Thursday, August 30, 2018
Hausa novel
SANADIN KENAN!
Dr. Turaki ya yi murmushi yana duban Amina a tsanake, cikin kwantaccen sauti ya ce da ita "As a doctor, ba sai na gaya miki yadda zaki yi da patients dinki ba, but wannan patient din....needs extra more..... Saboda marainiya ce. Sannan lafiyarta (matters a lot to her Dad)."
Zai nutsu ne kadai wajen aikin al'ummarsa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu, kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa da kafafuwanta. "Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye zaki dinga magana da His Excellency in kuna buqatar wani abu ko sanar dashi wani abu daya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and the best physiotherapist as we know... Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa".
Tunda ya fara bayanin Dr. Amina bata ce komai ba, tunani kawai take cikin zuciyarta, ta mika masa wayar, ya karba ya sanya, ya mayar mata ta adana lambar cikin wayarta. A ranta ta san ta karba ne kawai amma ba zata taba iya kiran MA'AROUF JI-KAS ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, akan dalilin da ba zata ce mene ne shi ba. Duk da zasu kasance gida daya. Shi din dai (Turakin) zata cigaba da baiwa jakadancin ko yana so ko baya so!!!
-Takori
Alkalan Hikayata na 2018 sun tantance labarai 25
Alkalan uku sun tattauna ne don bambance tsaki da tsakuwa a kan wadanda ko wannensu ya riga ya zaba a matsayin labarin da ya ciri tuta.
Alkalan su ne Farfesa Ibrahim Malumfashi, masani, masharhanci, kuma babban malamin adabin Hausa a Jami'ar Umaru Musa 'yar'adua da ke Katsina, da Dokta Halima Abdulkadir Dangambo, malamar adabi a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami'ar Bayero ta Kano, da kuma Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, fitacciyar marubuciya, kuma mai sharhi a kan adabin Hausa.
Nan ba da jimawa ba ne dai za a sanar da marubuciyar labarin da alkalan suka zaba a matsayin Tauraruwar Hikayata ta bana.
Wannan ne dai karo na uku da ake shirya wannan gasa da nufin bai wa mata damar bayyana abubuwan da ke damunsu a rayuwa.
A bara dai Maimuna Idris Sani Beli ce ta lashe gasar, kuma ta samu kyautar kudi dalar Amurka 2,000 da lambar yabo.
Labaran da alkalan Hikayata suka duba:
- Aurena 12
- Alhaki
- Alheri
- Bakar Rana
- Barin Kashi a Ciki A
- Barin Kashi a Ciki B
- Da Kyar Na Sha
- Da Na Sani
- Duniyata
- Har Yanzu Ana Yi
- Illar Talla
- Kalubale
- Kulu
- Kururuwar Iblis
- Kwaya
- Laifin Suna
- Lauren Tirmi
- Matallafina
- Nadama
- Nakasa Ba Kasawa Ba
- Rubutaccen Al'amari
- Sunanmu Daya
- Waye Sila
- 'Ya Mace
- Zaina
Littafin
SHATA IKON ALLAH!
(Rayuwar Mamman Shata Katsina)
Na
IBRAHIM SHEME
*LITTAFIN "SHATA IKON ALLAH!" YA FITO*
Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!
Bayan na shafe shekara 12 ina aiki kan sake rubuta shahararren littafin nan na tarihin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina, da zurfafa bincike a kan rayuwar sa, a yau dai Allah (SWT), mai kowa mai komai, ya yi ikon sa, littafi ya shigo hannu na. An kammala dab'in sa da shirya shi a bisa sabon fasalin da ya dauka. Allah na gode maka!
SHATA IKON ALLAH!
(Rayuwar Mamman Shata Katsina)
Na
IBRAHIM SHEME
*LITTAFIN "SHATA IKON ALLAH!" YA FITO*
Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!
Bayan na shafe shekara 12 ina aiki kan sake rubuta shahararren littafin nan na tarihin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina, da zurfafa bincike a kan rayuwar sa, a yau dai Allah (SWT), mai kowa mai komai, ya yi ikon sa, littafi ya shigo hannu na. An kammala dab'in sa da shirya shi a bisa sabon fasalin da ya dauka. Allah na gode maka!
