Monday, December 23, 2019

HAUSA SHORT STORY: RAMAKON ALHERI...


RAMAKON ALHERI...
Gajeren Labari
Kabiru Yusuf Fagge

Wani Alhaji ne, yana da shago a kasuwar Sabongari, yana sayar da kayan 'karau, sai wani bawan Allah ya zo gare shi, ya roke shi, ya ba shi gefen shagon nasa don ya rinka sayar da kayan miya, idan ya so ko wani abu sai ya rinka biya a matsayin kudin haya.
Alhajin nan ya ce ba komai, ya zauna ba sai ya rinka bayar da komai ba, Malam mai kayan miya, ya yi godiya, washegari ya fara sana'arsa ta sayar da kayan miya.
Yau da gobe, Allah ya buda wa mai kayan miya, ya habaka, yana ciniki sosai. To zuciya ba ta da kashi, da Alhaji mai kayan karau ya ga haka, sai zuciyarsa ta rinka kulla masa mugun abu, don haka watarana sai ya kira Malam mai kayan miya, kai tsaye ya ce masa lallai yana so ya tashi daga gefen shagonsa yana son wurin.
Malam mai kayan miya ya yi ta rokonsa Allah - Annabi ya yi masa hakuri, ya kyale shi ya ci gaba da kasuwancinsa, amma fafur Alhaji mai kayan karau ya ki, ya ce, ya ba shi zuwa jibi ya tashi.
Haka, Malam mai kayan miya yana hawaye, yana komai, ya bar wurin. Bayan tafiyarsa, Alhaji ya dubi abokinsa ya ce, "Ai ni ma, wani zan kawo in rinka saro masa kayan miyar yana siyar min, ina biyan shi."

Sunday, December 22, 2019

GIDAUNIYAR MARUBUTA: TA TALLAFAWA WANI MARUBUCI



GIDAUNIYAR MARUBUTA: TA TALLAFAWA WANI MARUBUCI


Gidauniyar ta dade tana aiki gwargwadon iyawarta ga wasu marubuta da suka cancanci tallafinta. Amma ba kowanne marubuci ne ya sani ba, bare wasu na waje.
Wannan ya faru ne saboda tsarin ita gidauniyar shi ne; yawancin marubutan da suka samu tallafin gidauniyar babu wanda ya taba zuwa ya ce yana cikin wani da ya kamata a taimaka masa, kawai gidauniyar ce take lura da hakan kuma ta yi gwargwadon iyawarta wajen tallafawar.

Saturday, November 9, 2019

LABARIN LAIFUKA KO TASHIN HANKALI



*Rubutunka Tunaninka*
Kabiru Yusuf Fagge

*Labarin Laifuka Ko Tashin Hankali*
A ko'ina a fadin duniya ana samun tashe-tashen hankula, hakan ya zama wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum. Saboda haka ne ake samun yawan rubuce-rubucen labarai a kan tashe-tashen hankula.

Tuesday, October 29, 2019

DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI


*RUBUTUNKA TUNANINKA*
DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI

1.   Maimaici: Maimaita karanta labarin tare da sake kwafewa fiye da sau daya.
2.   Farawa da wani rikici.
3.   Farawa da labarin ainihin abin da ke faruwa a lokacin, ba farawa da tunanin baya ba ko mafarki.
4.   Kar ka sakar wa mai karatu ragamar sanin inda labari ya dosa daga farko zuwa karshe.
5.   Kar ka tsawaita bayani – amma ban da tsanantawa wajen boye abubuwa da yawa.
6.   Kana iya kirkirar matsaloli guda biyu. Cikin gidan tauraron labari da waje.
7.   Ka dinga furta magana ko kalaman dake cikin labarinka a fili, musamman yayin maimaita karantawa, don gane cancantarsu ko rashin dacewarsu.
8.   Yi amfani da siffatau, aikatau da maganganu ma fi dacewa.
9.   Ka tabbatar abubuwan da ka sa ko bayanan da ka yi amfani da su a labarinka sun bayar da ma’ana.

Hausa Novel Cover: BATAN BASIRA...


KHADDU ARABI 1 & 2



GWARAZAN GASAR HIKAYATA 2019



Wednesday, October 9, 2019

LABARAI UKU DA SUKA CANCANCI LASHE GASAR HIKAYATA

LABARAI UKU DA SUKA CANCANCI LASHE GASAR HIKAYATA

Salo na cikin ma'aunan da alkalan Hikayata suka yi amfani da su

Masu iya magana kan ce "Ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.

Tuesday, October 8, 2019

GASAR HIKAYATA 2019



GASAR HIKAYATA 2019

RUBUTU MAI KYAU: MAFITA GA SABON MARUBUCI

Rubutunka Tunaninka
Kabiru Yusuf Fagge
 
RUBUTU MAI KYAU: MAFITA GA SABON MARUBUCI
Akwai abubuwa da suke taimaka wa sabon marubuci ya inganta rubutunsa ya zamo mai kyau. Sau tari marubuta sukan manta da wadannan abubuwa, kuma suna bayar da matsala a rubutu. Wadannan abubuwa su ne kamar:-
(1) Saka sauye-sauye ko sabani a tsakanin taurari, ko a rayuwar tauraro. Misali: Da farko sun tsani juna – A karshe sun koma son juna.

