GUDUMMAWAR MARUBUTA A SHIRIN FIM
A Takaice
Ado Ahmad Gidan Dabino MON
Gabatarwa
Ta hanyar rubutu ne marubuta suke fitar da abubuwan da suke cikin zuciyoyinsu, wadanda suka faru da kuma wadanda suke hasashen za su faru nan gaba, don jama’a masu karatu ko sauraro ta hanyar rediyo su ji ko masu kallo kuma su karu da abubuwan da ke cikin rubutun wanda ya shafi ilmantarwa ko tarbiyyantarwa ko nishadantarwa ko kuma akasin haka.
Rubutu rayayyen al'amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wadda in har an yi ta za a girbi abin da aka shuka.
Wane ne Marubuci?
MARUBUCI DAN BAIWA NE, haihuwarsa ake yi ba yin sa ake ba. Marubuci shi ne wanda ta hanyar amfani da fasahar rubutu yakan kirkiri wani yanayi na gaske ko na almara ko tunani ya kuma yi amfani da shi don gina wasu mutane da abubuwa wadanda yake amfani da su don isar da sako ga al'ummar da ke karatun rubutunsa. Shi wannan sako ana tsara shi ne ta hanya ta musamman mai cike da hikima da hazaka don isarwa a saukake, kamar ta hanyar yin amfani da haruffa zuwa kalmomi zuwa jimloli zuwa sidarori da shafuka har zuwa cikakken littafi.
Wani ana haihuwarsa da rubutu wani kuma koyo yake yi, amma duk marubuta za mu kira su. Shi marubuci mutum ne na daban, ba wai ya fi sauran rukunonin bil'adama ba ne, a a, shi dai daban yake da sauran mutane, wato dan baiwa ne. Marubuci na yin tunani ne iri na daban, yana kuma kallon rayuwa da al'amuran rayuwa da wata irin fahimta tasa ta daban, sannan ya bayyana ta a rubuce. Kamar yadda aka ambata a sama shi marubuci dan baiwa ne, sannan shi kansa rubutun baiwa ne.
Mece ce Gudummawa?
Muwa wata mata ce mai tabin hankali wadda take tafiya gudu-gudu sauri-sauri, idan ta zo ta tarar da mutane sai ta ba su kyautar abin da ta zo da shi amma fa tare da ita za a cenye abin, wato za ta zauna a ci abin tare da ita, idan ta ga ya kare sai ta tashi ta tafi, wannan ita ce al’adarta kuma kowane lokaci haka take yi wa mutane, daga nan shi ne idan mutum yana so ka ba shi taimako wanda yake sa ran nan gaba shi ma ya saka maka ko kuma nan gaba kai ma ka amfana daga abin, ko kuma Allah ya saka maka, sai ya ce wane me zai sa ba za ka yi min irin gudun da Muwa take ba, daga nan ne mutane suka juya kalmar ta koma gudummawa kai tsaye. A dunkule kalmar gudummawa tana nufin taimakawa da wani abu wanda kake sa ran samun sakamako a nan duniya ko kuma lahira, wata kuma gudummawar ba a samun sakamako sai dai a lahira.
Mene ne Fim?
Fim tantagaryar kimiyya da fasaha ce, kuma rayuwar dan’adam ce ake nunawa. Fim yana dauke da tarihi da dabi’un jama’a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu. Fim yare ne da kowane mutum yake iya fahimtarsa a duniya, musamman bisa harshensa da tsarinsa na rayuwa da hanyoyin tunaninsa da suka hada da gani da ji da motsi.
Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa da ilmantarwa da jan hankali da nishadantarwa da fadakarwa da yada manufa da tallatawa. A dunkule kafa ce daga cikin kafafen yada labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci.
Wace Irin Gudummawa Marubuta Suka Bayar a Harkar Fim?
Kacokan zan mayar da maganar ne a kanmu wato masu shirya finafinan Hausa na asana’antar Kannywood, ba na son in shiga wata uwa duniya gwara in tsaya iya inda muke muka fi fahimta, muka fi sani muka fi wayo domin mu fi saurin kamo bakin zaren. Kuma za mu yi a takaice saboda nan ba fage ne na Jami’a ba, wajen taron ga-ni ga-ka wanda za a baje koli ido da ido ba a yi bayanai da baki da baki ba.