Wannan littafi, wanda Shata da kan shi ne ya ba ni izinin rubuta shi,
ya bambanta da wanda na jagoranci rubutawa a baya, wato wanda ya fito a
shekarar 2006. Ko makaho ya shafa, zai ji bambancin. Ya inganta ta
fuskar kyautata bincike da nazari, ya inganta ta fuskar yawan shafuka,
ya inganta ta fuskar kyan dab'i, ya inganta ta wajen yawan shafuka.
Shafi 921 ne. Akwai shafi 32 masu dauke da hotuna masu kala, wadanda aka buga kan takarda mai santsi.
A cikin littafin, akwai hotuna guda 580. A cikin su, akwai hotuna masu kala har 98.
Babu littafin da na taba shan wuyar rubutawa kamar wannan. Na yi yawo a garuruwa da kauyuka. Na kashe kudi ban san adadin su ba. Na rika zama a tebur, a gaban komfuta, daga safe zuwa karfe 2 na dare, na tsawon watanni, na hana kai na more rayuwa yadda ya kamata, kafin wannan aiki ya kammala. Sannan na sha fama da masu cewa don Allah yaushe wannan littafi zai fito? Masoyan kenan. Na sha fama da masu zunden cewa na rike littafi, na hana shi fitowa. To, Allah ya yi - wai aure da mara kwabo - a yau ga kwafen littafin ya shigo hannu na.
To yaushe zai shiga kasuwa? Ai har ma ya shiga, domin kuwa ko a gobe za mu iya sayar da shi ga duk mai so.
Addu'a ta ita ce Allah ya sa a ce gara da aka yi. Allah ya sa albarka.
Allah ya jikan Alhaji Muhammadu Shata, amin.
Ibrahim Sheme
Shafi 921 ne. Akwai shafi 32 masu dauke da hotuna masu kala, wadanda aka buga kan takarda mai santsi.
A cikin littafin, akwai hotuna guda 580. A cikin su, akwai hotuna masu kala har 98.
Babu littafin da na taba shan wuyar rubutawa kamar wannan. Na yi yawo a garuruwa da kauyuka. Na kashe kudi ban san adadin su ba. Na rika zama a tebur, a gaban komfuta, daga safe zuwa karfe 2 na dare, na tsawon watanni, na hana kai na more rayuwa yadda ya kamata, kafin wannan aiki ya kammala. Sannan na sha fama da masu cewa don Allah yaushe wannan littafi zai fito? Masoyan kenan. Na sha fama da masu zunden cewa na rike littafi, na hana shi fitowa. To, Allah ya yi - wai aure da mara kwabo - a yau ga kwafen littafin ya shigo hannu na.
To yaushe zai shiga kasuwa? Ai har ma ya shiga, domin kuwa ko a gobe za mu iya sayar da shi ga duk mai so.
Addu'a ta ita ce Allah ya sa a ce gara da aka yi. Allah ya sa albarka.
Allah ya jikan Alhaji Muhammadu Shata, amin.
Ibrahim Sheme
Wednesday, August 29, 2018
Short story: MAKAUNIYA
A short story
MAKAUNIYA
“Da iyayen nawa, da dukkannin wasu ‘yan uwana,
da dangina da kowa da ka sani na tsane su, ba na kaunarsu.” Na ce da Amadu, ina
fitar da hawaye.
“Kar ki
ce haka Zaliha, ita rayuwar nan ba ta kai gurin da ki ka kai ta ba, ba ta kai
matsayin da ki ka dauketa ki ka dorata ba...” Amadu yana kokarin fada min haka,
na dakatar da shi ba tare dana waiwayi inda yake ba, ko na waiwaya ba ganin shi
zan yi ba, ba idanu.
“Ka fi
ni sanin cewa ina da hujjar fadar haka. Dole tsinuwa ta tabbatar ga al’umma na
kusa da na nesa.” Na yi shiru ina shisshika.
