Monday, July 6, 2020

GASAR RUBUTATTUN GAJERUN LABARAN HAUSA TA ARCH. AHMAD MUSA DANGIWA




GASAR RUBUTU! GASAR RUBUTU!!
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

GASAR RUBUTATTUN GAJERUN LABARAN HAUSA TA
ARC. AHMAD MUSA DANGIWA
BISA MANUFOFIN BABBAN BANKIN BADA LAMUNI DON MALLAKAR GIDAJE NA ƘASA. (FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA)

Wannan gasa wata dama ce da za ta taimaka wajen bunkasa rubutaccen adabin Hausa da ya danganci gajerun labaran zube na Hausa, a karkashin jagorancin Arc. Ahmad Dangiwa, bisa manufofin babban bankin bayar da lamuni don gina gidaje na Kasa.

MAUDU'IN GASA
Maudu'in gasar zai kasance wani linzami da ake da yakinin cewa za ya ja akalar tunanin marubuta domin su fito da batutuwan;
• Tasirin da ke tattare da mallakar muhalli, da kuma wasu illoli da ka iya shafar rashin mallakar muhallin.
• Matsalolin da ake fuskanta na tsara muhalli ba bisa ka'ida ba, da suka hada da shata filaye ba bisa ƙa’ida ba, tare da gina muhalli a wuraren da ba su dace ba, kamar rashin gina magudanan ruwa, da illar da hakan ka iya haifarwa a cikin al’umma musamman ta fuskar kiwon lafiya da tsabtace muhalli.
• Fito da matsalolin da gine-gine marasa inganci ka iya haddasawa, da suka hada da asarori masu dimbin yawa, na dukiyoyi da rayuka da ma rasa muhallin kacokam!
Tilas masu gasa su yi anfani da salon ayyanawa na gajerun labaran zube na Hausa.

ABUBUWAN DA AKE SA RAN GASAR ZATA SAMAR BAYAN KAMMALA TA
• Samar da littafin zube Sukutum wanda ke ɗauke da labarai da suka danganci muhalli a cikin Harshen Hausa
• Fito da ayyukan bankin bayar da lamuni don samar da gidaje na ƙasa ƙarkashin jagorancin Arc. Ahmad Musa Ɗangiwa cikin sigar labaran zube.
• Fito da Fasihan matasa marubuta waɗanda ke da wata baiwa ta musamman da su kan iya tsayuwa akan ta domin dogaro da kai, musamman ta sigar yadda ake zana taswirar gida da tsara muhalli a cikin zube.
• Fito da girman matsalolin da ke akwai a ɓangaren muhalli tare da wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallaka da kuma kiyaye muhalli.
• Jawo hankalin ‘yan kasuwa da kamfanoni da su zuba jari a fannin samar da muhalli
• Jawo da hankalin gwamanti da hukumomi wajen sa ido game da yadda ake samar da muhalli tare da bin doka wajen shata filaye na tsarin garuruwa da unguwanni.

TASWIRAR GASA
An ba da dama ga marubutan Hausa, maza da mata, su aiko da samfurin labarin da za su rubuta mai ɗauke da kalmomi 1000. A tabbata an turo da samfurin kai tsaye ga dangiwaliterary2020@gmail.com zuwa ranar 04 ga watan Agusta, 2020. Za a tace da zabar 20 daga cikin samfurin labaran da aka aiko waɗanda suka fi burgewa a watan Augusta, 2020 Daga nan za a nemi masu waɗannan samfuran labaran guda 20 da su halarci wata bita ta musamman ta kwana 1 da za a yi a birnin Katsina a watan Satumba, 2020, don koya musu abin da ake buƙata da yadda za su tsara labaran domin su dace da manufar da aka assasa gasar inda daga karshe, za a zabi labarai goma da suka yi zarra domin fitar da na daya zuwa na goma.
Ana sa ran waɗanda suka halarci bitar su koma gida su kammala rubutun labaran zuwa watan Octoba 2020. Za a ba da awalaja ga mutane ashirin da labaran su suka samu zuwa zagaye na gaba (waɗanda suka halarci bitar).
Za a tace da tsara da kuma buga labaran, a ƙaddamar da su a wani gaggarumin biki da za a shirya a Katsina, a watan Disamba da yardar Allah.

