GABATARWA
A kowanne zamani, a ko'ina a duniya za a ga koyaushe mutane suna da hanyoyin koyar da 'ya'yansu hankali, tsinkaya da basira, jurewa, hakuri, azanci da dabara da dai sauran halayen da za su taimake su lokacin da suka fara ma'amalar zaman duniya.
Daya daga cikin hanyoyin nan yakan kasance iya amfani da harshe wajen magana. Daga nan sai labarai na gaske da na almara, zaurance, karin magana, azancin tatsuniya, habaici, wa'azu, waka, cita-cita da sauransu.
Harshen Hausa ko kadan bai gaza wajen wadannan ba; haka kuma wajen labaran ban dariya, azanci, tausayi, wayo da dabara.
Ganin abubban nan sun fara bacewa a kasar nan, da kuma ganin rashinsu zai tauye mana wata daraja nan gaba balle ga ba da ilimi kyauta ga 'ya'yanmu ya zo, na duaki nauyin rubuta wadannan dan littafi da fatan taimakawa a wannan siffa. Kuma ina kara fata da addu'a cewa zai zama kafin alkalami ne ga sauran marubuta.
Mai karatu zai ga na debo abubba daga sassa; har da labarai na gaskiya bayan na almara saboda manufa dai ita ce kaifafa zukatun yara don kafin su girma su sami wukar gindi maganin aron ta wani. Allah ya yi mana muwafaka.
Daga karshe ina so in mika godiyata ga 'yan Komitin Inganta Hausa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano musamman ma Marafan Sakkwato Alhaji Ahmadu da Dr. Dandatti Abdulkadir, Dr. Kabir Galadanci, da Alhaji Abdulmalik Mani da Alhaji Usman Mairiga, da Alhaji Abdullahi Khalil, da M. Ibrahim Yaro Yahaya wadanda suka karfafa mini gwiwa a taron da muka yi a Sakkwato cikin watan Oktoba 1976 kan wallafar wannan littafi don tarbiyyar yaranmu da inganta hikimomin Hausa.
Aminu Kano.
Kano, 21st January, 1977
Na karanta wannan littafi kuma yayi min amfani. Allah Yajikan magabata. Engr. Umar Modibbo
ReplyDelete