Monday, July 20, 2020

NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM -Daga Rahma Abdulmajid





NASABA TSAKANIN LABARI DA LABARIN FIM

 

Rahma Abdulmajid

 

Bismillahirrahmanirraheem. Assalaatu Ala RasulilKareem.

 Kalmomin "Story By", "Screenplay By" "Written By" kalmomi ne da mai biye da jawabin godiya na kammala fim kan hadu da su, kuma su rikita shi, saboda tunanin kowa a karon farko akan fim shi ne; mai labari fa shi ne marubucin labari da tsara shi. Amma kuma ga shi a nan an karkasa aikin wa mutane da yawa, shin me hakan ke nufi? Haka ma da yawa marubuta ko masu dauke da labari a zuciya kan ji cewa ai da zaran ina da labari to fa ni marubuci ne har kuwa rubutun fim!

Muddin ba a samar da hanyar fallasa wannan tunani da wartsakar da shi ba, to zai yi wuya mutane su san abin da ke kunshe a wannan littafi da muke kaddamarwa na rubutun fim a yau, domin da zaran mutum yana da labari ji yake ya zama marubuci, in ko ya zama marubuci ai baya bukatar irin wannan littafin don koyon dabarun zama marubuci.

Don haka me ake nufi da Labari? Me ake nufi da rubutun fim? Sannan wace alaka ce tsakaninsu?

 

LABARI shi ne wani bayani da za a bai wa mai saurare ya saurara ko ya karanta, amma ba shi da damar ganin sa sai dai zuciyarsa ta sauwara masa labarin da jarumansa.

 

LABARIN FIM kuwa shi ne tsararren hoton labarin da aka hutasshe da zuciyar mai sauraro da kallo daga sauwara wa kansa ta hanyar nuna masa shi akan idonsa da taimakon allon kallo.

 

Koda yake za a iya ji ana amfani da kalmar labari da nufin rubutun fim, sai dai kalmar "Labari" ko "Story" a fannin rubutun film ta sha bambam da kalmar labari da mutane suka fi sani.

 

A cewar Patrick Cattrysse: Kalmar Labari a fannin fim tana nufin wasu sadarori hudu ko biyar da ke bayar da labarin jarumin da kalubalensa cike da amfani da hanyoyin da za su ja hankalin masu zuba jari a labari ba masu zallar sauraro ba, Nasarar wannan salon labarin shi ne ya karbu a wajen masu hannu da tsaki don ya zamo "Screenplay" har ya iso matakin hoto mai motsi.

 

Mahadar abubuwan biyu kuwa a bayyane take a salon ba ni gishiri-in ba-ka manda tsakanin labari da rubutun fim, domin a yayin da labarin ke zama jari ko uwar kudin "Screenplay", Shi kuma "Screenplay" shi ne ribar wannan uwar kudi wato labari.

 

Daraja daya Labari ke iya nuna wa "Screenplay" a wannan dangantaka shi ne: A kowane "Screenplay" akwai labari, amma ba a kowane labari ne akwai "Screenplay" ba ko kuma a wani salon mu ce gundarin labari ne ke haifar da tsararren labarin film.

 

Hakan na nufin duka abubuwan biyu na bukatar marubuci ne ya rubuta su, amma kuma abin mamakin shi ne hakan baya nufin kowane marubucin labari ne marubucin fim, sai dai a ce ya fi yi wa marubucin labari saukin zama marubucin fim fiye da farar hula a harkar.

 

Dalilai fiye da daya sun zamo sanadiyyar hakan cikinsu akwai:

1. Rubutun Fim, labari ne da ake shirya shi bisa ka'idoji tsaurara da ba su da jimirin bai wa marubuci uziri kamar wanda sauran labarai ke ba shi.

 

2. Labarin Fim tun daga samansa zuwa kasansa kasuwanci ne da ke bukatar kwarewa maimakon zallar kirkira da tunani don a mafi yawan lokuta yana dauke ne da jarin wanin marubuci ba marubucin kai tsaye ba.

 

3. Samar da Idea ba ta tattare da wata asara ko kuma uwar kudi, domin aikin kwanya mai tunani ne, ita kuma kwanya mai tunani tana kasancewa ne cikin aikinta na tunani yana so ko ba ya so, da riba ko hasara, amma inda gizo ke sakar, shi ne wannan Idea din na iya zame masa babban jari idan ya iya sarrafa shi ta hanyar rubuta labarin Fim.

 

Wani producer ya taba samun wani marubuci yana bayar da wani labari da na kirkira, ka da bakinsa sai ya ce "kana ta bayar da labari idan aka sace maka fa?" Marubucin ya yi dariya na amsa masa "Sai na kirkiro wani, wannan ne ya sanya ake kira na storyteller, saboda a duk inda nake ya kamata na iya samar da sinima ga abokan hirata ko da babu majigi. Amma idan na mai da shi Script to ya tashi daga Story ya zama jari har ya hau kan takarda, a nan ne ba zan bari kowa ya saci jari na ba"

Don haka Labari shi ne uwar kudi amma ba shi ne jari ba, iya mayar da labarin jari shi ne jari, shi kuma iya mai da labari jari ana yin sa ne bisa kwarewa da bin matakan ilminsa wanda su aka tattara a wannan littafin da muka taru don karramawa Da fatan duk wanda ke wurin nan zai yi kokari ya mallaki wannan dabara.

Assalamu alaikum


an karanta wannan rubutu a ranar da aka gabatar da littafin Rubutun Fim na Bala Anas Babinlata

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...