LABARAI UKU DA SUKA CANCANCI LASHE GASAR HIKAYATA
Salo na cikin ma'aunan da alkalan Hikayata suka yi amfani da su
A fagen Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, ko wanne labari ne zai ciri tuta a bana?
Yanzu dai ta tabbata "A Juri Zuwa Rafi" da "Ba a Yi Komai Ba" da "Maraici" ne labaran da suka tsallaka zuwa mataki na karshe a gasar, kuma marubuciyar daya daga cikinsu ce za ta zama Gwarzuwar Hikayata ta bana.
Alkalan gasar ne dai suka darje wadannan labarai daga cikin guda 25 din da suka duba.
Abin da ya bambanta wadannan labarai har ya sa suka yi fice, inji jagorar alkalan, Dokta Aliya Adamu Ahmad, shi ne "Salo".
Ta kara da cewa, "Salo dabara ce ta…isar da sakonka.
Marubutan sun yi amfani da wani salo na daga hankalin mai sauraro ko mai karatu
Dokta Aliya Adamu Ahmad, Jagorar Alkalan Hikayata ta Bana
"Marubutan sun yi amfani da wani salo na daga hankalin mai sauraro ko mai karatu, kuma su hukunta ko wanne tauraro daidai da rawar da ya taka a cikin labari".
"A Juri Zuwa Rafi" dai labari ne a kan wata yarinyar karama wadda wani mawadaci ya yi wa fyade, kuma danginta suka bukaci a rufe maganar amma mahaifiyarta ta ce sai inda karfinta ya kare. Labarin, wanda Jamila Babayo ta rubuta, ya kare ne da hukunta mawadacin, Alhaji Lado, sakamakon jajircewar da wasu mata suka yin a kwato wa yarinyar, Aisha, hakkinta.
Shi kuwa "Maraici", Safiyya Ahmad ce ta rubuta shi a kan yadda yara marayu, musamman mata, kan tsinci kansu a cikin tasku. Sai dai tauraruwar labarin, Karima, ba ta bari hakan ya karayar da zuciyarta ba; a maimakon haka sai ta jajirce don ganin ta mori rayuwarta, al'umma ma ta more ta.
Labari na uku, wato "Ba a Yi Komai Ba", irin tsangwamar da Uwani ke fuskanta daga mijinta da danginsa saboda tana haifar 'ya'ya mata marubuciyarsa, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta tabo. Marubuciyar ta nuna yadda tauraruwar ta yi ta shiga matsala saboda wani abu da ba ta da iko a kai.
Labarai sama da 300 ne dai aka shigar gasar ta Hikayata ta bana, kuma kafin a kawo wannan mataki sai dai aka tankade labaran aka fitar da 30.
Wajen tantancewar dai an yi amfani da ka'idojin shiga gasar, musamman game da adadin kalmomi, da bin ka'idar rubutu, da amfani da daidatacciyar Hausa, da kauce wa amfani da kalaman da ba su dace ba da zarge-zarge, da ma tabbatar da cewa labarin kagagge ne.
Baya ga labarai ukun da alkalan suka fitar, sun kuma ayyana wasu 12 a matsayin wadanda suka cancanci yabo.
Labarai 12 da suka cancanci yabo
* Kaddarata
* Kura da Shan Bugu
* Ranar Salla
* Menene Laifina
* Zahra
* Mugunyar Kawa
* Nadama
* Kaddarar Rayuwa
* Bakin Alkalami
* Da Guminmu
* Awa Arba'in da Takwas
* Zamanin da Nake Raye
Dukkan labaran 15 dai za a karanta su nan gaba a rediyo a kuma saka su a shafukanmu na intanet da na sada zumunta.
Wace ce Gwarzuwar Hikayata ta bana?
Za a sanar da Gwarzuwar bana ne dai a lokacin bikin karrama wadanda suka yi nasara a gasar, wanda za a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, nan gaba a wannan watan na Oktoba ne dai.
Daga shafin BBCHausa
No comments:
Post a Comment