Rubutunka Tunaninka
Kabiru Yusuf Fagge
RUBUTU MAI KYAU: MAFITA GA SABON MARUBUCI
Akwai abubuwa da suke taimaka wa sabon marubuci ya inganta rubutunsa ya zamo mai kyau. Sau tari marubuta sukan manta da wadannan abubuwa, kuma suna bayar da matsala a rubutu. Wadannan abubuwa su ne kamar:-
(1) Saka sauye-sauye ko sabani a tsakanin taurari, ko a rayuwar tauraro. Misali: Da farko sun tsani juna – A karshe sun koma son juna.
(2) Sauyin halayya: Da farko ya kasance mashayi – a karshe ya shiryu.
(3) Sauyi a zuciyar makaranci: Da farko kowa ya dauka tauraron labarin ne ya aikata wani laifi – a karshe ashe ba shi ya aikata ba.
(4) Ka da ka dora taurarin labarinka a kan rayuwar farin ciki tun daga farkon labari har karshe. Idan ya kasance haka, bai zama labari ba. Don haka dole ne ka gindaya musu wasu matsaloli ko tangarda, wacce za ta yi kamar ba za a iya warwarewa ba, sai a karshe a samu mafita.
Matsalolin da ake samarwa a labari sun hadar da:
(1) A tsakanin taurarin labarin da wani daga waje.
Misali – Wata tsohuwar budurwar tauraron ta kudirin aniyar ruguza auren tauraron ko ta halin kaka.
-Tsakanin tauraron da abokiyar zamansa.
Misali – Mijinta ne ya kasance cikakken mashayi. Kullum babu zaman lafiya.
-Tsakanin tauraron labarin da wani hali na rayuwa.
Misali – Takaici, wata cuta ko lalura da sauransu.
ABUBUWAN DA MARUBUCI ZAI SANI GAME DA TAURARO
Ya kamata marubuci ya san tauraronsa, don haka akwai wasu manya abubuwa da ya kamata lallai marubuci ya sani game da tauraronsa; babba ko yaro (wannan ya shafi tauraro mace da namiji)
Tauraro (a matsayin babban mutum)
1. Suna
2. Shekaru
3. Fasalinsa/Siffofinsa
4. Gidansa
5. Dangantakarsa/iyayen sa
6. Danginsa/iyalinsa
7. Abokansa a labarin
8. Alakarsa da sauran mutane
9. Aiki ko sana'arsa a labarin
10. Dabi'u ko halayyarsa
11. Irin abincin da ya fi so
12. Yanayin kayan da yake sawa
13. Yadda jama'a suke kallon sa
14. Ra'ayin sa
15. Burin sa
16. Muhimmin abin da ya kamata a sani a tare da shi
17. Shin makaranta za su so shi a ransu ko za su tsane shi?
Tauraro (karamin yaro)
1. Suna
2. Shekaru
3. Ranar haihuwar sa
4. Fasalinsa/Siffofinsa
5. Gidansu
6. Sunan mahaifinsa
7. Sunan mahaifiyarsa
8. 'Yan uwansa maza da mata
9. Matsayinsa a gidansu (na nawa ne?)
10. Abokansa na kusa
11. Abokansa na musamman
12. Abin da ya fi so (karatu, kallo ko kade-kade?)
13. Abin da ya fi ki
14. Matsayinsa a makaranta
15. Halayyarsa a makaranta
16. Wasannin da ya fi so
17. Abincin da ya fi so
18. Kayan da ya fi son sa wa
19. Alakar sa da sauran yara
20. Mutumin da ya fi masa muhimmanci a rayuwarsa (uwa, uba ko dan'uwa)
21. Halayyar sa a gida
22. Yadda mutane suke kallon sa
23. Ra'ayin sa
24. Shin zai shiga ran makaranta ko za su ji sun tsane shi?
KARIN BAYANI A KAN ABUBUWAN DA SUKA GABATA
1. Idan tauraron labarin yana aiki ko sana'a; shin yana jin dadin yi?
2. Daga cikin dabi'un tauraron akwai munana? Wadanne iri ne?
3. Wane irin buri ya ke da shi? Wane irin mutum yake son zama?
4. Me ya fi tsoro?
5. Mene ne aibun sa? Me ya rasa a rayuwarsa?
6. Wa ya fara so a ransa?
7. Wane abu mara kyau ne ya taba samun sa?
8. Dangane da burin sa na rayuwa. Ya cimma burin? Ta ya ya?
(c) Kabiru Yusuf Fagge
No comments:
Post a Comment