SHARHI A KAN RUBUTUN FIM, NA BALA ANAS
BABINLATA
Daga
Yusuf M. Adamu PhD, MNAL
Sashen Labarin Qasa, Jami’ar Bayero,
Kano
GABATARWA
Rubutu, shi ne ginshikin duk wani
abu na kirkira a harkar adabi. Sai an rubuta za a karanta, sai an rubuta za a
baddala, sai kuma an rubuta sannan za a sarrafa. Mai harkar fim, ba zai iya
samar da komai ba har sai an rubuta masa me zai samar. Koda yana da
masaniyar me yake so ya haska, hakan
ba za ta samu ba har sai an rubuta. Wannan
rubutu shi ne turken da ake daure
duk wani aiki da za a yi na fim, musamman ma na
labari. Marubucin tun farko ya yi kokarin
bambance rubutun zube da na fim, ya nuna cewa shi na zube ana rubuta shi cikin
tunanin marubuci ta yadda an ba marubuci da
makaranci damar tunanin yadda
taurari da wuraren da aka yi amfani da su suke, ta
haka, kowa zai iya bada na sa
tunanin koda kuwa marubucin ya bada siffar wuri ko
taurari. Bayan haka, babu ruwan
marubucin zubi da tunanin ta yaya za a nuna ko
maida labarinsa hoto, don haka yana
da ‘yanci fiye da na marubcin fim wanda kamar
yadda marubucin wannan littafi ya
fada a shafi na 15 sakin layi na daya "…shi kuwa
rubutun fim, ya kunshi ginin labari
ne da hotuna…" don haka shi wannan rubutu kusan
hoto ake so ya bada shi ba marubucin
ba. Ta yadda koda ba ka jin harshen ko kuma ba
murya, hoton zai iya bada labarin.,
ya bada misalai da dama a cikin littafin wanda ke
nuna yadda mai rubuta fim ke magana
da mai daukar hoto kai tsaye, ba mai kallo ba, bambancin rubutun zube wanda
marubucin na magana ne kai tsaye da mai karatu.
RUBUTA LABARINKA
Marubucin wannan littafi ya yi
amfani da fina-finan hollywood wajen bada misalansa, amma ya yi togaciya da
cewa ba wai don babu finan-finan kannywood da zai iya bada
misali da su ba ne illa, yana so ne
misalan su fito daga fina-finai na silima ba home
videos ba, saboa burin marubucin shi
ne nan gaba Hausawa su rika yin fina-finai don
duniya ta fuskar silima ba home
video ba. Marubucin ya kawo misalin taswirar labari wato synopsis wadda za a yi
amfani da ita domin jan hankali mai zuba jari da kuma bada labarin fim din a takaice
kamar haka:
1. Mene ne rukunin labarin?
2. Wane ne tauraron labarin?
3. Mene ne burin tauraron labarin (a
labarin)?
4. Mene ne cikas ga burinsa (a
labarin)?
5. Mene ne muhimmamncin Labarin?
In dai mai rubuta labarin fim zai
iya samar da wannan to ya kamo hanyar cin nasara.
SAMAR DA TAURARO KO TAURARUWA A
LABARIN FIM
Ya yi bayani da zai taimakwa mai
rubuta labari yadda zai samar da tauraro ya kuma
gina shi ta yadda zai iya aikin da
ake so ya aiwatar a labarin. Abin lura a nan shi ne mai rubuta labari kamar
yadda masu nazari su kan ce, shi ne Ubangijin labarinsa da.. abinda ya kunsa, don haka, dole ai rubutun fim ya san
tauraronsa ciki da bai (p21) ta haka ne zai ba mai shirya fim ya san wani
jarumi ne zai iya hawan wannan tauraro da marubuci ya kirkira, saboda ba da ka
ake yin abin ba. Ba kuma farkawa daga barci mai shirya fim zai yi ya ce wane zo
ka hau tauraro ka a ba don kawai yana son shi ko don in ya sa shi zai samu kudi
ba. Shi marubuci shi ke fidda siffofi da dabi’u da zai samar da tauraro ko tauraruwa.
Wannan magana ce mai muhimmanci domin in mun lura da finan-finan kannywood,
akan yi casting taurarin da ba su dace da role a fim ba, musamman taurari mata.
