Friday, August 24, 2018

Bikin Bayar Da Kyaututtuka Na Gasar Rubutun Gajerun Labarai Ta Pleasant Library and Books Da Makarantar Malam Bambadiya

Ibrahim Malumfashi

Yanzu zai gudana ranar 21 ga watan Satumba 2018
Kamar yadda aka sanar aka kuma alkawurta a baya, ga sakamakon gasar da ke kunshe da mutane 15 daga cikin 50 da alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda labaransu suka burge domin kasancewa wadanda za su fafata domin amsar kambin wannan gasa da za a yi yanzu a ranar 21 ga watan SATUMBA na 2018 in Allah a kai mu, a wani dan kwarya-kwaryan biki da za a yi a birnin Katsina
Wannan jadawali ba yana nufin shi ne sakamako na karshe ba, a’a, wadanda suka samu kai wa zagaye na karshe ne, daga cikin su za a bayyana na 1 zuwa na 3 wadanda za a ba awalajar N55,000 ga na daya, N35,000 ga na biyu sai N25,000 ga na uku. Sauran wadanda suka yi na 3 zuwa 12 za a ba kowannen su tukwicin N12,500.
Kamar yadda aka shelanta za a kuma tace da tsara da kuma buga wadannan labaran da suka ci gasar su 15, a matsayin littafi, a kuma kaddamar da su da yardar Allah.

Ga zakarun gasar:
1 Na'ima Abdullahi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Zagon Kasa
2 Kabir Yusuf Fagge Daga Jihar Kano, Taken Labari Matalauciyar Rayuwa
3 Zakariya Haruna Daga Jihar Kano, Taken Labari Da Sandar Hannunka
4 Fadila H. Kurfi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Rayuwar 'Ya Mace
5 Abubakar Yusuf Mada Daga Jihar Zamfara, Taken Labari Sauyin Rayuwa
6 Hamza Dawaki Daga Jihar Kano, Taken Labari Katantanwa
7 Ibrahim Babangida Suraj Daga Jihar Katsina, Taken Labari Hangen Dala
8 Hassana Abdullahi Hunkuyi Daga Jihar Kaduna, Taken Labari A Sasanta
9 Kabiru Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Ragguwar Dabara
10 Amina Sani Shu'aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Balaguron Talauci
11 Fatima Husaini Ladan Daga Jihar Katsina, Taken Labari Kowa Ya Bar Gida
12 Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano, Taken Labari Jamhuriyar Matalauta
13 Usman Muhammad Alqasim Daga Jihar Katsina, Taken Labari Dangina
14 Jamila Muhammad Lawal Daga Jihar Kaduna, Taken Labari Tsananin Talauci
15 Zaharadeen Nasir Daga Jihar Kano, Taken Labari Salmakal

Mun gode

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...