“Kar ki
manta makanta da Allah ya dora miki ba yana nufin ya fifita sauran mutane masu
gani a kan ki ba ne, da har za ki dauki mugun tunani na dora wa sauran mutane laifi. Lokacin da ke,
ki ke a matsayin makauniya, wasu na can, ba sa gani kamar yadda ba kya gani, ba
sa tafiya, ba su da hannun dauka ko karba, sun rasa abubuwa da dama fiye da ke,
sun kasance makafi, guragu, kutare...Amma ke fa? Ido kawai ki ka rasa.” Cewar
Amadu, yana kokarin lallashina.
Na
girgiza kai, “Ka ga duk wannan wani kwaskwarima kake yi ga danwaken da ba ya
jin gishiri bare maggi. Bari in gaya maka mai gaba daya, bari in yi maka ta
babban mahaukaci, Allah, Allah, wallahi tallahi, a yanzu na dauki rayuwata a
matsayin ba ni da kowa sai kai, kai kadai da kake kulawa da ni da rayuwata. A
yau da zan sami idon gani, to zan daukeka a matsayin uwa da uba ne, za ka zama
miji a gareni, kuma madafin dafa rayuwata, ba ruwana da kowa bare kowan kowa,
kai kadai ne nawa, kai ne mijina, kai ne ni.”
Amadu ya
yi shiru, wannan ya tabbatar min ya gamsu da maganata, koda yake Amadu yana son
ya ji na ce ina son shi, bare kuma in ce ya dauka kamar ni matarsa ce. Na
tabbatar dadin da yake ji, ya fi gaban in misalta, ina ma ina gani, da na ga
irin kyakkyawan murmushin jin dadin da yake wanzuwa a fuskarsa.
*
Ina ya
Allah, babu ya Allah. Kwanci tashi, wata rana Allah ya turo da daya daga cikin
hanyoyinsa, kawai wasu Larabawa, irin masu taimakawa din nan, bisa tsari da
koyarwar addinin Musulunci, masu bi gari-gari suna taimakawa marasa lafiya irin
wadanda rashin kudi, ko rashin kulawa ko kwararrun ma’aikata a Nijeriya ya sa
suke zaune da cutuka a jikunansu. Suka sauka a unguwarmu.
Allah da
taimakonsa, ina daya daga cikin wadanda suka sami ni’ima ta addinin Musulunci,
cikin kwanaki uku da yi min aikin idanuna, wanda ban taba zaton zan kara gani
ba, suka bude. Allah kenan, mai cuta da maganinta. Sai gani ina gani, sai gani
ina kiftawa, sai gani ina ganin rahamar Ubangiji. Alhamdulillahi. Sai me, Amadu.
Na san
babu wanda zai fi kowa farin ciki da samun ido da ya zarta Amadu, kai ni kaina
ba dan kar a ce na yi son kai ba, sai in ce Amadu zai fi ni farin ciki da
budewar idanuna. “Wayyo Allah, ina Amadu nawa.” Haka nake ta fada ina murmushin
jin dadi.
Ban ga
Amadu ba sai bayan kwana daya da budewar idanuna, wanda nake ganin Amadu ya yi
min nisa har, farin cikin na neman disashewa. Da na ga Amadu sai na rasa inda
zan sa raina, na rasa a wacce irin duniya nake tsakanin ta takaici da bakin
ciki, tsakanin mummuna da kazama?
“Yanzu
ashe Amadu makaho ne, baya gani? To ni me zan yi da makaho? Ina kyakkyawa,
wallahi ba zai yiwu ba, ba zan taba auren Amadu makaho ba, haba! Sam wallahi.”
Na fashe da kuka, na wuce shi, har da hankade shi, ya fadi, na yi tafiyata, ko
kallon wajen ban kara yi ba.
Tuesday, August 28, 2018
Kai ma ka dara: SERGENT BURTU ON DUTY
Short story
SERGENT BURTU ON DUTY
Kabiru
Yusuf Fagge (Anka)
Babu
gurin da Sajen Burtu ke bukatar a tura shi aiki irin gurin da ya tabbatar akwai
maiko a gurin, to shi ko da ya ya ne a tura shi.
Sajen
Burtu ya saba shige da fice, ya saba bayar da cin hanci ga S.O. (Station
Officer) mai yin posting domin a tura shi guraren da ya tabbatar ko da
tsiya-tsiya ko ta halin-kaka sai ya tunbatso aljihunsa, ya dawo yana murza
gashin baki.
