Friday, July 10, 2020

A DALILIN SON KAI - 2 NA IBRAHIM BIRNIWA



A DALILIN SON KAI - 2 NA IBRAHIM BIRNIWA

Zahra’u da Maryam sun keve a cikin xakin Maryam qarfe huxu da rabi ne na yamma a loakcin.Maryam ta xauko album wanda ya kasance cike da hotunan Faruq ta baiwa Zahra’u domin taga gwarzon nata. Zahra’u ta karvi kundin hotunan tariqa buxewa tana kallon kala-kala hotunan Faruq. Kyakkyawan saurayi, ma’abocin iya saka sutura, gaye wayayye ko a hoton. Ta riqa bin hotunan tana kallon su cikin yabawa yayin da suke ‘yar hira ita da Maryam, duk yawancin hirar akan Faruq. A lokacin da ta gama kallon hoton Zahra’u ta tabbatar ya kwanta mata a rai. Ta rufe album xin.

“Mutumin ina ne?” Ta tambayi Maryam.

“Kano.” Maryam ta ce da ita.

“Gaskiya ya haxu, babu shakka kin yi zave. A ina ku ka haxu da shi?”

“A garin nan.” Maryam ta ce, “Ya zo xaurin auren wnai abokinsa, ni kuma ina daga cikin qawayen amarya,sai mukahaxu wajen hada-hadar bikin, ya ji na kwanta masa a rai tun a lokacin da ya fara gani na, saboda hakabai bar garin nan sai da ya bayyanar da soyayyar sa a gare ni, ni kumana amince da shi. Wannan shi ne watan mu kusan na huxu da shi. Mun haxu da shi a watan da muka gama karatu.”

“Gaskiya ya  yi wallahi. Mene ne sana’ar shi?” Zahra’u ta tambaya.

“Fitar da kaya waje, da kuma shigo da na waje ciki.”

Import and export kenan.”

“Sana’ar sa kenan.”

“Ki ce mai kuxi ne gaskiya.”

“Sosai ma kuwa.” Maryam ta ce “In ki ka ga motocin da yake hawa. Xari biyu da hamsin fa ya bani dan shirya wannan bikin.”

“Dubu xari biyu da hamsin?” Zahra’u ta tambaya baki buxe.

“E, wallahi!” Maryam ta tabbatar mata.

Zahra’u ta jijjiga kai, “Lallai ki ce jarumin naki mai gani ne, Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi.”

“Ameen.” Maryam ta ce “Na gode da ki kayaba min shi.”

“Na gode da ki ka nuna min shi nima.” Zahra’u ta ce a ranta.

Sun gabatar da duk wani abu da ya kamata su gabatar da dangane da shirye-shirye a ranar koma Maryam ta yi suna tare da Zahra’u tare suka shirya komai. Zahra’u ta fahimci mahaifiyar Maryam, Hanne tana qaunarta kamar yadda mahaifiyarta Umma Hauwa take qaunar Maryam.

Abin da suka yi na qarshe a ranar kafin su dawo gida da magariba shi ne maganar kujeru waxanda za a zazzauna wajen party baiko sun biya kuxi gaba xaya ba rabin kuxi ba. A gajiye suka shigo gidan liqis.

“Sannunku da dawowa.” Hanne ta ce da su.

“Yauwa sannu Umma. Sunka amsa a tare, sannan suke sassamu wuri suka zazzauna a nan tsakar gidan.

“Wash, gaskiya na wujijjiga.” Zahra’u ta ce, “Wai tun ma kafin a zo mai gaba xaya.”

“Ka ji wai ta wujijjiga.” Maryam ta ce, “Sai ka ce ita kaxai ta yi yawon ba da ni ba.”

“To lallai ne ke ki ji yadda na ji.” Zahra’u ta ce “Kin ji ki,ke da kina ta zumuxi ko gajiya ma ba kya ji.”

