Short story
SERGENT BURTU ON DUTY
Kabiru
Yusuf Fagge (Anka)
Babu
gurin da Sajen Burtu ke bukatar a tura shi aiki irin gurin da ya tabbatar akwai
maiko a gurin, to shi ko da ya ya ne a tura shi.
Sajen
Burtu ya saba shige da fice, ya saba bayar da cin hanci ga S.O. (Station
Officer) mai yin posting domin a tura shi guraren da ya tabbatar ko da
tsiya-tsiya ko ta halin-kaka sai ya tunbatso aljihunsa, ya dawo yana murza
gashin baki.
Sai
dai kuma Sajen Burtu gwani na gwanaye ne gurin rowa, duk yaran da aka tura shi
da su to dan abin da ya ke ba su bai taka kara ya karya ba, sai dai kuma yana
da kokarin bayar da cin hancin Naira dari in har zai sami Naira dubu.
Hausawa
na cewa wanzam bai son jarfa, wata ranar Alhamis daga cikin ranekun aikin Sajen
Burtu, duk dibishin din su aka sami labarin, don haka S.O. Karba-Karba ya nemi
shima ya tsakuri wani abu daga cikin abin da Sajen Burtu din ya kaso.
Kememe
Sajen Burtu ya ki amincewa, karshe ma cewa "Ni fa ban yi eating din
noise ba. A wannan ranar, kawai dai na san wani Alhaji ya tsaya a cikin
tafkekeiyar motarsa 'End of discussion' ya yi mana alherin Naira
ashirin, to da ita na tashi, ta ya ya za wa wani sani a gaba wai sai na bada
wani abu?"
Wannan
rainin hankalin ya baiwa S.O. Karba-karba haushi, don haka da ya tashi yin posting
a ranar sai ya yi posting din Sajen Burtu zuwa Kankare Road, titin da ya
tabbata a bushe ya ke karaf, domin kafin ka ga mota da ta fi tsoffin Kiya-kiya
da Akori-kura sun wuce ta titin sai bayan watanni shida, shima sai ranar da
Barista Muhammadu Lawandi ya dawo hutu gida a motar sa Odyssey. To fa in ban da
ita, sai kuma tarin jakuna da suke safa da marwa.
Don
haka S.O. ya san babu maiko a gurin, kuma ya hadashi da 'yan sanda guda uku, da
direba daya wadanda ya san suma kar-ta-san-kar ne a gurin kudi, ta haka ya ke
sa ran hukunta Sajen Burtu. Sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne, shi Sajen
Burtun din da kansa ya ke samowa kansa maiko a yayin aiki ko a ina ne, sai dai
idan babu mutane a gurin.
Sai
misalin karfe goma sha biyu Sajen Burtu da yaransa, su Kofir Kaukau, da
Kurata Bala Baushe, Gabros Money Monger
da direban Bash Aljihun Baya, suka isa Kankare Road. Ganin yanayin titin ya
tabbatarwa da Sajen Burtu, lallai babu mamora, domin kadas titin yake, to amma
ya, ya iya tunda dan iskan Isfektan ya turo shi gurin, kuma ba damar ya bashi
cin hanci a wannan lokacin domin abin da ya faru tsakanin su.
Sun
kai mintuna arba'in ba tare da wani mai abin hawa ya zo ya wuce ba, in ka dauke
masu tafiya a kasa, sai wani dan acaba, dan caburos da ya wuce su a guje, bayan
ya yi musu dogon haske.
Shi
kansa Sajen Burtu ya san yau ranar a bushe ta ke, don haka har ya saduda sai ya
hango hasken fitilar mota, ajiyar zuciya ya yi gami da godiya ga Allah, ya
umarci yaransa yana cewa.
'Get
ready for duty'
Yana
zaune a cikin motarsu ta aiki a gidan gaba, motar ta silalo zuwa inda su Kofur Kaukau
suke tsaye a tsakiyar titi sun tsare hanya, Kofur Kaukau ne ya leka gurin mai
motar.
"Yallabai
daga ina haka cikin tsohon daren nan? Ka fa sabawa doka."
Mutumin
dake cikin motar ya dubi agogonsa sannan ya dubi Kofur Kaukau din.
"Wallahi
wani muhimmin abu ne ya tsayar da ni a hanya, amman yanzu ina kusa da
gida."
"No
ni cewa na yi ka sabawa doka, don haka kawai ka san abin yi." Cewar Kaukau.
"To
me ya kamata in yi kenan?" Ya tambaya, da alama ya dauki haske ga abin da
Kofur din ke nufi.
Da
hanzari Kofur din ya kara yin alama ta gaba, "Ka ganmu kawai ka wuce, mu
gaisa."
Ya
zura hannu a cikin dan akwatin motar ya dukunkuno wani abu ya mikawa Kofur Kaukau
a dukunkune, shima ya karba a dukunkune sannan ya yi murmushi.
