Tuesday, October 29, 2019

DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI


*RUBUTUNKA TUNANINKA*
DOKOKI 9 NA INGANTA LITTAFI

1.   Maimaici: Maimaita karanta labarin tare da sake kwafewa fiye da sau daya.
2.   Farawa da wani rikici.
3.   Farawa da labarin ainihin abin da ke faruwa a lokacin, ba farawa da tunanin baya ba ko mafarki.
4.   Kar ka sakar wa mai karatu ragamar sanin inda labari ya dosa daga farko zuwa karshe.
5.   Kar ka tsawaita bayani – amma ban da tsanantawa wajen boye abubuwa da yawa.
6.   Kana iya kirkirar matsaloli guda biyu. Cikin gidan tauraron labari da waje.
7.   Ka dinga furta magana ko kalaman dake cikin labarinka a fili, musamman yayin maimaita karantawa, don gane cancantarsu ko rashin dacewarsu.
8.   Yi amfani da siffatau, aikatau da maganganu ma fi dacewa.
9.   Ka tabbatar abubuwan da ka sa ko bayanan da ka yi amfani da su a labarinka sun bayar da ma’ana.


KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA NA 1
*a ga* ba *aga* ba
*a can* ba *acan* ba
*a nan* ba *anan* ba
*a yi* ba *ayi* ba
*a ba* ba *aba* ba
*a bar* ba *abar* ba
*a bi* ba *abi* ba
*a da* ba *ada* ba
*a je* ba *aje* ba
*a kai* ba *akai* ba
*a kan* ba *akan* ba
*a kan doki* ba *akan doki* ba
*a kan hanya* ba *akan hanya* ba
*a kan kujera* ba *akan kujera* ba
*a sa* ba *asa* ba
*a zo* ba *azo* ba
*A'isha* ba *Aisha* ba
*Abdullahi* ba *Abdul Lahi* ba
*Abdussalam* ba *AbdulSalam* ba
*abin da* ba *abinda* ba
*aka ce* ba *akace* ba
*akan me?* ba *a kan me?* ba
*akan ci tuwo* ba *a kan ci tuwo* ba
*akan so haka* ba *a kan so haka* ba
*akan sha ruwa* ba *a kan ruwa* ba
*akan yi* ba *a kan yi* ba
*ake* ba *a ke* ba
*al'adu* ba *aladu* ba
*al'umma* ba *alumma* ba
*aljanna* ba *al-janna* ba
*Alkur'ani* ba *Al-kur'ani* ba
*Allah da ikonSa* ba *Allah da ikonsa* ba
*Allah da manzonSa* ba *Allah da Manzonsa* ba
*Allah Ya hana* ba *Allah ya hana* ba
*Allah Ya fada* ba *Allah ya fada* ba
*ambaliya* ba *anbaliya* ba
*amfani* ba *anfani* ba
*an sa* ba *ansa* ba
*an yi* ba *anyi* ba
*an ki* ba *anki* ba
*an bi* ba *anbi* ba
*an ce* ba *ance* ba
*an ga* ba *anga*
*an so* ba *anso*
*ana ba* ba *a na ba* ba
*ayyuka* ba *aiyuka* ba
Ga mai tambaya ya iya yi.
Na gode,
Kabiru Yusuf Fagge

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...