MAI MULKI BAYAN MULKI
Kabiru
Yusuf Fagge (Anka)
SHEKARUN
BAYA KAFIN IN ZAMA GWAMNA
Sai
da na hada kafafuna biyu iya karfina na take birkin sannan motar ta yi tutsu ta
tsaya, haka nake yi a kullum, domin rashin isasshen birki a motar, kar ka dauka
ban kai gyara ba, a'a kawai dai birkin ya lalace ne saboda tsufa, kuma ya ki
gyaruwa. Tsayawar da na yi hayaki ya cika motar da wajen ta, ni har na saba da
hakan. Gumi ya jika ni kamar daga dakin gasa burodi na fito.
Karo
na biyu, sai da na takarkare iya karfina na doki murfin motar da kafa sannan ta
bude, haka nake fama da ita, rufewa da kyar budewa ma da kyar. Na fito ina huci
kamar kumurci, kana na kalle ta kamar kullum idan na je na dawo nakan yi mata
kirari in ce:
“Rakyana
motar kara, motar Habu ki kaini da kyar ki dawo da ni da kyar, wannan bugun sai
mai jan hali.”
Tsohuwar
Bakswaja ce, kirar farko, ana tunanin ita ce ta farko da wani malalacin Baturen
Fotigal ya kera ta, an yi kiyasin ta girmi kakan kakana na uku.
Motar
ta yi lalacewar da wani bangare na injinta ba ya gyaruwa, irin su tafsalanda,
lagireto da sauransu.
Ta
yi kwararrabewar da gangar jikinta ba ya daukar fenti kofanal-bitin ko walda
sai dai na daure da igiya ko kebil. Ta yi tsananin da iyalaina ko abokaina ba
sa shigar ta don dai mu tafi unguwa in rage musu hanya, sun gwammace su tafi a kasa
komai nisan wurin.
Ka
san me ya jawo haka? Tambaya da amsa shi ne Kinko, Kinko dai shi ake kira Kuddaru
a wani lokacin a ce masa Nauyi, ko Morinho ko Girbau ko Kumaji ko ka fadi suna
gama-gari wato Talauci.
Malamin
makaranta ne ni, ina koyar da darasin Hausa, albashin fam dubu a wata bashin
jaka talatin, haka ake buge-buge, mata guda mai suna Talatu da 'ya'ya biyar,
abokai irina, imu-imu.
Sai
dai ina da gwagwarmaya a rayuwa, ina da tarar aradu da fadin kai idan ya yi
yawa in sa hannu in tallafe. A yanzu ni ne shugaban malamai masu neman karin
albashi da walwala.
Tafiya
tana mikawa, kwanaki na karewa, zabe ya tunkaro a mulkin dimokradiyya, haka
kawai 'yan ziga, 'yan tura lukuti ya hau tsauni, suka rinka tunzurani na tsaya
takara, wai ai ina da gwagwarmaya, kuma ina da mutane irin su malamai da dalibai
wadanda a cewar su, suna da yawa.
Kawai
kuma sai na amince, aka fara da tunani da shawarar in tsaya takarar ciyaman na karamar
hukumarmu, ni da mutanena muka ga ciyaman ya yi kadan, muka tafi batun dan
majalisar jiha, af shima ya yi kankanta a ganin mu, muka gangaro dan majalisar
tarayya, mun dan tsaya shawara, amma sai shima muka ga ai karamin alhaki ne,
domin baya mulkar jama'a sai wakilci, kawai muka debo ta da zafi, muka yanke
shawarar na fito takarar gwamna ko barazana ma yi.
Haka
aka yi, to a nan fa aka fara batun wacce jam'iyya zamu shiga, muka tantance
shiga jam'iyyar da ba ita take mulkin jiha ba, domin a nan zamu samu dama, haka
aka yi, muka shiga.