Hanne da ke can gindin murhu ta yi dariya “Ni ko har da zance ku zo kukarvi girki tun da kun dawo, ni kuma in huta, amma duk kun cika gida da qorafe-qorafe.”

Suka yi dariya.

“Umma ki ka bamu girki ai kuwa a ci jaga-jaga.” Maryam ta ce.

“Ai har gara ma jaga-jaga.” Zahra’u ta ce, sannan ta miqe “Bari dai ki ga na yi wanka ko na dawo garau.” Ta nufi xakin Maryam domin shirin wanka.

“Yi ki fito nima na yi.” Maryam ta ce yayin da ta bi ta a baya zuwa cikin xakin.

Qarfe takwas da rabi na dare.

Zahra’u da Maryam suna kwance akan qatuwar katifar Maryam suna hira, suna jiran barci ya zo ya kwashe su.Ba su fi minti talatin ba da kammala, cin abincin dare suka kwanta saboda a gajiye suke, sakamakon zirga-zirgar da suka yi.

“Zahra’u ina labarin Sani Magaji ne?” Maryam ta tambaya.

“Ke rabu da wannan.” Zahra’u ta ce, “Bai zo ba, wallahi kwata-kwata bai haxu ba.”

“Kai Zahra’u, ke dai kin fiye ruwanido. Ke kenan kullum ki yi ta xauka kina ajiye wa. Ya kamata ki nutsu fa tun kafin kasuwa ta watse.”

“Wa ya gaya miki wancan kasuwar za ta watse?” Zahra’u ta ce, “Ai wannan kasuwar ko yaushe kasa mata kaya ake.”

“Haka ki ke gani?”

“Ya haka na ke gani, haka ne.”

“To shi kenan.” Maryam ta ce, “Yanzu waye gwanin?”

“Ba ni da wani gwani ni.”

“Ke Zahra’u?”

“Wallahi da gaske, duk masu zuwa wuri na, ni ba su yi min ba.” Zahra’u ta ce.

“Ruwan idon ki dai, amma Sanin nan mene ne laifin sa?” Maryam ta ce.

Zahra’u ta xan juya can ta baiwa Maryam baya, “Ina za ki gane laifinsa ke da ba sanin haxuwar maza ki ka yi ba.”

“Ban san haxuwar maza ba kuma na zavo Faruq?” Maryam ta ce.

“Ya zavo ki dai, ba shi ya ganki ya ce yana so ba?” Zahra’u ta ce.

“To dama ni zan je na ce ina son sa ne. Amma kuma da na amince fa?

To ai dolenki neki amince.Wace ce za ta kasa amsa tayin wannan. Gaye ya kai gaye, amma da yake ke mai son kai ce, kina da kamar Faruq, ni kuma ki ke so ki nuna min cewa ba laifi ba ne idan na amincewa Sani, mutumin da ko sutura bai iya sawa ta yi masa kyau ba. Abokin nan nasa Ibrahim ne ma fa yake xan koya masa gayu. Da ma dai Ibrahim xin ne yake so na, to da sai na amince.”

Maryam ta xan yi dariya.

“To ki sace zuciyar Ibrahim xin mana.”

“Tab, wannan ba shi da wata magana kullum sai ta wata wai ita Shafa’atu ‘yar Gusau.”

“Kin tava zuwa Gusau?” Maryam ta tambaya.

“Kai ban tava zuwa ba.”

“Ba ki ma san wajen ina take ba ko?”

“Na sani mana, ba can take ba wajen Baushi?”

“A’a, me ya haxa Gusau kuma da Baushi?” Daga jihar Sokkwato fa aka cire ta.”

“Haba?”

“Allah.”

Haka suka yi ta hira har barci ya xauke Maryam. Zahra’u ba ta sani ba tana ta magana sai ta ankara Maryam ba ta amsawa.

“Maryam!” Ta kira sunanta.