Kafuwar Kannywood
An kafa wannan masana’anta ne tare da marubuta, marubutan kuma na littattafai ko in ce labarai. Wasu daga cikin mu za su iya tuna lokacin, a wajejen shekarar 1994 zuwa 1995 aka yi yinkurin kafa Kungiyar Masu shirya Finafinai ta Jihar Kano, wato Kano State Film Makers Association. Mutanen suna da yawa amma wasu daga ciki da zan iya tunawa a wannan kokari su ne:
1. Ibrahim M. Mandawari
2. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
3. Aminu Hassan Yakasai (Marigayi)
4. Auwalu Muhammad Sabo
5. Auwalu Mashal
6. Dan’azumi Baba Chediyar ‘Yan Gurasa
7. Bala Anas Babinlata
8. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
9. Balarabe Sango II
In muka dubi wannan jerin sunaye, za mu ga sama da rabin mutanen marubuta ne, kuma duk suna da littattafai ko labarai da suka rubuta a lokacin da suka yi wannan gangami na kafa kungiyar masu shirya fim ta farko.
Yi wa fim Jaket: Wanda ya fara yin sa shi ne Bala Anas Babinlata a shekarar 1995. Kafin ya gabatar da wannan tunani, ba a sanya wa fim jaket sai da ya kawo wannan abu ne aka amsa ga shi har yanzu ana yi wa fim jaket.
Samar da sunan Kannywood a shekarar 2002, Sunusi Shehu Daneji shi ne ya samar da wannan suna kuma marubuci ne na.
Marubuta da Suka Fara Kafa Kamfanonin Shirya Finafinai Kuma Suka Zuba Jari
Ga wasu daga cikin marubuta da suka bayar da gudummawa wajen kafa kamfanonin shirya finafinai a wannan masana’anta ta Kannywood, sannan kuma suna rubutawa suna shiryawa suna bayar da umarni.
1. Ibrahim Mandawari
2. Aminu Hassan Yakasai (marigayi)
3. Bala Anas Babinlata
4. Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan gurasa
5. Ado Ahmad Gidan Dabino
6. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
7. Abubakar Ishak Zariya
8. Abdullahi Yahaya Mai Zare
9. Bashir Sanda Gusau
10. Balaraba Ramat Yakubu
11. Bala Muhammad Makosa
12. Nura Abdullahi Azara
13. Ibrahim Muhammad Kofar Nasarawa
14. Abba Bature
15. Nazir Adam Saleh
Wasu daga cikin Marubuta Jarumai a Farkon Kafuwar Kannywood
1. Ibrahim Mandawari
2. Aminu Hassan Yakasai (marigayi)
3. Bala Anas Babinlata
4. Dan Azumi Baba Chediyar ‘Yan gurasa
5. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
6. Adamu Muhammad Kwabon Masoyi
7. Abubakar Ishak Zariya
8. Nura Abdullahi Azara
9. Hamisu Bature
Mujallun da Suke Bayar da Labarin ’Yan Fim da Marubuta Littattafai
Kamfanin Gidan Dabino Publishers, Kano, su ne suka fara buga mujalla ta farko a jihar Kano mai suna Zamani, wadda take bayar da labaru a kan masu yin wasan kwaikwayo da kuma marubuta, a cikin watan Yuli na shekarar 1994 aka fara buga ta. Wannan mujalla tunanin wasu fitattun marubuta ne masu sha’awar ci gaban harshen Hausa, mutanen da suka gudanar da ita su ne Aliyu Abubakar Aliyu da Bala Anas Babinlata da Dan’azumi Baba Chedyar ’Yangurasa da Balarabe Abdullahi Sani da Farfesa Yusuf Muhammad Adamu da Sunusi Shehu Daneji da marigayi Aminu Hassan Yakasai (Allah ya jikansa) da Bashir Sanda Gusau da kuma Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.
Mujallar Tauraruwa ita ce mujalla ta biyu da aka samar a wannan masana’anta, ta fito ne a watan Janairun shekarar 1999, Sunusi Shehu Daneji ne ya kafa ta.
Sai mujallar Fim da ta fito a watan Maris, 1999, wadda Ibrahim Shehe ya kafa.
Ado Ahmad Gidan Dabino, MON- ya kafa mujallat Mumtaz a cikin shekarar 2000.