Sai ka ga an ga mata ganda-ganda a matsayin ‘yan mata da ba su yi aure ba. Ko a
sa wadda ba ta dace da labarin ba ko shi ma jarumin a sa wanda sam bai hau kan
labarin ba. Ina ganin wannan ne ya sa marubucin wannan littafi ya fara da
buxewa da wannan muhimmiyar magana. Marubucin ya fitar filla-filla yadda ake
gina tauraro ta yadda zai hau kan lokaci da yanayi na labarin ba tare daan samu
matsala ba. Ya kawo misalin yadda ya kamata mai rubutu ya sa wa tauraro ko
tauraruwa sunan da ya dace da kuma fahimtar tarihinsa da na iyayensa da
shekarunsa lokacin da aka fara labarin da sauyin da zai iya samu bayan shekaru
da halayya da sauransu.
MAZAUNIN BINCIKE A RUBUTA LABARIN
FIM
In dai ba labarin kansa marubuci zai
bayar ba, to gudanar da nazari da bincike ya zama wajibi a gare shi, kai ko
labarin kansa zai bayar in dai ya hado da wasu a ciki sai ya zurfafa bincike.
Marubucin wannan littafi watau Babinlata ya jaddada muhimmancin a samu fahimtar
batutuwan da za a kawo a labarin don ya dace da zahiri da kuma abinda hankali
zai yadda da shi. Ta haka, mai rubutu sai ya yi nazari mai zurfi akan lafazi,
ma’ana yadda jinsunan mutane ke magana. Misali, maganar yaron dan shekara
bakwai ba za ta yi dai dai da mutum dan shekara talatin ba, haka ta dan shekara
talatin ba za ta yi dai-dai da ta dan shekara sittin ba. Maganar malamin makaranta
ba za ta yi dai-dai da ta dan siyasa ba ta yadda maganar alaramma ba za ta zo
daidai da ta dan daba ba. Bincike ne kawai zai bada damar a fahimci wannan.
Matukar ba a yi bincike ba, sai ka ji likita na magana kamar ta dan kasuwa ko
ka ji Sarki na maganar kamar wani shugaban Karamar Hukuma. Amma Babinlata ya ce
kada mai rubuta labari ya vata lokaci akan lafazi har sai ya tabbatar da cewa
labarin ya zauna da kafarsa. Amma kuma kada ya manta bai dawo ya tsefe shi ba.
Tsarin Rubuta Labarin Fim (Script)
Babinlata ya ce duk lbaran fim iri daya
ne. A nan ba yana nufin cewa labari iri daya ake bayar wa, illa salon rubuta
labarin na bin matakai iri daya ne. A nan ina ganin marubucin na son jan
hankali ne ga jigon labari wanda zai iya zamowa daya amma yadda aka warware shi
kuma ya zama daban. Ya kuma yi ikirarin cewa kowane irin labari za ka rubuta ko
kuma salo da za ka yi amfani da shi, akwai fina-finai dubbai da za ka iya kalla
don su haska maka hanyar da za ka bi ka samu sauki. Ya ce ba yana nufin ka sata
ba, a’a ka dai yi dauraya ko wankiya. A nan, ya kamata a fahimci abin da Babinlata
yake nufi, a fahimta ta, yana nufin kada marubuci ya dauka ba wanda ya taba
magana akan jigon da yake so magana a kai ko kuma salon da yake son amfani da
shi. Hausawa na cewa, da na gaba ake ganin zurfin ruwa Jera labari
Daga shafi na 45-51, ya bada yadda
ake jera labari filla-filla ta hanyar bada bayanin
akan ko me zai faru daga minti na
farko zuwa minti na 110, daga farko zuwa karshe
kenan, kamar dai yadda maru rubuta
labari suke tsara littafi babi-babi. Rukunan Labarai
Babinlata ya kawo rukunan labarai
har guda tara kamar haka:
1. Soyayya
2. Barkwanci
3. Yaki
4. Bantsoro
5. Almara
6. Kirji-dar-dar
7. Tarihi
8. Tashin hankali
9. Labari cikin waka
Amma ya ce wannan na masu kallo ne
ba na mai rubutu ba ne, ya ce ga mai rubutu kamata ya yi amfani da wasu rukunan
da za su taimaka masa wajen fadada tunaninsa don hawa turba mikakkiya. Ya ce
Mr. Snyder wanda Ba’amurke ne da abokan aikinsa sun bada shawarar marubuci ya
yi amfani da wadannan rukunai. Wadannan rukunai da aka gina mafi yawancin
littafin sune kamar haka:
1. Farautar Bajinta
2. Soyayya Gamon Jini
3. Hadadden Bagidaje
4. Bin-kwakkwafi
5. Tsuntsun da Ya Ja Ruwa
6. Gwarzon Sadauki
7. Gaye Cikin Matsala
8. Matakan Yaye
9. Tsafi Gaskiyar Mai shi
10. Rantswarwa
Wannan ya nuna kenan shi marubucin
fim, idan ya tashi rubutu, wadannan rukunai za su iya zamar masa jagora.