Shiru, ta tabbatar Maryam ta yi barci, sai ta yi shiru itama, ta lumshe idanuwanta ta faxa kogin tunani. Tunanin faruq, mutumin da ba ta tava ganin sa a zahiri ba sai a hoto. Zuciyarta ta karkata gaba xay zuwa gare shi. Ta matsu Talata ta yi domin ya zo ta ganshi a zahiri. Kwanaki ukun da suka rage Talata ta zo sai take ganin su kamar wasu sati uku. Abin da yake tava ranta shi ne sanin cewa babu yadda za ayi ta ganshi dole sai ranar Talatar nan idan ya zo.

Ta tashi zaune a hankali, sannan ta miqa hannu kan wani xan tebur da ke gefen katifar, da suke kwance ta xauko album xin da ke xauke da hotunan Faruqu. Ta buxe album xin ta  riqa kallon hotunan xaya bayan xaya. A lokacin data gama kallon hotunan sai ta album xin ta rungume a qirjinta, tana mai ina ma ina ma, ina ma da ita suka haxu ba da Maryam ba, ina ma ita yake so ba Maryam ba, ina ma baikonta za a yi gata ba na Maryam ba.

Ta xan juya ta dubi Maryam dake kwance tana barci abin ta.

Barcin  ta ma take saboda babu abin da ya dameta ta mallaki saurayi da ya kwanta min a rai. Ta xan jima tana dubanta. Sannan sai ta xaukie kai ga barin kallonta, sannan ta juya ta maida album xin ta ajiye a wurin da ta xauka.

Ta miqa hannu ta kamo makunnar lantarki ta gado ta kashe wuta, duhu ya gauraye xakin, sannan ta rufe idanuwanta ta gayyato barci. Barcin bai zo ba sai bayan da ta shafe sama da minti goma sha biyar tana tunanin Faruq.

Can cikin dare a cikin barcin ta sai ta yi mafarki ana biki. Kuma tana xaya daga cikin qawayen amarya, sai abokan ango suka zo maganar kuxin zanchen, sai ta ga har da Faruq a cikin su. Ya kura mata idoyana ta kallon ta ita ma tana ta kallonsa. Can sai ya kira ta suka keve su biyu.

‘Ina son ki.’ Ya ce da ita.

‘Ina son ka nima.’ Ta amsa masa.

Sai ta ga ya qyalqyale da dariya. Yana ta dariya sai ta ga ya juye ya koma Sani. Ashe dama ba Faruq ba ne Sani ne. Sani ya juya baya yana ta dariyar jin daxin ta ce tana sonsa.

Sai taji ranta ya vaci ‘Bana son ka, ba na sonka...ba na sonka.’ Ta riqa faxa cikin tsawa.

Sani ya juyo. Yana juyowa sai ta ga Faruq ne, ya daina dariya ya vata rai.

‘Ba kya sona?’ ya ce da ita ‘Shi kenan na gode.’ Ya juya, ya tafi, ya bar ta.

A xan lokacin sai ta ruxe ta rasa yadda za ta yi, sai kuma ta daidaita qwaqwalwarta.

‘Ina sonka....ina son ka....’ ta faxa da qarfi. Ta tabbatar ya ji, amma kuma bai tsaya ba ya ci gaba da tafiyar sa, sai ta bi shi da gudu tana ta faxin ‘Ina son ka....’ina son ka...’ tana gudun sai ta yi tuntube ta faxi. Ta yunkura za ta tashi, sai ta farka daga barcin da take.

Da farko ta xan yi jim anan a kwance, tana qoqarin rarrabewa tsakanin mafarkin da kuma gaske. Ta ja dogon numfashi  bayan da ta fita a mafarki, shiru babu wuta an xauke. Ta ji haushi saboda tana son ta sake kallon hoton Faruq. Duk da haka sai ta juya ta sa hannu amma sai ta bubbuxe album xin, ba ta ganin komai xin kuwa sai duhu, ta rufe album xin  ta rungume shi a qirjinta ta faxa tunanin Faruq.