DOKOKIN RUBUTUN
Domin shiga wannan tsarin samar da gajerun labarai na Hausa wanda zai kasance mai ɗauke da kalmomi 5000, marubuta na da damar su yi bincike da nazari da tuntuɓa na tsawon wata ɗaya kafin aiko da labaran, bayan halartar bita da aka shirya musu.
1. Ba a kuma buƙatar sai ana da wani kwali ko satifket na musamman kafin a kasance cikin wannan tsarin samar da labarai, illa iyaka gwaninta da fasahar tsara labaran Hausa. Ana kuma bukatar rubutun ya dace da batutuwan da suka shafi muhalli da fasahar zane-zanen gidaje da ayyukan bankin bada lamunin gina gidaje na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Arc. Ahmad Musa Ɗangiwa ke gudanarwa da sauran makamntansu.
2. Dole ne ya kasance an yi amfani da ka'idojin rubutu bisa daidaitaciyar Hausa.
3. Dole ne a yi rubutun bisa tsarin haruffa masu ƙugiya, kuma rubutun ya kasance an aika shi bisa tsarin Microsoft word ko PDF. Zuwa ga wannan email din dangiwaliterary2020@gmail.com
4. Wajibi ne labaran su kasance sabbi waɗanada ba a taba shiga wata gasa da su ba ko kuma buga su a wasu jaridu ko zauruka na kafafen sadarwa.
5. Wannan gasa ba ta buƙatar ayi haɗin guiwa wajen shigarta ana buƙatar daidaikun mutane ne kawai mace ko namiji.
6. Wannan gasar buɗe take ga duk wanda ya iya rubutu da harshen Hausa ne kadai,matuƙar da zai iya kiyaye dokoki da ƙa'idojin da aka gindaya.
7. Wajibi ne a aiko da somun taɓi na kalma dubu (1000) daga 12 dare na ranar 4 ga watan Yulin 2020 zuwa 17 na hudu ga watan Agustan 2020.
8. Duk labarin da aka shiga gasar da shi mallakin gasa ne, ba a yarda a sake ɗaukar shi a shigar da shi wata gasa ba ko makamancin haka.
9. Hukuncin da alkalan gasa suka yanke shi ne na ƙarshe ba za a sake tattaunawa ko duba hukuncin ba, bayan fitar sakamako.
10. Wajibi ne duk wanda zai turo da labarinsa ya aiko da lambar wayarsa da takaitaccen bayani game da shi.

KYAUTUKAN DA ZA A BAYAR
Za a bada kyautuka ga waɗanda suka shiga gasar daga na daya zuwa na goma kuma a buga littafin, a kaddamar da shi a yayin bikin bayar da kyautukan. Ga yadda tsarin kyaututukan zasu kasance.
a. Kyautukan da za a bayar ga mutane uku na farko
i. N250,000 ga wanda ya zo na ɗaya
ii. N150,000 ga wanda ya zo na biyu
iii. N100,000 ga wanda ya zo na uku
iv. Wanɗanda suka zo na huɗu zuwa na goma kowanensu za a bashi kyautar N50,000
Za a bayar da Kambu ga na daya zuwa na uku, sannan kuma dukkan mutane goma da suka yi zarra za a basu takardar sheda wadda take ɗauke da sa hannun shugaban hukumar bankin bayar da lamuni don gina gidaje na kasa Arc. Ahmad Musa Ɗangiwa.
Domin tuntuba ko ƙarin bayani
08036954354
09022709603

3 comments:

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...