Tuesday, November 19, 2019

AMFANIN YAWAN KARANCE-KARANCE


AMFANIN YAWAN KARANCE-KARANCE
Daga Abdullahi Hassan Yarima


1) Kara sanin girman Ubangiji.
2) Fahimtar wata baiwa da Allah ya yi maka.
3) Sanin abinda ba ka sani ba.
4) Tunatar da kai abinda ka manta.
5) Fadada fahimta.
6) Koyar da zuzzurfan tunani.
7) Rage zazzafan ra'ayi.
8) Iya kallon abu ta fuskoki daban-daban.
9) Koyon azanci.
10) Sanin dabarun gudanar da rayuwa.
11) Sanin dabi'u ma su kyau.
12) Sanin muhimmancin lokaci.
13) Koyon hikima.
14) Sanin cewa bayyana ra'ayi sabanin naka ba laifi ba ne.
15) Sanin yadda za ka taimaki al'ummarka.
16) Koyon wani yaren.
17) Samun ilimi a Fage daban-daban.
18) Samar da nutsuwa ta musamman.
19) Iya Koyon yadda ake magana mai ma'ana.
20) Koyar da bincike.
Daure kullum ka karanta ko da shafi daya ne na littafi. Za ka yi mamaki.

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...