Rungume da hoton a qirjinta, barci ya sake xauketa.

Qarfe takwas na safe maryam ta farka daga barci, da yake xakin a kulle yake har yanzu hasken qwan lantarki yana da tasiri a xakin. Zahara’u ba ta kashe wuta ba kenan, maryam ta zata. Ta tashi, ta zauna nan akan katifar yayin da ta yaye mayafin da take lulluve dashi. A hankali ta juya, ta dubi Zahara’u dake kwance a gefenta tana barci, ga mafarkinta sai ta ga Zahara’u tana rungume da album xin dake xauke da hotunan Faruq. Ta xan jima tana kallon Zahara’u, a cikin zuciyarta tana jujjuya abin da ta gani, tan son ta fahimci al’amarin irin fahimtar da ya dace mene ne hakan ke nufi? Me ya kai Zahara’u rumgume hotunan Faruq har tayi barci da su a qirjin ta.

Maryam tayi tunanin abubuwa da dama amma ta kasa tsaida tunanin ta a kan wani abu guda xaya. Abin da zuciyarta ke qoqarin saqa mata ba za ta amince da shi ba, ba za ta yarda yadda suke da Zahara’u wani abu makamancin abin da zuciyarta take karkata gare shi zai kasance ba.

Ta sa hannu a hankali ta zare album xin daga qirjin Zahara’u ta ajiye shi a wurin da ta saba ajiyewa, sannan sai ta xan doki kafaxar Zahara’u, ta sake  duka. Zahara’u ta farka a hankali, ta buxe idanuwanta kaxan tana xan yatsina fuska a qoqarinta na baiwa idanuwanta damar karvar hasken da ke gauraye da xakin.

Bayan idanuwanta sun tabbatar da sun amince da hasken sai ta buxe idanuwan natasosai ta dubi Maryam dake zaune a kan katifar a gefenta kana tayi miqa da hamma tare da yin salati.

“Tashi gari ya waye.” Maryam ta ce da ita.

Misalin karfe tara da rabi sun kammala da komai. Maryam ta shigo musu da kayan karin kumallo xaki, suka zauna suna ci suna kuma hirar abubuwan da suka shafe su da ma waxanda ba su shafe su ba kamar yadda qawaye suka saba yi. Can cikin hira bayan Maryam ta yi shawara da zuciyar ta sai ta amince ya kamata ta tuntuvi Zahara’u game da al’amarin da ya fara yi mata barka da asuba bayan ta shin ta daga barci yau.

“Zahara’u zan yi miki tambaya.” Maryam ta ce da Zahara’u.

“Ina sauraronki.” Zahara’u ta ce da ita.

Maryam ta kurvi shayi daga kofin da ke riqe a hannunta ta haxiye, sannan ta dubi Zahara’u.

“Wane matsayi ki ka baiwa Faruq nawa a wajenki?”

“Matsayi?”  Zahara’u ta ce “Wane matsayi kuwa ban da matsayin da ya dace da shi?” Zahara’u ta amsa mata.

“Kamar wane matsayi kenan ki ke zaton ya dace da shi?”Maryam ta tambaya.

“Saurayin qawata mana.” Zahara’u ta ce “Yana da wani matsayi da ya wuce ne? Me ya sa ki ka yi min wannan tambayar?” Ta xauki kofin shayi, ta nufi bakinta da shi.

“Na farka daga barci ne yau sai na gan ki rungume da album xin hotunan Faruq, shi ne nake son na san dalilin faruwar hakan.”

Zahara’u ta fasa kurvar shayin da ta kai bakinta, ta dawo da kofin qasa ta ajiye, zuciyarta na jujjuya abin da Maryam ta faxa cikin gaggawa tana son ta tuna abin da ya faru daren jiya da kuma amsar da ta fi dacewa ta baiwa Maryam.