Babinlata ya yi bayani dalla-dalla akan wadannan rukunai da ya bayar a sama. Ga
kowane rukuni a bada tarin yadda salon ya samu asali. Misali rukunin Farautar
Bajinta wanda nake tunanin yana nufin Adventure kenan, labari ne da neman suna
da arziki a uwa duniya, ya karkasa shi zuwa nau’i-nau’i kamar haka:
1. Aboki da Aboki
2. Bajintar Sadaukantaka
3. Kai Kadai Gayya
4. Gasar Bajinta
5. Bajintar Barayi
A misalan da ya sun hada da misalan
fina-finai kamar Finding Nemo (Aboki da Aboki) da Bajintar Sadaukantaka wanda
ya ce labarai ne da akasari na yaqi ne ko kwato wani abu da aka rasa ya kawo
misalan waxannan fina-finai kamar Star Wars, National Treasure, Lord of the
Rings da sauransu. Akwai kuma labaran Kai Kadai Gayya inda akan samu wani
sadauki irin su Iliya Dan Mai Karfi wanda ya amsa sunansa, ya kawo misalai
kamar su Cast Away da Cold Mountain. Da sauransu. Sauran Rukunonin da ya kawo
ma ya sake farfasa su domin saukakawa mai karatu da mai koyo, misali, a kashin
Soyayya Gamon Jini wanda ya ce harka ce ta ‘Rayuwata ta sauya saboda na gamu da
wane, ko saboda na gamu da wance. A karshen kowane labari sauyi kan faru ga
Tauraro ko Tauraruwa a wata gaba dalilin afkuwar wani abu. A labarai rukunin
Soyayya Gamon Jini sauyi kan faru ne ga Tauraro ko Tauraruwa dalilin gamuwa da
wani ko Wata’ (Sh. 67) ya kawo kashi-kashi irin su tauraro Warin-takalmi da
Abokin Burmi da Cikas da
haramtacciyar soyayya da sauransu.
Ya kawo misalin fina-finanda suka dace a kowane aji don mai karatu ya fahinci
yadda abin yake. Ya bada misalan fina-finai kamar su Gone with the Wind da
Lethal Weapon da The Proposal Da dai sauransu. A kashi na uku kuma na Hadadden
Bagidaje ya bayyana cewa ‘Wannan rukunin labaran yafi karfi a labaran
Barkwanci. Labarai ne salon Beran Kauye a Birni. Wato gabotarin kauye a Birni,
saboda kallon dogwayen gine-gine har hularsa ta fadi kasa. Tauraro ko
Tauraruwar Hadadden Bagidaje suke zama gidadawa idan suka samu kansu a wani
waje da ya sha bambam da salon rayuwarsu, ko ya shallake tunaninsu’ (sh. 84). A
nan ya farfasa wannan kashi ta hanyar fidda kananan rukunai kamar su wawan
sarki da wawan vadda-bami da wawan gari da wawan jinsi da sauransu. Ya kuma
bada misalan fina-finai kamar su Meet John Doe da Trading Places da I am Sam da
The Party da Coming to America da sauransu. Na gaba kuma shi ne sashen da ya
tattauna wani karamin kununin watau Bin Kwakkwafi wanda ya bayyana da cewa
‘Labaran dake wannan rukunin cike suke da Wane ne? Mene ne? Ina ne? Yaushe ne?