Sai
dai kuma Sajen Burtu gwani na gwanaye ne gurin rowa, duk yaran da aka tura shi
da su to dan abin da ya ke ba su bai taka kara ya karya ba, sai dai kuma yana
da kokarin bayar da cin hancin Naira dari in har zai sami Naira dubu.
Hausawa
na cewa wanzam bai son jarfa, wata ranar Alhamis daga cikin ranekun aikin Sajen
Burtu, duk dibishin din su aka sami labarin, don haka S.O. Karba-Karba ya nemi
shima ya tsakuri wani abu daga cikin abin da Sajen Burtu din ya kaso.
Kememe
Sajen Burtu ya ki amincewa, karshe ma cewa "Ni fa ban yi eating din
noise ba. A wannan ranar, kawai dai na san wani Alhaji ya tsaya a cikin
tafkekeiyar motarsa 'End of discussion' ya yi mana alherin Naira
ashirin, to da ita na tashi, ta ya ya za wa wani sani a gaba wai sai na bada
wani abu?"
Wannan
rainin hankalin ya baiwa S.O. Karba-karba haushi, don haka da ya tashi yin posting
a ranar sai ya yi posting din Sajen Burtu zuwa Kankare Road, titin da ya
tabbata a bushe ya ke karaf, domin kafin ka ga mota da ta fi tsoffin Kiya-kiya
da Akori-kura sun wuce ta titin sai bayan watanni shida, shima sai ranar da
Barista Muhammadu Lawandi ya dawo hutu gida a motar sa Odyssey. To fa in ban da
ita, sai kuma tarin jakuna da suke safa da marwa.
Don
haka S.O. ya san babu maiko a gurin, kuma ya hadashi da 'yan sanda guda uku, da
direba daya wadanda ya san suma kar-ta-san-kar ne a gurin kudi, ta haka ya ke
sa ran hukunta Sajen Burtu. Sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne, shi Sajen
Burtun din da kansa ya ke samowa kansa maiko a yayin aiki ko a ina ne, sai dai
idan babu mutane a gurin.
Sai
misalin karfe goma sha biyu Sajen Burtu da yaransa, su Kofir Kaukau, da
Kurata Bala Baushe, Gabros Money Monger
da direban Bash Aljihun Baya, suka isa Kankare Road. Ganin yanayin titin ya
tabbatarwa da Sajen Burtu, lallai babu mamora, domin kadas titin yake, to amma
ya, ya iya tunda dan iskan Isfektan ya turo shi gurin, kuma ba damar ya bashi
cin hanci a wannan lokacin domin abin da ya faru tsakanin su.
Sun
kai mintuna arba'in ba tare da wani mai abin hawa ya zo ya wuce ba, in ka dauke
masu tafiya a kasa, sai wani dan acaba, dan caburos da ya wuce su a guje, bayan
ya yi musu dogon haske.
Shi
kansa Sajen Burtu ya san yau ranar a bushe ta ke, don haka har ya saduda sai ya
hango hasken fitilar mota, ajiyar zuciya ya yi gami da godiya ga Allah, ya
umarci yaransa yana cewa.
'Get
ready for duty'
Yana
zaune a cikin motarsu ta aiki a gidan gaba, motar ta silalo zuwa inda su Kofur Kaukau
suke tsaye a tsakiyar titi sun tsare hanya, Kofur Kaukau ne ya leka gurin mai
motar.
"Yallabai
daga ina haka cikin tsohon daren nan? Ka fa sabawa doka."
Mutumin
dake cikin motar ya dubi agogonsa sannan ya dubi Kofur Kaukau din.
"Wallahi
wani muhimmin abu ne ya tsayar da ni a hanya, amman yanzu ina kusa da
gida."
"No
ni cewa na yi ka sabawa doka, don haka kawai ka san abin yi." Cewar Kaukau.
"To
me ya kamata in yi kenan?" Ya tambaya, da alama ya dauki haske ga abin da
Kofur din ke nufi.
Da
hanzari Kofur din ya kara yin alama ta gaba, "Ka ganmu kawai ka wuce, mu
gaisa."
