WAKAR NEMAN TAIMAKO GA ALLAH
Ta Alhaji Mudi Sipikin
1. Allah Ta'ala Jalla na bid'i taimako,
Na ko fake a gare ka ya Allahu.
2. Nai wo salati ga Annabinmu Muhammadu,
Sahabai da Alayensa ya Allahu.
3. Mun tabbata shi Musdafa Manzonka ne,
Mun sallama mun bi shi ya Allahu.
4. Allahu kai ne wanda ba ka da kishiya,
Ka halicci komai mun sani Allahu.
5. Kuma mun sani kowa idan ya ga ya matsu,
Komai irin laifinsa ya Allahu.
6. Kai ne kake kar'bar du'a'in taliki,
Komai yawan laifinsa ya Allahu.
7. Rahamarka ga ta a ko ina fa ana gani,
Ka baiwa kowa mun sani Allahu.
8. Mun gaskata bisa wanga zance kamili,
Ba gardama a gare mu ya Allahu.
9. Ya Rabbi ni ma ga ni zan wo addu'a,
Na durkusa a gare ka ya Allahu.
10. Rokon da zan yi gare ka da ma ka sani,
Kuma kai ka fi ni saninsa ya Allahu.
11. Ni dai nufina Rabbi kai min gafara,
Daga duniya har lahira Allahu.
12. Ka saka ni bin hanyar Muhammadu shugaba,
San nan ka ban yardarka ya Allahu.
13. Allah raba mu da hange-hangen zuciya,
Na kaba'ira da saga'ira Allahu.
14. Sannan ibada wadda yanzu mu ke ta yi,
Karbe ta ya Allahu ya Allahu.
15. Kuma Rabbi sanya mun yi don Zatinka ne,
Kuma ka yi umarni da yi Allahu.
16. Ba don gudun wuta ko shiga Aljanna ba,
Wannan fa duk bayinka ne Allahu.
17. Ba don halimmu ba Rabbi kai mana agaji,
Komai da komai na gare ka Ilahu.
18. Ya Rabbi yadda ka wo da mu mun gaskata,
Rahamarka na a gare mu ya Allahu.
19. Mu dai Rahimu mu ke kiranka a lahira,
Nan duniya Rahammu ya Allahu.
20. Ya Rabbi duk zunubammu wanda mu ke ta yi,
Shafe shi ya Allahu ya Allahu.
21. Dukkan irin sharrin da Shaidan ke ta yi,
A cikin zukatan 'yan Adam Allahu.
22. Sanya ya zam ba zai yiwo nasara ba shi,
Ya Rabbi mun kararsa gunka Ilahu.
23. Ya Rabbi ka san yadda za ka yiwo da shi,
Sharrin la'inu ka fid da mu Allahu.
24. Ya Rabbi duk mai hasadata ka sani,
Har mai habaice-habaice ya Allahu.
25. Har masu zagina suna dada yi da ni,
Har masu zundena da baki Ilahu.
26. Har masu so su ga na bace su yi dariya,
Har masu gillina a ransu Ilahu.
27. Ya Rabbi ka san yadda za ka yiwo da su,
Komai da komai na wajenka Ilahu.
28. Ya Rabbi duk wahalar da nan gaba za mu sha,
Kuma har ta yanzu da ke ciki Allahu.
29. Ya Rabbi shafe dukkaninta Ubangiji,
Ya zamo fa ba wahala a kammu Ilahu.
30. Ya Rabbi ko da tun azal ka kaddara,
Wani dan jidali kammu ya Allahu.
31. Allah Ta'ala Rabbi to shafe mana,
Ka ije masifar kammu ya Allahu.
32. Ya Rabbi mu bayinka ba mu da hankali,
Laifimmu ya yi yawa kwarai Allahu.
33. Ga zuciyarmu tana ta shashatar da mu,
Iblis yana ta zugata ya Allahu.
34. Ya Rabbi duk tarommu ba mai taimako,
Kai ne kadai mai taimako Allahu.
35. Dukkan irin laifimmu ko da yai yawa,
Ko da dubu nawa mun kawo Allahu.
36. Mun zo wajenka Afuwu don ka fitad da mu,
Komai yana hannunka ya Allahu.
37. Tun dai da komai kai ka ke iko da shi,
Na wakkala a gare ka ya Allahu.
38. Ya Rabbi duk tsanani gare ka a ke bidar,
Rahama a samu gunka ya Allahu.
39. Wata duk dabara tamu har wani kokari,
Mun bar shi da ma babu shi Allahu.
40. Ba don halimmu ba Rabbi kai mana gafara,
Ga shiga ukun ga da mun kawo Allahu.
41. Ya Rabbi ba mai magani sai kai kadai,
Ba taimako sai kai kadai Allahu.
42. Dukkan fa rokon nan da na yi Ubangiji,
Na kyauta zatto gunka ya Allahu.
43. Ya Rabbi ka san babu inda fa za na je,
Sai dai gare ka Ubangiji Allahu.
44. In ka ki karba wai ina kuma zan nufa,
Wa zana je ni wajensa ya Allahu.
45. Sai kai kadai Allahu nan muka dogara,
Komai da komai na wajenka Ilahu.
46. Allahu ya Allahu Sarkin gaskiya,
Nai sujjada a gare ka ya Allahu.
47. Ya Rabbi don sirrin da kun yi da Annabi,
Na batun wajen sadanku ya Allahu.
48. Don littafai basa ma wuya ya Rabbana,
Ya Rabbi don zatinka Jalla Ilahu.
49. Da Makarrabuna da Lauhu don kuma Alkalam,
Ya Rabbi don Ka'aba Rahimu Ilahu.
50. Ya Rabbi don shumagabammu Hasan kaza,
Kuma har Husaini Rahimu ya Allahu.
51. Ya Rabbi don darajar Aminatu hakaza,
Don Fadima Zahra'u ya Allahu.
52. Ya Rabbi don shumagabammu na Kaulaha,
Ya Rabbi na roke ka Jalla Ilahu.
53. Ya Rabbi don matan da ke yin kokari,
Mabiya mazansu da gaskiya Allahu.
54. Don masu cewa ba mu ba mu Ubangiji,
Kullum dare rokonka ya Allahu.
55. Allah ka amsa duk irin rokon da nai,
Komai yana hannunka ya Allahu.
56. Kowa ya ce Allahu kai ka isar mana,
Wallahi zai san taimakonka Illahu.
57. Kuma babu fifiko ga dukkan zamani,
Sai in da tsoron Rabbi Jalla Ilahu.
58. Albarkacin lafazin Jalala mun bida,
Allahu ya Allahu ya Allahu.
59. Sittin da shidda idan ka kirga za ka ga,
Suld'anu ke nan ba musu Allahu.
60. Mai tsara wa'kar nan idan aka tambaya,
Mudi Sipikin ne ya ro'ki Ilahu.
An ciro wannan waka daga cikin littafin TSOFAFFI DA SABABBIN WAKOKIN ALHAJI MUDI SIPIKIN
A wata shekara alhaji mudi sipikin ya wallafa wakar neman taimakon Allah
ReplyDelete