RAMAKON ALHERI...
Gajeren Labari
Kabiru Yusuf Fagge
Wani Alhaji ne, yana da shago a kasuwar Sabongari, yana
sayar da kayan 'karau, sai wani bawan Allah ya zo gare shi, ya roke shi, ya ba
shi gefen shagon nasa don ya rinka sayar da kayan miya, idan ya so ko wani abu
sai ya rinka biya a matsayin kudin haya.
Alhajin nan ya ce ba komai, ya zauna ba sai ya rinka bayar
da komai ba, Malam mai kayan miya, ya yi godiya, washegari ya fara sana'arsa ta
sayar da kayan miya.
Yau da gobe, Allah ya buda wa mai kayan miya, ya habaka,
yana ciniki sosai. To zuciya ba ta da kashi, da Alhaji mai kayan karau ya ga
haka, sai zuciyarsa ta rinka kulla masa mugun abu, don haka watarana sai ya
kira Malam mai kayan miya, kai tsaye ya ce masa lallai yana so ya tashi daga
gefen shagonsa yana son wurin.
Malam mai kayan miya ya yi ta rokonsa Allah - Annabi ya yi
masa hakuri, ya kyale shi ya ci gaba da kasuwancinsa, amma fafur Alhaji mai
kayan karau ya ki, ya ce, ya ba shi zuwa jibi ya tashi.
Haka, Malam mai kayan miya yana hawaye, yana komai, ya bar
wurin. Bayan tafiyarsa, Alhaji ya dubi abokinsa ya ce, "Ai ni ma, wani zan
kawo in rinka saro masa kayan miyar yana siyar min, ina biyan shi."
Suka yi dariya.
Washegari ina zaune a gidan Malam mai kayan miya ya zo, ya
gaya min halin da ake ciki, na dangane da tashinsa da Alhaji mai kayan karau ya
yi. Na dube shi na ce, "To Malam yanzu me ka yanke za ka yi?"
Mai kayan miya ya ce, "Babu abin da na yanke, kai nake
so ka yi tunani ka yanke mafita."
Na dan yi tunani, kana na ce, "Shi kenan, bari zuwa
gobe zan je kasuwar in same shi."
Ya ce "To."
Washegari da sassafe na isa kasuwar Sabongari, rumfar Alhaji
Mai kayan karau, bayan mun gaisa, na bayyana masa kaina, nan da nan ya gane ni,
sannan na gaya masa abin da ya kawo ni, batun wurin da Mai kayan miya yake
sana'a.
Ya dube ni, ya ce "To Kabiru, kai ne za ka kwashe masa
kayan ke nan?"
Na girgiza kai na ce, "Alhaji akwai abin da ba ka sani
ba, wato wannan rumfar da kake ciki ta Malam Mai kayan miya ce..." Ya yi
saurin sake kallona, bai yi magana ba, na ci gaba da cewa, "Kwarai kuwa,
domin lokacin da aka ce za a siyar da ita, ka ce kai ba za ka iya siya ba, shi
ya siye ta, kuma ya ki gaya maka ne don kar ka takura ganin mai rumfa a waje
dan haya a ciki. Sannan ai ka ga an yi maka ragin kudin rumfar ko? To shi ya sa
aka yi ragin, kuma ya hana wakilin rumfar ya gaya maka shi ne mai rumfar."
Na dan numfasa.
"Yanzu turo ni ya yi in ba ka hakuri, idan har ba wani
abu za ka yi da wurin da yake sana'ar ba, ka bar shi ya ci gaba da neman
abincinsa, don mutane sun saba da shi a wurin."
Alhaji Mai kayan karau ya yi sototo cikin mamaki yana
dubana, ya ce, "To yanzu wanne hakuri za ka ba ni, ai ni ne mai bayar da
hakuri, daman sharrin zuciya ne, tashhi ka raka ni gidansa in ba shi
hakuri." Ya mike a zabure.
Na ce, "A'a, ka kwantar da hankalinka, zai zo kasuwa,
kuma ba sai ka ba shi hakuri ba, kai yake so ka hakura."
Shiru kawai ya yi, yana kallona, wannan al'amari, yana cikin
lamarin da ya dade yana yawo a kwakwalwata, lallai aikata alheri ka ga alheri,
Allah ka sa mu fi karfin zuciyarmu, amin.
Idan kai ne Mai kayan miya, ya ya za ka yi da Alhaji Mai
kayan karau?
No comments:
Post a Comment