Wednesday, August 29, 2018

Short story: MAKAUNIYA





A short story
 

MAKAUNIYA




 “Da iyayen nawa, da dukkannin wasu ‘yan uwana, da dangina da kowa da ka sani na tsane su, ba na kaunarsu.” Na ce da Amadu, ina fitar da hawaye.
“Kar ki ce haka Zaliha, ita rayuwar nan ba ta kai gurin da ki ka kai ta ba, ba ta kai matsayin da ki ka dauketa ki ka dorata ba...” Amadu yana kokarin fada min haka, na dakatar da shi ba tare dana waiwayi inda yake ba, ko na waiwaya ba ganin shi zan yi ba, ba idanu.
“Ka fi ni sanin cewa ina da hujjar fadar haka. Dole tsinuwa ta tabbatar ga al’umma na kusa da na nesa.” Na yi shiru ina shisshika.
“Kar ki manta makanta da Allah ya dora miki ba yana nufin ya fifita sauran mutane masu gani a kan ki ba ne, da har za ki dauki mugun tunani na  dora wa sauran mutane laifi. Lokacin da ke, ki ke a matsayin makauniya, wasu na can, ba sa gani kamar yadda ba kya gani, ba sa tafiya, ba su da hannun dauka ko karba, sun rasa abubuwa da dama fiye da ke, sun kasance makafi, guragu, kutare...Amma ke fa? Ido kawai ki ka rasa.” Cewar Amadu, yana kokarin lallashina.
Na girgiza kai, “Ka ga duk wannan wani kwaskwarima kake yi ga danwaken da ba ya jin gishiri bare maggi. Bari in gaya maka mai gaba daya, bari in yi maka ta babban mahaukaci, Allah, Allah, wallahi tallahi, a yanzu na dauki rayuwata a matsayin ba ni da kowa sai kai, kai kadai da kake kulawa da ni da rayuwata. A yau da zan sami idon gani, to zan daukeka a matsayin uwa da uba ne, za ka zama miji a gareni, kuma madafin dafa rayuwata, ba ruwana da kowa bare kowan kowa, kai kadai ne nawa, kai ne mijina, kai ne ni.”
Amadu ya yi shiru, wannan ya tabbatar min ya gamsu da maganata, koda yake Amadu yana son ya ji na ce ina son shi, bare kuma in ce ya dauka kamar ni matarsa ce. Na tabbatar dadin da yake ji, ya fi gaban in misalta, ina ma ina gani, da na ga irin kyakkyawan murmushin jin dadin da yake wanzuwa a fuskarsa.
*
Ina ya Allah, babu ya Allah. Kwanci tashi, wata rana Allah ya turo da daya daga cikin hanyoyinsa, kawai wasu Larabawa, irin masu taimakawa din nan, bisa tsari da koyarwar addinin Musulunci, masu bi gari-gari suna taimakawa marasa lafiya irin wadanda rashin kudi, ko rashin kulawa ko kwararrun ma’aikata a Nijeriya ya sa suke zaune da cutuka a jikunansu. Suka sauka a unguwarmu.
Allah da taimakonsa, ina daya daga cikin wadanda suka sami ni’ima ta addinin Musulunci, cikin kwanaki uku da yi min aikin idanuna, wanda ban taba zaton zan kara gani ba, suka bude. Allah kenan, mai cuta da maganinta. Sai gani ina gani, sai gani ina kiftawa, sai gani ina ganin rahamar Ubangiji. Alhamdulillahi. Sai me, Amadu.
Na san babu wanda zai fi kowa farin ciki da samun ido da ya zarta Amadu, kai ni kaina ba dan kar a ce na yi son kai ba, sai in ce Amadu zai fi ni farin ciki da budewar idanuna. “Wayyo Allah, ina Amadu nawa.” Haka nake ta fada ina murmushin jin dadi.
Ban ga Amadu ba sai bayan kwana daya da budewar idanuna, wanda nake ganin Amadu ya yi min nisa har, farin cikin na neman disashewa. Da na ga Amadu sai na rasa inda zan sa raina, na rasa a wacce irin duniya nake tsakanin ta takaici da bakin ciki, tsakanin mummuna da kazama?
“Yanzu ashe Amadu makaho ne, baya gani? To ni me zan yi da makaho? Ina kyakkyawa, wallahi ba zai yiwu ba, ba zan taba auren Amadu makaho ba, haba! Sam wallahi.” Na fashe da kuka, na wuce shi, har da hankade shi, ya fadi, na yi tafiyata, ko kallon wajen ban kara yi ba.




No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...