Friday, August 24, 2018

Short Story (Gajerun Labaru)

DANGIN AMARYA



 Na Kabiru Yusuf Fagge (Anka)
Haka yanayin marka-marka yake, yanzu ana ruwa, in an jima a tsagaita, ana kara jimawa ka ga ana sheka ruwa. Sam Ado Mai Walda ya tsani wannan yanayi, ya tsani wannan lokaci, domin lokaci ne da masu sana’ar walda irin shi ke shan wahala, suke shan kumaji na rashin samun aikin waldar a kai a kai. Sannan kuma idan ka samu kana yi, wuta na jan ka.
A yanzu da Ado Mai Walda ke zaune, ya yi jugum cikin tsammanin ‘Wa Rabbuka’, yana sauraron ko zai sami aiki, ita kuma amaryarsa Raliya tana can a gida tana nakuda. Watansu takwas da ‘yan kwanaki da yin aure, Allah ya albarkaceta da ciki, kuma haihuwa ta zo mata.
Allah da taimakonsa a daidai wannan lokaci, kanwar Ado, mai suna Abula, ta iso gidan Raliya, ta tarar da ita cikin wannan hali, da sauri ta fita, ta je ta nemo mota domin kai ta asibiti.
Abula ta samo motar, da taimakon wata mata, Abula suka sa Raliyar a motar. Wani karin sa’ar, a daidai wannan lokaci dangin amarya Raliya suka iso gidan cikin tawaga, su uku. Akwai yayar Raliyar mai suna Asabe, wadda ake yiwa lakabi da Asabe Guduma, sai kuma kanwar Raliya mai suna Minal, da kuma kanwar mahaifiyar su Raliyar, wato Gwaggo Agasha.
Wadannan tawagar Ado ya sha fama da su kafin da kuma baya daura masa aure da Raliya, da kyar aka samu aka yi auren, domin su Asabe Guduma suna hanawa, Allah yana hadawa, a karshe kowa ya san wanda zai yi nasara, aka yi auren.
Su Asabe suka karaso jikin motar cikin mamaki da damuwa, Asabe ce ta fara magana “Me ya faru, ba dai nakudar ba ce ta zo?”
Abula ta dubesu cikin damuwa, ta ce “Wallahi nakuda ce, shi ne na samo mota za mu kai ta asibitin Murtala.”
Asabe Guduma ta dakawa Abula tsawa gami da harara a lokaci guda, “Asibitin wa? Uban wa ya gaya miki danginmu ana kai su asibitin talakawa? Kauce nan ba mu wuri, koma cikin gida,  ki jire mata daki, International Hospital za mu kai ta.” Sai da Asabe ta shiga gidan, ta shiga dakin Raliya ta kare masa kallo, sannan ta fito.
Suka duru a cikin motar su uku, suka bar Abula nan a tsaye, suka nufi International Hospital.

Lokacin da Ado ya sami labarin an kai amaryarsa Raliya asibiti tana nakuda, a lokacin ana yayyafi, kuma a lokacin ya sami yin walda har ta Naira dari biyu da arba’in, amma wuta ta ja shi da ya kamata ace ya sha madara gwangwani biyu ta dari da tamanin. Ana yayyafi amma yana gumi, a haka ya kammala aikin, ya tattare kayansa, ya sa a jire masa, ya yi sauri a guje ya garzaya zuwa asibitin da aka ce an kai ta.
Da Asabe Guduma ya fara yin karo, kullum suka hadu sai ya ji gabansa ya fadi tamkar ta buga masa guduma. Tun asali, tun yana tsoronta, har ya dawo suna kar da kar da ita saboda rashin mutuncinta sam ba ta raga masa, har shima ya koyi rashin raga mata.
Tana murmushin da bai iya gane wane iri ba ne, suka hadu, ta mika masa katin asibiti. “Ai ta sauka lafiya, an sami mace, an gama komai, ga lissafinsu nan sai ka je ka biya su.”
Ado ya dubi katin, kai tsaye jimillar lissafin ya duba, ba zuciyarsa ba ce ta karanta yawan kudin ba, kwakwalwarsa ce, wato Naira dubu Hamsin da bakwai da dari uku, cajin komai da komai, karbar haihuwa, magunguna, gado da sauransu.
Ya so ya yi kwalla, ya riketa, ya so ya yi murmushi, nan ma ya makale shi, ya so ya yi dariya, anan ma ya guntse ta. Ya dubi Asabe.
“Ina fatan ita da ‘yar duk suna lafiya?”
Asabe ta harare shi, ta ce “Da ba sa lafiya, da ka ga ina kuka, amma tun da ka ga ina murmushi ai ka san ciki lafiya baka lafiya, sai lafiya kuma sai karin lafiya da biyansu kudinsu, kafin mu tafi gida.”
“To madalla.” Ado ya sami bakinsa yana fadin haka. Maimakon ya shiga dakin, kawai sai ya juya ya fice daga asibitin. Bai zarce ko’ina ba sai kasuwar Kurmi, ‘yan kwanuka. Ya samo mai siyen tangaraye da kwallaye. Suka shigo mota suka nufo gida, yana zuwa ya tarar da Abula zaune a dakin, suka gaisa. Sannan ya nunawa mai siyen tangaraye wadanda yake so ya siyar na dakin amaryarsa Raliya.
Da yake kasuwanci ne na mai bukata da wanda yake bukatar ya siyar, cikin kankanin lokaci suka daidaita, Ado ya sayar da tangarayen Raliya, aka biya shi. Kai tsaye ya koma asibiti ya biya kudin da aka tanada, ya sa ‘yan canjin a aljihu ya samo musu mota suka nufo gida. Asabe Guduma har habaici take yi masa, tana cewa “Ashe dai ana son haihuwa, ga kudi sun fito lakadan ba ajalan ba.”
Har lokacin da suka dawo gida da mai jego, Abula tana zaune a dakin tana jire wa, kamar yadda Asabe ta umarceta, lokacin da suka shiga, Minal ce a gaba, sai kuma Agasha wadda ke dauke da jaririya, sai kuma Asabe a bayan Agasha, yayin da Ado da Raliya suke bayan Asabe.
Suna shiga suka yi cirko-cirko gaba dayansu, saboda sun lura babu tangaraye a dakin, cikin tsawa da hargagi Asabe ta juyo ta kalli Ado ta ce “Kan uba, uban wa ye ya kwashe wadannan tangarayen na Raliya?”
Ran Ado a bace ya ce “Ubanki ne, don uwarki. Kuma wallahi kadan ma na diba, domin sai na dauki na ragon suna da ragowar hidindimun suna.”
Asabe Guduma ta kwance zani, ta yi damara. Ado ya nannade hannun riga.

Akwai ci gaba.

2 comments:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...