Monday, August 27, 2018

Gajeren Labari: MIJIN MATATA


Gajeran Labari
 
MIJIN MATATA
Kabiru Yusuf Fagge (anka)

Karfe goma sha daya da mintuna na dare na dawo gida. Ni kaina na san na dawo a makare, amma dai na sanar wa matata Balaraba cewa yau ba zan dawo gida da wuri ba, kuma ta ce ba komai tun da yanayin aiki ne ya sa.
Bayan na daidaita motata a ma’ajinta, na kashe, na dauki jakata da ke gefe, sannan na bude kofa na fito, na kulle motar na nufi cikin gida.
A kofar shiga na yi sallama har sau uku ba a amsa min ba, na shiga cikin gidan, a daf da kofar dakin Yayana Badamasi ma na tsaya, na kuma yin sallamar, a nan ma ba amsa, amma dai ga muryar shi nan, shi da matata Balaraba ina ji suna hira cikin raha suna dariya ta nishadi.
Cikin damuwa na wuce, na nufi dakinmu.
Gidanmu gidan gado ne, iyayenmu suka mutu suka bar mana mu uku, ni da yayana Badamasi da kanwarmu Baraka, ita tana aure a Portharcout. Dakin farko a nan yayana yake zaune, tsohon dan boko ne, ya kai shekaru hamsin bai yi aure ba,  sai boko. Daki na can cikin gidan kuwa, nawa ne da matata muke zaune.
Na karasa falonmu na jefa jakata a kan kujera, na bi ta na zauna a gefe, cikin bacin rai, na yi tagumi ina tunanin me Balaraba da Badamasi ke nufi a cikin daren nan ace matar wani da wani kato a daki guda suna hira irin wannan?
Haka nan na yi sakato - ina tunani, raina yana kuma baci, ina tsumayin in ga lokacin da za ta komo. Mintuna talatin da hudu suka gifta Balaraba ba ta dawo ba, kuma har yanzu ina jiyo tashin hirarsu ta nishadi.
Da na ga abu ba na karewa ba ne wai an ba wawa damar yiwa sarki habaici, sai na mike, na fita, na nufi dakin Yaya Badamasi, na tsaya a kofar dakin na yi sallama. Alamu suka nuna ba su ji ni ba saboda shewa da suke yi.
Na takarkare tun karfina na kuma rangada sallamar. Suka ji ni, don haka suka yi shiru, amma ba su amsa ba, Balaraba ce ta daga labule ta fito, tana kallona sai ta fara murmushi.
“Yanzu ka dawo? Sannu da zuwa sweetheart. Ina jakar taka?” Duk cikin feleke da tarairaya take maganar.
Ban ce mata komai ba, na juya na nufi daki, ta biyo ni a baya tana surutu, ita da alama ma ba abin da ya dame ta.
“Lallai yau aiki ya yi maka yawa. Da ace ana zuwa da aikin gida ai da ka taho da shi na rinka rage maka.”
Na yi banza da ita, na shiga daki, na zauna a kan kujera, na yi shiru, ina tunanin ta inda zan fara mata. Ta sami wuri itama ta zauna, tana kallona da idanun kissa da feleke.
Darling da alama, yau ka wahala a aikin nan. Wai ya na ga ka yi shiru?”
Na yi tsaki, na kalle ta na ce “Wai ke Balaraba mene ne hadin ki da Yaya Badamasi?” Wannan ne karo na farko da na kirata da sunanta tun da muka yi aure, amma sai dai in ce sweetheart  ko darling ko my heart ko my lobe da sauransu.
Ta kyalkyale da dariyar nishadi, ita ma a karon farko ta kira sunana, ta ce “Haba Bello, wai kai ganina a dakin Yayanka ne ya sa ranka ya baci, har da yi min tsaki da kiran sunana gatse-gatse haka?”
Ta kuma maskewa da dariya, ta ce “Kawai fa ganin shi na yi shi kadai a daki cikin kadaici, shi ne na je ina debe masa kewa, to mene ne abin damuwa a ciki? Yaya Badamasi fa dan boko ne, ba ruwan shi da irin abin da kake tunani. Uhm, wallahi ni yadda nake ji hatta wanka ma Yaya Badamasi zai iya yi min, kuma ba wani abu. Haba don Allah darling, ka daina irin wannan tunani, ai mu’amalata da Yaya Badamasi mutu-ka-raba, ya iya zama da jama’a, kuma ya iya tafiyar da ni da jin dadina.”
Duk harafi daya na maganarta kara min takaici take, wai ita wannan wacce irin mata ce haka? Ana fatan a nuna mata munin da ke cikin mu’amalarta da wani namiji tana kara shisshigewa.
Na mike rai a bace, na shige dakina na fada kan gado a gajiye, a fusatance, ko kayan jikina ban cire ba.
Tunani na shiga yi, tunanin irin wannan badakala ta mu’amala da sau tari nake gani tsakanin matata Balaraba da Yayana Badamasi. Mu’amala ce irin ta mata da mijin da suka shaku da juna, suka waye, amma a kebe tunda Hausawa ne, yadda wani ba zai gansu ba.
Na taba zuwa na tarar da su a kicin din shi Yaya Badamasin wai tana taya shi girki, suna yi suna hira ta jin dadi da nishadi, Yaya Badamasi har da dan dukanta a duwawu da ludayin miya, suka yi dariya.
Sannan akwai ranar da na tarar da su a tsakar gida a kan tabarma suna hira, da hirar ta yi dadi suka yi shewa, suka tafa.
Haka nan wata rana da marece yaya Badamasi yana koya mata karatu, yana siffanta mata yadda za ta furta wata kalma, har da kama mata leben sama da na kasa na bakinta yana gwada mata practically.
A wata rana ma, idan har ba idanuna bane suka yi min gizo ba, na taba tarar da su suna wasan langa da wasan ‘yar goyo.
Hawayen takaci ya biyo idanuna, na ci gaba da tunani, wai shi Yaya Badamasi an ce masa haka bokon take, ta hana mutum aure, kuma ya rinka wasa da matar wani ba tare da damuwa ba?
Can a cikin tunane-tunane na, na juya na ga Balaraba a kwance a bayana, raina ya baci matuka, na juya mata baya.
Bayan kamar mintuna biyar na juyo don a yi ta, ta kare, sai na ga wayam ba ta nan. Na mike tsam, na nufi falo na duba, bata falon, na je dakinta na duba, a nan ma bata nan.
Na nufi dakin Yaya Badamasi, ko sallama ban yi ba, ina zuwa na bankada labule, na tura kai.
Balaraba na gani a kwance a gefen Badamasi sun yi rigingine suna kallon sama suna hira suna dariya.
Da suka ganni babu wanda ya damu bare su razana, Yaya Badamasi ya ci gaba da hirarsa, ita kuma Balaraba ta kalle ni ta ce “Sorry sweetheart, yau hira nake so, kai kuma na ga fushi ka ke ji, shi ne na taho nan muke hira da Yaya.”
Zuciyata na ji kamar za ta faso kirjina ta faso don haushi. Wai ya ya zan yi da wannan matar tawa?


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...