Ya
zura hannu a cikin dan akwatin motar ya dukunkuno wani abu ya mikawa Kofur Kaukau
a dukunkune, shima ya karba a dukunkune sannan ya yi murmushi.
"You
less go." Wato yana ba shi damar tafiya ne a zaton shi. Shi kuma ya
juya, ya bar gurin. Maimakon ya nufi gurin da Sajen Burtu ke zaune, sai ya
zagaya jikin wata katanga kamar mai shirin yin fitsari, ya dan kare kansa,
sannan ya bude abin da mai motar ya bashi a dukunkune da nufin ya dauki nashi
kason kafin ya kaiwa Sajen Burtu kason bai-daya.
Yana
dubawa, sai ya ga ashe (katin adireshi da suna ne) complimentary, ya bude
shi cikin mamaki da takaicin raina masa hankali da aka yi, ya haska da tocilat din
hannun sa, abn daya gani a rubuce ya so firgita shi, ya san sunan, wato Barista
Muhammadu Lawandi ne, tsohon AIG na kasa, yanzu kuma babban lauya, shugaban
lauyoyi masu zaman kansu.
Sum-sum
ya kudundune katin, ya nufi gurin Sajen Burtu, ya mika masa katin a kudundune
bayan ya sara masa ya ce "Sir, bakonka ne." Domin ya hangoshi a tsaye
bai tafi ba.
Sajen
Burtu ya kware wajen damkar kudi, ya kan iya bambance Naira ashirin, goma,
biyar, hamsin, dari daya, biyu, biyar da dubu, to bare takarda, don haka abin
da aka bashi a dukunkune, nan da nan ya bambance cewar takarda ce, don haka ya
yi saurin dubawa. Shima ya karanta abin da Kofur Kaukau ya karanta, sai ya yi
saurin iko masa ya ce.
"Munafuki,
bakonka ne dai, ai ina ganin lokacin da ka tafi can ka duba, wato da kudi ne da
yawa da sai abin da ka bamu kenan ko, to ka yi karya sai ka je ka sallame shi,
ni ba ruwana."
Kaukau
ya sara "Yes sir, zan je in ce ka ce ya zo." Bai jira abin da zai ce
ba, ya nufi gurin da motar Barista ta ke. Burtu ya san zai iya aikatawa don aka
ya yi hanzarin bin sa, suka je gaban motar, inda Baristan yake suka sara a
tare.
Kafin
su ce komai Barista Lawandi ya ce musu "Ga katina nan ku sameni a gida
gobe karfe daya." Ya ja motar, ya wuce.
Nan
suka tsaya kikam kamar gumaka, can Sajen Burtu ya yi ajiyar zuciya gami da shekawa
Kaukau mari "Munafuki, Allah ya tsine maka."
Kaukau
ya sara ya ce "Yes sir, ya kuma tsine mana."
A
lokacin wani hasken motar ya kuma ratso tsakankaninsu, nan da nan suka kauce
daga kan titin da nufin baiwa motar hanya ta wuce kar a kuma. Ba sai ganin wata
kwaababbiyar Kiya-kiya suka yi ba, tana tafiya da kyar tana nishi da gurnani.
Cikin sauri, Bala Bushe ya nufi motar yana ihun tsayar da ita.
"Wet,
wet." A tunanin sa "Wait ya ke fadi." Ita kuwa baiwar
Allah tun kafin direbanta ya tsayar da ita ta kafe cak, tana hayakin gajiya.
Gaba
dayansu suka yi kan motar, ganinta makare da kaya, sai direba da kwandastansa
da ke zazzaune a gaban motar. Yuuu suka isa gaban motar.
Bala
Bushe ne ya fara magana "Me ku ka dauko haka, na smuggle ko?"
Direban
da kwandastansa, sun san ba kayan laifi ba ne face buhunan gyada da suka dauko,
don haka kwandastan ya ga cewar ba laifi bane idan ya ba da amsa a turance
cikin nishadi, don haka ya ce.
"Na
gurnet insiyet."
Razana
ta zowa kafatanin 'yan sandan, Bala Bushe ya yi karfin hali ya kuma tambaya
"Me ka ce?"