Ta yaya? Cike yake da tarin tambayoyi masu bukatar amsoshi.’ (sh.94). Ya
karkasa shi zuwa wasu azuzuwa kamar su mai bincike da kasada da kwakkwafi da
Bin Kwakkwafin ‘yan sanda da sauransu ya kuma kawo misalan fina-finai da mai
rubutu zai duba don kara fahimtar wannan rukuni irin su Missing da Total Recall
da Fargo da Taken da dai sauransu. Tsuntsun Da Ya Ja Ruwa shine rukuni da gaba
da ya yi bayani a kai. Ya bayyana wannan rukuni da cewa ‘Labaran dake wannan
rukunin labarai ne na alhaki kwikwuyo. Wato tauraron ne ke yin wani babban
kuskure da ke bibiyarsa a rayuwa. Shi ke tsokano fitina, fitinar ta dawo ta
addabe shi, har idan ya shiga wani hali a rinka tausaya masa ana ganin kamar
cin zalinsa ake yi.’(Sh. 108). Wannan rukuni ma ya farfasa shi zuwa kananan
azuzuwa kamar su Gidan Rina da Tauraruwa mai Wutsiya da Daurin Boye da
sauransu. Ya kuma bada misalan fina-finai kamar su Psycho da The Shining da
Anaconda da Saw da sauransu. Rukuni na gaba shi ne Gwarzon Sadauki (Legends and
Super heroes) wanda marubucin ya ce ‘Labarin Gwarzon Sadauki ya dade yana
tasiri a duniya. Mutane suna ganinsa ne wani abu dabam kamar ba tsurar mutum
ba. Ana kallonsa a matsayin maceci, wato wanda zai zo ya cece mu akwai irin
wannan tunanin a kowace al'umma a duniya.’ (Sh. 115). Ya farfasa wannan rukuni
zuwa Sadaukin Zahiri da Sadaukin Littafi da Sadaukin Almara da Sadaukin Jama’a.
Ya bada misalan fina-finai kamar su Malcom X da The Jungle Book da The Matrix
da X-Men da sauransu.
A rukuni na gaba ya tattauna akan
gaye Cikin Matsala wanda ya bayyana da cewa Labarin Gaye Cikin Matsala labari
ne na mutumin da bai ji ba, bai gani ba wasu suka jefa shi cikin tashin
hankali’ Ya ce. ‘A fim din Sai A Lahira Ali Nuhu ya fito yiwa matarsa sayayya
da dare, wasu mutane da bai sansu ba suka zo a mota suka ama shi da karfin
tsiya suka tafi da shi, wanda daga baya aka gano musanya shi aka yi da wani dan
mai kudi a gidan yari.’ (Sh.123) Ya farfasa wannan sashi zuwa azuzuwa kamar su Matsalar
Leqen Asiri da Matsalar Jami’an Tsaro da Matsalar Azal da sauransu. Ya bada
misalan fina-finai kamar su The Net da Speed da Hostage da Volcano da Apollo 13
da sauransu. A rukuni na takwas wanda ya kira Matakan Yaye (Rites of passage)
wanda ya bayyana a cewa ‘labarai ne dake kunshe da matakan rayuwa tun daga
haihuwa, kuruciya ya zuwa girma da mutuwa.’ (sh. 131). Ya farfasa wannan rukuni
zuwa azuzuwa kamar su Tashen Balaga da Jarabtuwa da Rabuwa da Mutuwa da
sauransu. Ya kuma bada misalan fina-finai kamar su Sixteen Candles da Permanent
Midnight da Lost in Translation da Byebye Love da The Sweet Hereafter da
sauransu. Rukuni na kusa da na karshe wanda ya kira Tsafi Gaskiyar Mai shi
wanda ya ce Labaran siddabaru na daga cikin labarai mafi karbuwa a wajen mutane
a duniya. Wannan ba zai rasa nasaba da kasancewarsu kama da mafarki ba.’ (Sh.
140). Ya farfasa wannan rubutu zuwa azuzuwa kamar su Almarar Musanye Jiki da
Almarar Rauhani da Almarar Budurwar Zuciya da Almarar Rainin Wayo da sauransu.
Ya bada misalai kamar su Like Father Like Son da Alladin da Jumanji da Field of
Dreams da sauransu. A karshe ya rufe da rukuni na karshe wanda ya kira
Rantsarwa. Ya ce ‘Labaran wannan rukuni, labarai ne da jarumin ke yunkurin fita
daga kungiyar ko hukumar, wanda hakan ke haddasa masa zazzafar matsala.’ (sh.