(2) Sauyin halayya: Da farko ya kasance mashayi – a karshe ya shiryu.

(3) Sauyi a zuciyar makaranci: Da farko kowa ya dauka tauraron labarin ne ya aikata wani laifi – a karshe ashe ba shi ya aikata ba.

(4) Ka da ka dora taurarin labarinka a kan rayuwar farin ciki tun daga farkon labari har karshe. Idan ya kasance haka, bai zama labari ba. Don haka dole ne ka gindaya musu wasu matsaloli ko tangarda, wacce za ta yi kamar ba za a iya warwarewa ba, sai a karshe a samu mafita.

Matsalolin da ake samarwa a labari sun hadar da:
(1) A tsakanin taurarin labarin da wani daga waje.
Misali – Wata tsohuwar budurwar tauraron ta kudirin aniyar ruguza auren tauraron ko ta halin kaka.

-Tsakanin tauraron da abokiyar zamansa.
Misali – Mijinta ne ya kasance cikakken mashayi. Kullum babu zaman lafiya.

-Tsakanin tauraron labarin da wani hali na rayuwa.
Misali – Takaici, wata cuta ko lalura da sauransu.

ABUBUWAN DA MARUBUCI ZAI SANI GAME DA TAURARO
Ya kamata marubuci ya san tauraronsa, don haka akwai wasu manya abubuwa da ya kamata lallai marubuci ya sani game da tauraronsa; babba ko yaro (wannan ya shafi tauraro mace da namiji)
Tauraro (a matsayin babban mutum)
1. Suna
2. Shekaru
3. Fasalinsa/Siffofinsa
4. Gidansa
5. Dangantakarsa/iyayen sa
6. Danginsa/iyalinsa
7. Abokansa a labarin
8. Alakarsa da sauran mutane
9. Aiki ko sana'arsa a labarin
10. Dabi'u ko halayyarsa
11. Irin abincin da ya fi so
12. Yanayin kayan da yake sawa
13. Yadda jama'a suke kallon sa
14. Ra'ayin sa
15. Burin sa
16. Muhimmin abin da ya kamata a sani a tare da shi
17. Shin makaranta za su so shi a ransu ko za su tsane shi?

Tauraro (karamin yaro)
1. Suna
2. Shekaru
3. Ranar haihuwar sa
4. Fasalinsa/Siffofinsa
5. Gidansu
6. Sunan mahaifinsa
7. Sunan mahaifiyarsa
8. 'Yan uwansa maza da mata
9. Matsayinsa a gidansu (na nawa ne?)
10. Abokansa na kusa
11. Abokansa na musamman
12. Abin da ya fi so (karatu, kallo ko kade-kade?)
13. Abin da ya fi ki
14. Matsayinsa a makaranta
15. Halayyarsa a makaranta
16. Wasannin da ya fi so
17. Abincin da ya fi so
18. Kayan da ya fi son sa wa
19. Alakar sa da sauran yara
20. Mutumin da ya fi masa muhimmanci a rayuwarsa (uwa, uba ko dan'uwa)
21. Halayyar sa a gida
22. Yadda mutane suke kallon sa
23. Ra'ayin sa
24. Shin zai shiga ran makaranta ko za su ji sun tsane shi?

KARIN BAYANI A KAN ABUBUWAN DA SUKA GABATA
1. Idan tauraron labarin yana aiki ko sana'a; shin yana jin dadin yi?
2. Daga cikin dabi'un tauraron akwai munana? Wadanne iri ne?
3. Wane irin buri ya ke da shi? Wane irin mutum yake son zama?
4. Me ya fi tsoro?
5. Mene ne aibun sa? Me ya rasa a rayuwarsa?
6. Wa ya fara so a ransa?
7. Wane abu mara kyau ne ya taba samun sa?
8. Dangane da burin sa na rayuwa. Ya cimma burin? Ta ya ya?
(c) Kabiru Yusuf Fagge

Friday, September 6, 2019

MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA


Rubutunka Tunaninka

 MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA
Gabatarwa
Muna farawa da sunan maqagin baiwa da hikima, wanda ya saukar da Alkur'ani da ya labarta mana labaran al'ummun da suka gabata don izina da misali. Yabo ga mafi girman darajar halittun duniya da na lahira, (S.A.W.)
Da farko an samar ko in ce an sabunta wannan fili ne a wannan zaure domin darasi a kan DABARUN RUBUTA LABARI (littafi ko gajeren labari); DA SAURAN MATAKAN YIN RUBUTU MAI ARMASHI, a lokaci guda za a rinqa tattaunawa don faxaxa ilimi a harkar rubuce-rubucen labaru na Hausa.
Rubutunka Tunaninka;- Duk marubuci kafin ya yi rubutu sai ya yi tunani akan abin da zai rubuta, don haka kenan rubutun da marubuci ya yi tunaninsa ne, (hakan ya zama rubutunka tunaninka) akasi daya da ake samu shi ne tunanin ya zama ingantacce ko karvavve ko kuma akasin hakan.

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...