"Ai
se na gurnet buhu-buhu a cikin motar." Shi kam kwandasta so ya ke ya
ce gyada ce a ciki, wato groundnut a turance, shi ne yake cewa gurnet
cikin rashin sani.
Sajen
Burtu ya maimaita kalmar "Gurnet!"
Kwandastan
bai yi kasa a gwiwa ba ya kuma jaddadawa "Yes sir."
Kafin
ya yi kif da bakinsa su Sajen Burtu sun bazama da gudu, har daya na tunkude daya.
Domin shi Bala Bushe ma can ya yi tsalle kusa da motarsu ya fadi yana dafe da
kansa, don ya san da wuya ya kai ba tare da gurnet din ya tashi da su
ba.
Kiya-kiyar
nan ma da kanta ta finciki kanta da gudu, tana kugi, to ya za ta yi dan wani ma
ya yi rawa bare dan makadi, 'yan sanda ma sun guru bare ita, da gudu kwandastan
ya cimmata, domin shima aikin sa ne.
Monday, August 27, 2018
Gajeren Labari: MIJIN MATATA
Gajeran Labari
MIJIN MATATA
Kabiru Yusuf Fagge (anka)
Karfe goma
sha daya da mintuna na dare na dawo gida. Ni kaina na san na dawo a makare,
amma dai na sanar wa matata Balaraba cewa yau ba zan dawo gida da wuri ba, kuma
ta ce ba komai tun da yanayin aiki ne ya sa.
Bayan na daidaita motata a ma’ajinta, na kashe, na dauki jakata da ke gefe,
sannan na bude kofa na fito, na kulle motar na nufi cikin gida.
A kofar shiga na yi sallama har sau uku ba a amsa min ba, na shiga cikin
gidan, a daf da kofar dakin Yayana Badamasi ma na tsaya, na kuma yin sallamar,
a nan ma ba amsa, amma dai ga muryar shi nan, shi da matata Balaraba ina ji
suna hira cikin raha suna dariya ta nishadi.
Cikin damuwa na wuce, na nufi dakinmu.
Gidanmu gidan gado ne, iyayenmu suka mutu suka bar mana mu uku, ni da
yayana Badamasi da kanwarmu Baraka, ita tana aure a Portharcout. Dakin farko a
nan yayana yake zaune, tsohon dan boko ne, ya kai shekaru hamsin bai yi aure
ba, sai boko. Daki na can cikin gidan
kuwa, nawa ne da matata muke zaune.
Na karasa falonmu na jefa jakata a kan kujera, na bi ta na zauna a gefe,
cikin bacin rai, na yi tagumi ina tunanin me Balaraba da Badamasi ke nufi a
cikin daren nan ace matar wani da wani kato a daki guda suna hira irin wannan?
Haka nan na yi sakato - ina tunani, raina yana kuma baci, ina tsumayin in
ga lokacin da za ta komo. Mintuna talatin da hudu suka gifta Balaraba ba ta
dawo ba, kuma har yanzu ina jiyo tashin hirarsu ta nishadi.
Da na ga abu ba na karewa ba ne wai an ba wawa damar yiwa sarki habaici,
sai na mike, na fita, na nufi dakin Yaya Badamasi, na tsaya a kofar dakin na yi
sallama. Alamu suka nuna ba su ji ni ba saboda shewa da suke yi.
Na takarkare tun karfina na kuma rangada sallamar. Suka ji ni, don haka
suka yi shiru, amma ba su amsa ba, Balaraba ce ta daga labule ta fito, tana
kallona sai ta fara murmushi.
“Yanzu ka dawo? Sannu da zuwa sweetheart. Ina jakar taka?” Duk cikin
feleke da tarairaya take maganar.
Ban ce mata komai ba, na juya na nufi daki, ta biyo ni a baya tana surutu,
ita da alama ma ba abin da ya dame ta.
“Lallai yau aiki ya yi maka yawa. Da ace ana zuwa da aikin gida ai da ka
taho da shi na rinka rage maka.”
Na yi banza da ita, na shiga daki, na zauna a kan kujera, na yi shiru, ina
tunanin ta inda zan fara mata. Ta sami wuri itama ta zauna, tana kallona da
idanun kissa da feleke.