Yanzu jiya barci ta yi album a qirjinta. Ya aka yi ta fara bada qofar da Maryam za ta fahimci wani abu tun yanzu. Ta dubi Maryam za ta fahimci wani abu tun yanzu. Ta dubi Maryam ta yi ‘yar dariyar qarfin hali.

‘Me ki ke so ki ce?’

‘Me na me ke so na ce, ko kuma me na ke so na ji?’ Maryam ta ce.

‘Kar fa ki yi wani tunani na shirme.’ Zahara’u ta ce.

‘Ba zan yi ba.’ Maryam ta ce ‘Shi ya sa ai na tambaye ki.’

‘Ok. Jiya na yi barci, can sai na yi wani mafarki mai ban tsoro, sai na farka nan da nan ke kuwa a lokacin kina barcin ki. Bayan wannan farkawar sai kuma barci ya qi wuza min. Na kwanta nan kawai idona buxe, cike da gundura. Na jima a haka barci bai zo ba, sai na kuma wuta na xan duba ko zan sami wani littafin karatu amma ban ga komai ba, shi ne sai na xauki album xin ina dubawa, ina gayyatar barci. Ban san lokacin da yayi awon gaba dani ba.

 “Ke da me ki ke zato?”

“Babu komai.” Maryam ta ce, sannan ta kurvi shayi ta ajiye kofi, “Kin san ina ji da shi, ina matuqar qaunar sa, ina kuma matuqar kishin sa.”

“Kina kuma matuqar zargi a kansa.” Zahra’u ta ce.

“Idan haka ne za ki ga laifi na?” Maryam ta tambaye ta, tana kallonta cikin ido.

“Ba zan ga laifin ki ba.” Zahra’u ta ce, “Ba zan ga laifin duk wata qawa da ta zargi qawarta da son saurayinta ba.”

“Za ki ga laifin ita qawar da aka zarga idan ta yi fushi?” Maryam ta tambaye ta.

“In dai tabbas an zarge ta xin.” Zahra’u ta ce. Sannan ta shi tsam daga gaban kayan karin kumallon ta koma bakin katifa ta zauna, sannan ta kwanta da baya akan katifar, yayin da qafafunta ke qasa. Ta yi qoqarin nuna fushi a fuskarta. Ya kamata ta nuna ranta ya vaci don hakan ya raunana zargin da Maryam take a ranta.

Maryam ta bi ta da kallo har ta kwanta xin, sannan ta ja dogon numfashi. Ba ta kyauta ba, ya za ta zargi qawarta qud da qud da son saurayin ta, bayan kuma ta faxi dalilin da ya sa ta same ta rungume da album xin hotunan saurayin nata.

“Ki yi haquri Zahra’u.” Maryam ta ce cikin sanyin rai, “Kin san yadda zuciya take kuma kin san yadda so ya ke. Bai kamata na zargi wani abu ba na sani amma na kasa hana kaina ne ki yi haquri don Allah, na gamsu da bayanin ki.” Ta yi shiru don jin abin da Zahra’u za ta ce, amma shiru ba ta ce komai ba.

“Zahara’u!” Ta kira sunanta.

“Don Allah ki qyale ni.” Zahra’u ta ce.

“Ki yi haquri don Allah don Annabi, I am sorry.”

 “Haba Maryam.” Zahra’u ta ce, “Ya ma za a yi ki yi min haka? Don kawai ke kina son Faruq sai ki xauka kowa ta ganshi za ta so shi, har ki fita a hankalinki ki zarge ni da sonsa, an ce miki Faruq ya yi min ne. Na fa yaba shi don kina sonsa, bai kamata na kushe miki shi ba...”

“Na dai ce ki yi haquri don Allah... Haba Zahra’u, ya wuce don Allah, Allah ya huci zuciyarki.”

Matsala.” Zahra’u ta ce a ranta, “Akwai babbar matsala.”


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...