ABUBUWAN DA SUKE CIKI
Gabatarwar Mawallafi 1
Qa’idojin Rubutun Hausa 4
Baqaqe da Wasulan Hausa 4
Qa’idojin Raba Kalmomi 11
Hukunce-hukuncen “Wa” 18
Wasu Kalmomi Masu Rikitarwa 19
Hukunce-hukuncen Wasalin “a” 23
Gutsirarren Aikatau Xaurarre 24
Kalmomin Sharaxi 25
Qarfafawa 26
Hausar Shiyya 26
QA’IDOJIN RUBUTUN HAUSA
Ma’anar Qa’idojin Rubutu
Qa’idojin rubutu, wasu dokoki ne da aka yi ittifaqin yin amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa. Ita kuwa daidaitacciyar Hausa, xaya daga cikin kare-karen harshen Hausa ce da aka zava, aka daidaita mata qa’idojin nahawu, don yin amfani da ita cikin rubuce-rubuce da harkokin yaxa labarai a dukkan qasashen Hausa da sauran duniya baki xaya.
Baqaqe da Wasulan Hausa
Jimillar baqaqen da ake amfani da su wajen rubuta daidaitacciyar Hausa, su Talatin da biyu (32) ne. Ashirin da huxu (24) daga cikinsu sauqaqa ne, Takwas (8) kuma masu goyo. Akwai kuma wasula goma sha biyu (12).
Sauqaqan Baqaqe
Manya:
B, V, C, D, X, F, G, H, J, K, Q, L, M, N, R (ta cikin biyar), R (ta cikin ruwa), S, SH, T, TS, W, Y, Z, ‘(alhamza).
Qanana:
b, v, c, d, x, f, g, h, j, k, q, l, m, n, r (ta cikin biyar), r (ta cikin ruwa), s, sh, t, ts, w, y, z, ‘ (alhamza).
Masu Goyo
Manya: FY, GW, GY, KW, KY, QW, QY, ‘Y,
Qanana: fy, gw, gy, kw, ky, qw, qy, ‘y
Wasula
Gajeru Manya: A, I, O, U, E,
Qanana: a, i, o, u, e
Dogaye Manya: AA,II, OO, UU, EE,
Qanana: aa, ii, oo, uu, ee
Masu aure: auren /a/ da /i/ = /ai/
auren /a/ da /u/ = /au/
Akwai kuma auren /u/ da /i/ kamar a kalmar a:
Ya yi targaxe a guiwa.
Ya kiwata xan kuikuyo.
mui gaba (mu yi gaba)
Kamar yadda muka sani, an samo wannan salon rubutu ne daga rubutun Rumawa wanda Turawa suka kawo mana. To daga cikin ainihin baqaqen abacadan Turanci akwai wasu baqaqe huxu da ba a amfani da su a Hausa, saboda ba mu da irin sautukansu. Baqaqen su ne: /p/, /q/, /v/ da /x/. Furucin kowannensu na da takwara a bakin Bahaushe da yake amfani da shi a madadinsa. Maimakon /p/ ana amfani da /f/ ne. /q/ a madadin /q/, /b/ a madadin /v/, sai /s/ a madadin /x/.
Duk da haka, akan rubuta /p/ a wasu sunayen yanka da ba ainihin na Hausa ba ne, kamar Pakistan, Potiskum, Pankshin, da makamantansu.
Babu sautin /ch/ a Hausa, sai dai /c/. Shi ma akan bar wasu sunaye, musamman na garuruwa waxanda Turawa suka rubuta imla’insu a hakan da /ch/. Kamar Bauchi, Bichi, Chiranchi, dm.
Ba a nuna dogon wasali ta hanyar ruvanya shi a rubutun Hausa na yau da kullum, kamar a ce /zoomoo/, sai dai /zomo/. Don haka kuskure ne rubuta wasu sunaye irin su Sameera, Haleema, Ameen, dm. haka ma qara baqin /h/ da wasu kan yi a wasu sunaye, musamman na mata kamar Aminah, Samirah, dm. Hasali ma ba imla’in rubutun Hausa ba ne, na Turanci ne.
Yayin ruvanya baqaqe masu goyo, ana ruvanya baqin farko ne kaxai, ba duka biyun ba. Misali:
Gwaggwaro ba gwagwgwaro ba
Kyakkyawa ba kyakykyawa ba
Fyaffyaxe ba fyafyfyaxe ba
Haka ma
Shasshaka ba shashshaka ba
Matsattsaku ba matsatstsaku ba
Madalla da wannan aiki, muna godiya matuƙa.
ReplyDeleteMuna godia Allah ya kara basira
ReplyDeleteMuna godiya
ReplyDeleteMasha Allah mun gode Allah ya saka da alkhairi ya kara karfafan ku
ReplyDeleteAllah yabawa mawallafin littafin nan Karin kwarewa wajen wallafa littattafan hausa
ReplyDeleteMasha muna godiya
ReplyDelete