“Darling da alama, yau ka wahala a aikin nan. Wai ya na ga ka yi
shiru?”
Na yi tsaki, na kalle ta na ce “Wai ke Balaraba mene ne hadin ki da Yaya
Badamasi?” Wannan ne karo na farko da na kirata da sunanta tun da muka yi aure,
amma sai dai in ce sweetheart ko darling
ko my heart ko my lobe da sauransu.
Ta kyalkyale da dariyar nishadi, ita ma a karon farko ta kira sunana, ta ce
“Haba Bello, wai kai ganina a dakin Yayanka ne ya sa ranka ya baci, har da yi
min tsaki da kiran sunana gatse-gatse haka?”
Ta kuma maskewa da dariya, ta ce “Kawai fa ganin shi na yi shi kadai a daki
cikin kadaici, shi ne na je ina debe masa kewa, to mene ne abin damuwa a ciki?
Yaya Badamasi fa dan boko ne, ba ruwan shi da irin abin da kake tunani. Uhm,
wallahi ni yadda nake ji hatta wanka ma Yaya Badamasi zai iya yi min, kuma ba
wani abu. Haba don Allah darling, ka daina irin wannan tunani, ai mu’amalata
da Yaya Badamasi mutu-ka-raba, ya iya zama da jama’a, kuma ya iya tafiyar da ni
da jin dadina.”
Duk harafi daya na maganarta kara min takaici take, wai ita wannan wacce
irin mata ce haka? Ana fatan a nuna mata munin da ke cikin mu’amalarta da wani
namiji tana kara shisshigewa.
Na mike rai a bace, na shige dakina na fada kan gado a gajiye, a fusatance,
ko kayan jikina ban cire ba.
Tunani na shiga yi, tunanin irin wannan badakala ta mu’amala da sau tari
nake gani tsakanin matata Balaraba da Yayana Badamasi. Mu’amala ce irin ta mata
da mijin da suka shaku da juna, suka waye, amma a kebe tunda Hausawa ne, yadda
wani ba zai gansu ba.
Na taba zuwa na tarar da su a kicin din shi Yaya Badamasin wai tana taya
shi girki, suna yi suna hira ta jin dadi da nishadi, Yaya Badamasi har da dan
dukanta a duwawu da ludayin miya, suka yi dariya.
Sannan akwai ranar da na tarar da su a tsakar gida a kan tabarma suna hira,
da hirar ta yi dadi suka yi shewa, suka tafa.
Haka nan wata rana da marece yaya Badamasi yana koya mata karatu, yana
siffanta mata yadda za ta furta wata kalma, har da kama mata leben sama da na kasa
na bakinta yana gwada mata practically.
A wata rana ma, idan har ba idanuna bane suka yi min gizo ba, na taba tarar
da su suna wasan langa da wasan ‘yar goyo.
Hawayen takaci ya biyo idanuna, na ci gaba da tunani, wai shi Yaya Badamasi
an ce masa haka bokon take, ta hana mutum aure, kuma ya rinka wasa da matar
wani ba tare da damuwa ba?
Can a cikin tunane-tunane na, na juya na ga Balaraba a kwance a bayana,
raina ya baci matuka, na juya mata baya.
Bayan kamar mintuna biyar na juyo don a yi ta, ta kare, sai na ga wayam ba
ta nan. Na mike tsam, na nufi falo na duba, bata falon, na je dakinta na duba,
a nan ma bata nan.
Na nufi dakin Yaya Badamasi, ko sallama ban yi ba, ina zuwa na bankada
labule, na tura kai.
Balaraba na gani a kwance a gefen Badamasi sun yi rigingine suna kallon
sama suna hira suna dariya.
Da suka ganni babu wanda ya damu bare su razana, Yaya Badamasi ya ci gaba
da hirarsa, ita kuma Balaraba ta kalle ni ta ce “Sorry sweetheart, yau
hira nake so, kai kuma na ga fushi ka ke ji, shi ne na taho nan muke hira da
Yaya.”
Zuciyata na ji kamar za ta faso kirjina ta faso don haushi. Wai ya ya zan
yi da wannan matar tawa?
Subscribe to:
Posts (Atom)
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA
RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...