Thursday, August 23, 2018

SAKAMAKON GASAR BITA DA KWAS NA RUBUTA GAJERUN LABARAI NA PLEASANT LIBRARY DA MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA

Ibrahim Malumfashi

Kamar yadda aka sanar, aka kuma alkawurta a baya, an shirya wannan gasa ne domin bukatar samar da labaran nishadi cikin Hausa da ke kunshe da matsalolin karantar da darussan Lissafi da Kimiyya da Ingilishi don yara da ke zangon karatu na Firamare da shekara 3 na farkon Sakandare. Wadannan labarai za a samar da su ne domin kyautata da inganta karatu da nakaltar darussan tsakanin malamai da dalibai na kasar Hausa.
Tun da farko an yi tsari ne da zai samar da marubuta 20 da za su halarci kwas na musamman bayan tantance wadanda suka aiko da samfurin labaransu, amma alkalan gasar sun zabo labarai 10 ne kawai daga cikin 75 da suka ga sun hau mizanin da masu ruwa da tsaki na shirya gasar suka tanada.
Yanzu ga sakamakon gasar da ke kunshe da sunayen mutane 10 da alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda labaransu suka burge, suka kuma cancanci zuwa zagaye na karshe don halartar kwas na musamman kan sanin makamar rubuta gajeren labari domin dalibai, kamar yadda aka tsara.

Baki Abin Magana Na Umar Saleh Gwani Daga Jihar Bauchi
Baya Ba Zane Na Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano
Karambani Da Karambana Na Bello Hamisu Ida Daga jihar Katsina
Keke Babbar Haja Na Danladi Zakariyya Haruna Daga jihar Kano
Kilikinji Na Maryam Umar Daga Jihar Sokoto
Lokaci Bako Na Abdullahi Hassan Yarima Daga Jihar Kano
Riga-Kafi Ya Fi Magani Yazid Nasudan Daga Jihar Katsina
Tubalin Toka Na Nafisa Abubakar Daga Jihar Katsina
Tafiyar Marar Wuri Abdurrahaman Aliyu Daga Jihar Katsina
Ina Matsalar Take? Bamai Dubawa Daga Jihar Jigawa

Wadannan zakakuran marubuta za su halarci kwas na musamman don bitar yadda ake tsara gajerun labarai da suka shafi Ilimin kimiyya da Lissafi da Ingilishi na kwana 2 da za a yi a birnin Katsina daga ranakun 21 da 22 ga watan Satumbar 2018, in Allah ya kai mu.
Ana sa ran wadanda suka halarci kwas din su koma gida su kammala rubutun labaran nasu zuwa watan Disambar 2018. Za a ba da awalajar N30,000 ga kowane gamsasshen labari da aka aminta da shi. Za a kuma tace da tsara da kuma buga labaran, a kuma kaddamar da su a wani dan kwarya-kwaryar biki da za a shirya a Katsina, da yardar Allah.
Mun gode.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...