Wasu Daga Cikin Sahun Farko na Marubutan da Aka Juya littattafansu Zuwa Fim a Kannywood
1. Ado Ahmad Gidan Dabino- In Da So Da Kauna
2. Dan’azimi Babba Chediyar ‘Yan Gurasa- Bakandamiyar Rikicin Duniya
3. Aminu Hassan Yakasai-Madubi
4. Ibrahim Mandawari- Aminu Mijin Bose
5. Khalid Musa- Kadaura (Hannun Da Ya Ba Da Kyautar
6. Bala Anas Babinlata- Tsuntsu Mai Wayo
7. Bala Muhammad Makosa -Halimatu ko Jummai
8. Adamu Muhammad -Kwabon Masoyi
9. Yusuf Aliyu Lawan Gwazaye- Cinnaka
10. Sunusi Shehu Daneji- Bankwana da masoyi
11. Abba Bature - Auren Jari
12. Abdul’aziz Sani Madakin Gini- Idaniyar Ruwa
13. Aminuddin L. Abubakar (Ala)- Bakar Aniya
14. Abubakar Ishak - Da Da Kyar Na Sha
15. Kabiru Ibrahim Yakasai – Suda
16. Auwalu Y. Hamza- Gidan Haya
17. Aminu Aliyu Argungu- Haukar Mutum
18. Bashir Sanda Gusau - Babu Maraya Sai Rago
19. Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa - Ki Yarda Da Ni
20. Balaraba Ramat- Alhaki Kwikwiyo
21. Ibrahim Birniwa- Maimunatu
22. Maje Elhajij- Sirrinsu
23. Ibrahim M. K/Nassarawa Soyayya Cikon Rayuwa
24. Muhammad .B. Zakari - Komai Nisan Dare
25. Nazir Adam Saleh -Naira Da Kwabo
26. Zuwaira Isa - Mowar Mata
27. Zilkifilu Mohammed - Su Ma ‘Ya’ya Ne (marigayi)
28. Halima A.D. Aliyu - Muguwar Kishiya
29. Rabi’u Abdullahi Sharfadi-Halak
30. Dalhatu Ibrahim Basawa-Cizon Yatsa
31. Kamilu Tahir-Rabi’a
32. Habibu Hudu Darazau – Zafin Nema
33. Lubabatu Ya’u -Yaya Kenan (Kasko)
34. Ibrahim Mu’azzam Indabawa - Boyayyiyar Gaskiya (Ja’iba)
35. Sadiya Garba Yakasai- Wake Daya (Yana)
36. Fauziyya D. Sulaiman- Rumaisa
37. Nasir Umar Ciromawa-Mata Da Kudi
38. Kabir Yusuf Fagge Anka-Kushewar Badi - Hakkin Miji
Gudmmawara da marubuta suka bayar ba ta tsaya nan ba kawai, ta gangaro har ga kafa wasu sababbin kamfanoni sanadiyyar zaman da wasu mutanen suka yi a karkashen wadannan marubuta. Sannan ta haka ne wasu ma suka zama marubuta a wannan masana’anta, wasu suka zama masu shiryawa da bayar da umarni, wasu kuma suka zama jarumai, wato sun raini wasu sun koyawa wasu su ma sun iya.
A shekarar 2003, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON da Bashir Mudi Yakasai sun gabatar da takarda mai taken: Matsaloli da Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa Musamman na Kano, an buga takardar a cikin littafin Hausa Home Videos: Technology, Economy and Society wanda Farfesa Abdalla Uba Adamu da Yusuf Adamu da Umar Faruk Jibrin suka zama editocinsa. Ana iya dubawa don samun Karin bayani da kuma ganin yadda marubuta suka bayar da gagarumar gudummawa wajen samuwar ci gaba da bunkasa da kafuwar wasu kamfanoni a wannan masana’anta ta Kannywood.
Kuma marubutan nan har yanzu wasu daga ciki suna wannan masana’antar ba su gudu ba, ko da sun gudu ma suna dawowa
Ina ga idan aka ce kashi 50 cikin dari na ci gaba da bunkasar da kuma kafuwar wannan masana’anta marubuta ne suka kawo su, ina ga ba a yi kuskure ba. Allah ne masani. Na gode.
MANAZARTA
Gidan Dabino, A.A, (1995) Muhimmancin Marubuta a Cikin Al’umma,
Takardar da Aka Gabatar a Bikin Kaddamar da Littafin Karshen Mai Zalunci. Koko, Jihar Kebbi: Makarantar Sakandare.
Gidan Dabino, A.A, (1993) Gudummawar Adabin Hausa da Addinin Musulunci, Takardar da Aka Gabatar a Taron Kara wa Juna Sani na Dalibai Musulmi na Babbar Makarantar Sakandaren Dawakin Tofa.
Gidan Dabino, A.A, (1992) Tasirin Labaran Soyayya ga Al’umma, Musamman ta Hausawa, An Gabatar da Wannan Takarda a Taron Kara wa Juna Ilimi Mai Taken “Rubutu Don Al’umma’’ Wanda Kungiyar “Writers Forum” ta Gudanar, a Majalisar Matasa ta Fagge, Kano.
Buba, Malami, Gidan Dabino, A.A, (2004) Adabi Mai Tafiya: Waiwaye A Kan Fasahar Mai Da Littafi Zuwa Fim. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Yakasai, B.M., Gidan Dabino, A.A, (2004) Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa Musamman Na Kano. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Hira da Marubuci Bala Anas Babinlata, 07/06/2020, karfe 7:49 na safe
Hira da Marubuci Almustapha Adam Muhammad, 07/06/2020, karfe 9:35 na safe
No comments:
Post a Comment