Allah
mai iko, sai ga ni na yi farin jini a wajen shugabannin jam'iyyar, sai dai kaka-tsara-kara
ga akuya ga kura, in ji mai wasa da kura, don jam'iyya dai tana da dan takarar
ta na gwamna.
Amma mai rabo ya kan samu rabo, a dalilin rashin
jituwa da shugabanni jam’iyya ke yi da dan takarar, sai ga su sun shiga sun
fita sun tsayar da ni takarar gwamna, ni dai na san an yi butulci, amma dai ina
da sa'a.
Siyasa
ta kankama a wajen Habu Dan Amadu, wato ni, zabe ya zo, muka yi 'yan dabarun mu
na jan hankalin mutane, kai gaskiya ma har da yaudara da bata gwamnati mai ci,
muka sami nasarar lashe zabe, Habu Dan Amadu sabon gwamna, ni na ke kiran kaina
da haka.
Aka
rantsar da ni, na rantse, gaskiya a lokacin da nake rantsuwar na tuno irin alkawuran
da na yiwa mutane, da wanda abokan kamfen dina suka yiwa mutane birni da kauye,
kuma zuciyata ta tabbatar min ba zan iya cikawa ba, kawai sai na ji hawaye yana
zubo min. Mutanena magoya baya suka yi kabbara, a tunanin su kukan dadi nake
yi, ba su san azaba nake tuna wa ba.
Azaba?
Ai ana fara mulki tuni na manta da ita, na manta da tsoffin abokaina, Rakyana
motata da wasu suke cewa motar kara ban san inda ta yi ba, ta yi nata gu. Kai
hatta matata Talatu da diyana guda biyu ganin su nake lokal.
Na
sake wanka, na sake abokai sabbi fil, wasu masu kudi suka rinka zuwa min da
tarihin cewar ni abokin su ne, mun hadu a makarantar allo kaza ko boko kaza,
wasu su ce min mun taba yin koyarwa tare. Akwai wanda ya same ni ya ce na taba
rage masa hanya, har ya yi min fatan zama gwamna, yanzu ga fatan sa ya cika a
kaina. Ka ji karya, ni wa na taba dauka a motata, wa kuma zai yi min fatan zama
gwamna ina matsiyaci? Karyar banza.
Na
yi sabbin 'yanmata biyu a matsayin matana, ban san yadda muka hadu ba, ni dai
ban ce ina so ba a zuciyata, kawai dai ina so ne saboda sabbin jini ne na aura.
Ita kuma ta ladan-noma na wato Talatu na daga mata jan kati da toshin dubu dari
biyu, a washegari na kuma daukar sabuwar amarya.
Mun
yi kwangilolin miliyan a biliyan, wannan aiki ne da aikatau. Babban abin da ya
ke bani mamaki a mulkina shi ne idan muka yiwa mutane aikin da nasu ne kuma kudinsu
ne sai in ji suna godiya a kafafen yada labarai. Alhalin a lokacin ina koyarwar
a makaratun firamare, babu uban yaron da ya taba yi min godiyar yau na koyawa dan
sa al'adun gargajiya.
Na
san akwai yabawa don a karfafawa mutum gwiwar rikon amana, amma mu sai ka ji
ana mana godiya kamar daga aljihunmu muka yi aikin.
Idan
ko ka fito ka ce bamu yi aiki ba, ko da ba mu yi din ba, to kaine abokin gabar
mu.
A
lokacin ina koyarwa duk kokarina wajen bayar da ilimi da gwagwarmaya babu wanda
ya taba bani wata kyauta ko hatimin yabawa ko girmamawa, babu wanda ya taba
rubuta tarihin rayuwata da kokarina don adanawa, amma a zama na gwamna ko
shekaru biyu ban rufa ba sai da na gina falon ajiyar award-award guda wanda saura
guda daya falukan su cika taf da takardar yabo ko girmamawa (certificate).