150). Ya farfarsa wannan rukuni zuwa azuzuwa kamar su Hukuma mai Damara da
Dangi da Jagora ko Uban Gida da sauransu/ Ya kuma bada misalan fina-finai kamar
su Platoon da The Godfather da Of ice Space da The Departed da sauransu. Ka’idojin
da Yadda Ake Fara Rubutun Fim Marubucin ya rufe littafin da bada xan
taqaitaccen bayani akan tsarin rubutun da ake amfani da shi wurin rubuta
sikirif da ma yadda ake fara rubuta sikirif. Ya yi bayani akan yadda ake fara
rubuta sikirif da tsarin da ake bu wanda kwararru suke amfani da shi, ya kawo
takaitaccen bayani akan matakai biyarkamar haka:
1. Fitowa
2. Motsi ko aikatau
3. Sunan Tauraro ko Tauraruwa
4. Lafazi
5. Motsin Rai Cikin Baka
Na tabbata dai wannan somin tavi ne
ya yi a masu son rubuta sikirif. Muna fatan nan
gaba zai fitarmana da littafi akan
wannan fanni.
WURAREN DA YA KAMATA A INGANTA
Kowane littafin, in dai ba Al-kur’ani
ba, to ba ya cika. Saboda haka, shi ma wannan
littafi, yana buqatar a qara inganta
shi in an zo sake bugawa. Zan kawo wurare bakwai a taqaice da ya kamata a duba.
1. Bangon littafi: bangon littafin
bai tsaru ba, ya yi duhu kuma ba zai ja hankali ba. Ya kamata a bayan littafin
a dan bada tsakure akan abinda littafin ya kunsa wanda zai taimakwa mai son
karanta littafin ya samu xan tava ka lashe.
2. Rashin yin amfani da harafin
Hausa masu lankwasa ya rage darajar littafin.
3. Akwai wurare da ba a bi ka’idojin
rubutu ba, misali a wasu wurare an hade
kalmomi maimakon raba su, misali a
shafi na 13 inda aka yi amfani da kalmar bashi
maimakon ba shi ko kuma a shafi na
12 sakin layi na 2-3 inda aka fara rubutu bayan
aya da karamin baki.
4. An rubuta wasu kalmomi ba daidai
ba, misali a shafi na 145 an rubuta kalmar
Rauhani da Raihani.
5. A shafi na 52 inda ya kawo
rukunan labarai ga masu kallo guda goma, sai dai tara
ya bayar amma babu lamba 6.
6. Ya kamata a ce a karshen littafin
ya samar da fihirisa watau glossory don taimakawa mai karatu fahimtar fassarar
da ya yi, wanna kuma zai iya zama babbar gudunmuwa ga harshen Hausa wajen samar
da fassara a harkar fim.
7. Ya kamata a inganta shafi na ii
inda ake bada bayani akan wallafar littafi, bai yi
kama da gwani ne ya buga littafin
ba. Ko ISBN babu.
KAMMALAWA
Marubucin ya yi amfani da salo mai
jan hankali wanda ba zai wahalar da mai karatu ba saboda ya ka sa littatfin
zuwa gajerun babuka miamakon masu tsawo ta yadda koda mai karatu ba mai son
yawan karatu ba ne zai iya bin littafin a hankali a ahankali ba tare da an
gundurar da shi ba. Wanann littafi ya nuna abin nan da Hausawa ke cewa masu abu
da abunsu. Bala Anas ya nuna mana cewa shi malamin fim ne, ba xan fim ba. Ya
kalli fina-finai da yawa kallo na nazari ba kallo na nisahxi kawai ba. Ya koya
mana yadda mai son harkar fim zai maida fina-finai darasu gare shi. Samar da
wannan littafi da harshen Hausa wata babbar hovvasa ce wadda za ta sauya harkar
fina-finai a Kannywood. Wannan littafi, in an karanta shi a tsanaki zai inganta
rubuta labari don fim ya kuma tabbatar da ingancin abinda ake haskawa muke
kallo in an samu hadin kan masu sana’ar. Dole ne mu yaba wa Malam Bala Anas
Babinlata bisa wannan hangen nesa da ya yi na rubuta wannan littafi da kuma
buga shi. Ya nuna cewa shi marubuci ne na asali, kuma marubuta na murna da shi.
Koda ya koma harkar fim, bai manta mafarinsa ba. Muna fatan za a sayi wannan
littafi a kuma karanta shi, sannan ayi amfani da shi. Alhamdulillah.
Note
Ban samu na sake yin bitar wannan
sharhi ba bayan na kammala shi, in an ga kurakurai a yi mun afuwa. Zan kara
inganta sharhin nan gaba.
Muna godiya, Allah Ya saka da alheri.
ReplyDelete