"You
less go." Wato yana ba shi damar tafiya ne a zaton shi. Shi kuma ya
juya, ya bar gurin. Maimakon ya nufi gurin da Sajen Burtu ke zaune, sai ya
zagaya jikin wata katanga kamar mai shirin yin fitsari, ya dan kare kansa,
sannan ya bude abin da mai motar ya bashi a dukunkune da nufin ya dauki nashi
kason kafin ya kaiwa Sajen Burtu kason bai-daya.
Yana
dubawa, sai ya ga ashe (katin adireshi da suna ne) complimentary, ya bude
shi cikin mamaki da takaicin raina masa hankali da aka yi, ya haska da tocilat din
hannun sa, abn daya gani a rubuce ya so firgita shi, ya san sunan, wato Barista
Muhammadu Lawandi ne, tsohon AIG na kasa, yanzu kuma babban lauya, shugaban
lauyoyi masu zaman kansu.
Sum-sum
ya kudundune katin, ya nufi gurin Sajen Burtu, ya mika masa katin a kudundune
bayan ya sara masa ya ce "Sir, bakonka ne." Domin ya hangoshi a tsaye
bai tafi ba.
Sajen
Burtu ya kware wajen damkar kudi, ya kan iya bambance Naira ashirin, goma,
biyar, hamsin, dari daya, biyu, biyar da dubu, to bare takarda, don haka abin
da aka bashi a dukunkune, nan da nan ya bambance cewar takarda ce, don haka ya
yi saurin dubawa. Shima ya karanta abin da Kofur Kaukau ya karanta, sai ya yi
saurin iko masa ya ce.
"Munafuki,
bakonka ne dai, ai ina ganin lokacin da ka tafi can ka duba, wato da kudi ne da
yawa da sai abin da ka bamu kenan ko, to ka yi karya sai ka je ka sallame shi,
ni ba ruwana."
Kaukau
ya sara "Yes sir, zan je in ce ka ce ya zo." Bai jira abin da zai ce
ba, ya nufi gurin da motar Barista ta ke. Burtu ya san zai iya aikatawa don aka
ya yi hanzarin bin sa, suka je gaban motar, inda Baristan yake suka sara a
tare.
Kafin
su ce komai Barista Lawandi ya ce musu "Ga katina nan ku sameni a gida
gobe karfe daya." Ya ja motar, ya wuce.
Nan
suka tsaya kikam kamar gumaka, can Sajen Burtu ya yi ajiyar zuciya gami da shekawa
Kaukau mari "Munafuki, Allah ya tsine maka."
Kaukau
ya sara ya ce "Yes sir, ya kuma tsine mana."
A
lokacin wani hasken motar ya kuma ratso tsakankaninsu, nan da nan suka kauce
daga kan titin da nufin baiwa motar hanya ta wuce kar a kuma. Ba sai ganin wata
kwaababbiyar Kiya-kiya suka yi ba, tana tafiya da kyar tana nishi da gurnani.
Cikin sauri, Bala Bushe ya nufi motar yana ihun tsayar da ita.
"Wet,
wet." A tunanin sa "Wait ya ke fadi." Ita kuwa baiwar
Allah tun kafin direbanta ya tsayar da ita ta kafe cak, tana hayakin gajiya.
Gaba
dayansu suka yi kan motar, ganinta makare da kaya, sai direba da kwandastansa
da ke zazzaune a gaban motar. Yuuu suka isa gaban motar.
Bala
Bushe ne ya fara magana "Me ku ka dauko haka, na smuggle ko?"
Direban
da kwandastansa, sun san ba kayan laifi ba ne face buhunan gyada da suka dauko,
don haka kwandastan ya ga cewar ba laifi bane idan ya ba da amsa a turance
cikin nishadi, don haka ya ce.
"Na
gurnet insiyet."
Razana
ta zowa kafatanin 'yan sandan, Bala Bushe ya yi karfin hali ya kuma tambaya
"Me ka ce?"
"Ai
se na gurnet buhu-buhu a cikin motar." Shi kam kwandasta so ya ke ya
ce gyada ce a ciki, wato groundnut a turance, shi ne yake cewa gurnet
cikin rashin sani.
Sajen
Burtu ya maimaita kalmar "Gurnet!"
Kwandastan
bai yi kasa a gwiwa ba ya kuma jaddadawa "Yes sir."
Kafin
ya yi kif da bakinsa su Sajen Burtu sun bazama da gudu, har daya na tunkude daya.
Domin shi Bala Bushe ma can ya yi tsalle kusa da motarsu ya fadi yana dafe da
kansa, don ya san da wuya ya kai ba tare da gurnet din ya tashi da su
ba.
Kiya-kiyar
nan ma da kanta ta finciki kanta da gudu, tana kugi, to ya za ta yi dan wani ma
ya yi rawa bare dan makadi, 'yan sanda ma sun guru bare ita, da gudu kwandastan
ya cimmata, domin shima aikin sa ne.
No comments:
Post a Comment