Littattafai
kuwa a kan tarihin rayuwata tun ina lissafawa da na kai guda saba'in da uku sai
na daina lissafawa, kowa da irin tarihin da yake bayarwa, wani ya ba shi suna
'Gwarzon Namiji', wani ya ba shi suna 'Gadamurkin Maza', wani ya ba shi suna
'Ka yi Taka...' wani ya rubuta 'Taka ba irin ta su ba' ga su nan dai barkatai.
Sarautun
gargajiya kuwa a matsayin girmamawa, wanda a da ban taba zaton zan zama cikin
fadawan sarki ba, ko da a garin Zariya sai gani da sarautun gargajiya
bila'adadin, ni ne 'Dan Zagalon Kano', ni ne "Kiki-Kakan Bauchi,' ni ne
'Goga-Masun Katsina' ni ne 'Jandarman' Maradi, ni ne 'Dan Bakwashen Sokoto' ni
ne 'Jinkau' din Jigawa, ni ne 'Taudon' Inugu, ni ne 'Shalelen Legas', ni ne
'Barden Kafancan' ni ne 'Jantarun Nupe’, kai har bana iya lissafawa, wata
sarautar ma ban san ma'anar ta ba, kuma ban san dalilin ba ni ita ba. A bangaren
makarantu na samu Dakta-Dakta, abin ba a cewa komai.
A
wani bangaren ga kudi a hannunmu, amma jama'a suna siyen filasta a asibitocinmu
mu kuma muna kai matanmu kasashen waje su haihu, ana mutuwa saboda rashin kayan
aiki a asibitocinmu, mu kuma muna kashe kudin kayan aikin a zazzabin 'ya'yanmu
a kasashen waje.
Kar
ka dauka ba ma aiki, muna yi gami da aikatau. A mulki, aiki da aikatau shi ne
ka yi aikin dubu dari ka dauki ribar miliyan daya da rabi, to irin aikin kenan.
Abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa.'
'Komai
ya yi farko yana da karshe, Allah ne kadai bai da farko ba a san karshen shi
ba. Mulki mai karewa ne, sai ga shi ya kare din, kamar wasa abin ke tafiya,
sannu a hankali fawa ta wuce gare ni, abokai suka fara nisa, ba a batun 'yan
jagaliya sun kauce, 'yan bambadanci masu yi min “sai ka yi” sun koma fadin
“bakka yi” masu fadin “honarabil” suka koma “kwanarabil” masu fadin Excellency suka
koma fadin cancellation abu ya zurme ya lalace.
Kar
ku yi zaton ban tara ba, na tara mana, sai dai yadda na siyo haka na siyar in
ji matar barawon da ta kai hajar sa kasuwa aka sace, yadda na sami kudin haka
suka kare, abin da na shuka shi na girba.
Na
zama butal a yanzu, farin cikina daya ne na gane kurena na yi nadama, kuma ina
fatan Allah ya yafe min, in samu sassauci a ranar bayanin da babu boye-boye,
ranar tsayawa a gaban sarki mai mulkin da baya karewa. Kuma na gode Allah da ya
bar ni da hikima da fasahata ta rubutu, nake fatan marubuta su taimaka min su
amsa min wasu ‘yan tambayoyina, su kuma tallafa min da tallafin rayuwa don mu
ganar da al'umma.
*Shin
me ya faru a wasu damina-damina da aka yi ruwa mai iska, sai ka tarar da gida
ginin mahadi-ka-ture ya rushe, amma gidan kara yana tsaye kikam?
*Me
ya sa shugabanni irin namu na yanzu, ko masu kudi ba sa iya fitowa kofar
gidansu su shimfida tabarma ko katifarsu su kwanta zuwa asuba ba? Amma sai ka
ga talakawa birjik kwance wasu har safiya.
*Me
ya sa shaidar saukar Alkur'ani ga Musulmi ko shaidar haddace Bible ga Kirista
ba ya baiwa mutum lasisin tsayawa takara ko da ta kansila ne sai dai shaidar
boko?
Naku
tsohon Gwamna, Habu Dan Amadu
No comments:
Post a Comment