isar wa ga makarancinsa. Shin a kan me za ka yi
rubutun? Me ya ke xauke da shi? Fitar da jigon labari kan taimaka wa makaranci
sanin abin da labari yake qoqarin koyarwa.
A labari, ana samun babban jigo
da kuma qananan jigogi; misali kamar a samu jigon “haquri” sannan sai kuma
“qaddara” ko “afuwa” da sauransu.
(2) Jerantawar Vangarorin Labarin
Labari ingantacce, akan gina shi a kan vangarori aqalla
uku. Farko da tsakiya da kuma qarshe.
To, ta ya ya marubuci ya kamata ya jeranta labarinsa a kan
waxannan vangarori uku don labarinsa ya sami karvuwa? Akwai matakai guda uku a kowanne
daga waxannan vangarori guda uku; xaya a kowanne vangare guda xaya.
A vangare na farko, marubuci ya fara da bayyana wata
matsala ko wani rikici.
A vangare na biyu, wato na tsakiya, matsalar ta kai
qololuwa.
Yayin da a vangare na uku marubuci zai samar da mafita. A
babban littafi, marubuci zai iya saqa matsaloli da yawa, amma a guntun labari
ko qananan littattafai, dole ne matsalar ta zama guda xaya kawai.
(3) Ginin Labari
Marubuci zai fara da tunanin; shin a kan wane irin tauraro
zai gina labarinsa?
A kan mutum na farko ko na uku?
Labari a kan mutum na farko shi ne labarin da tauraron
labarin yake bayarwa da bakinsa. Don haka dole zai kasance a sigar
"na" ko "ina" ko kuma "na kasance" sannan dole ne
ya zamo tauraron ya kasance a duk inda abubuwan cikin labarin suka faru, ko
kuma a qalla ya zamana an ba shi labari shi ma.
Misali:
"Na kasance mutum mai sha'awar
wasanni. Wata ranar Asabar na shirya na fita zuwa filin qwallo…"
Ko kuma:
"Na durqusa na gaishe shi cike da
ladabi, yayin da yake amsa wa da qyar kamar ba ya so…"
Ko kaxan a irin wannan siga, bai kamata tauraro ya dinga
bayar da labarin abin da yake faruwa a wani waje da ba ya can ba, matuqar ba
labari aka ba shi ba. Don haka labarin zai zama kamar kai marubuci ne kake ba
da labarin kanka.
Sai kuma labari a kan mutum na uku. Shi kuma yana kasance
ta sigar "ya kasance" ko "ta kasance"
Misali:
"Aliyu ya kasance mutum mai
sha'awar wasanni. Wata ranar Asabar ya shirya ya fita zuwa filin qwallo…."
Ke nan, "na" za ta rikixe zuwa "ya" a
wannan salon.
Sannan marubuci ya yi tunani a kan, shin a sigar abin da ya
riga ya faru zai ba da labarin, ko kuwa a kan abin da yake faruwa? To a nan
dai, an fi rubutu a kan abin da ya riga ya faru, wanda shi ne ya fi sauqin shiryawa
(rubutawa).ZAMU CI GABA
No comments:
Post a Comment