Tuesday, October 8, 2019

GASAR HIKAYATA 2019



GASAR HIKAYATA 2019

Tuni alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suka fara aikin fitar da labarai uku da suka ciri tuta a bana a yau Talata.

Daga cikin wadannan labarai uku ne kuma za a zabi labarin da zai hau matsayi na daya a gasar.

"Wani muhimmin bambanci tsakanin gasar bana da ta baya", a cewar mukaddashin Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, "shi ne a bana sai ranar da za a karrama gwarzuwar gasar za a fadi sunan wacce ta yi nasara.
"Domin haka ko wacce daga cikin marubutan da labarin ta ya kai wannan mataki za ta iya kasancewa Gwarzuwar Gasar".

Tantancewa
An yi amfani da ka'idojin gasar wurin tanatancewa kamar adadin kalmomi da ka'idojin rubutu
Labarai sama da 300 ne dai aka shigar gasar ta Hikayata ta bana, kuma kafin a kawo wannan mataki sai dai aka tankade aka kuma rairaye labaran zuwa 30.
Wajen tantancewar dai an yi amfani da ka'idojin shiga gasar, musamman game da adadin kalmomi, da bin ka'idar rubutu, da amfani da daidatacciyar Hausa, da kauce wa amfani da kalaman da ba su dace ba da zarge-zarge, da ma tabbatar da cewa labarin kagagge ne.

A mataki na gaba kuma, inda aka sake rairaye labaran, aka fitar da guda 25 (duba teburin da ke kasa), wadanda aka turawa alkalan gasar su uku don zabo su, kuma su darzo wadanda suka fi cancanta.

Labarai 25 da alkalai suka tantance
• Kaddarata
• Duniyarmu
• Hattara Dai Iyaye
• Kura da Shan Bugu
• Ishara
• Ranar Salla
• Menene Laifina
• Maza Mutanenmu
• Cin Amana
• Zahra
• Hansatu 'Yar Baiwa
• Mugunyar Kawa
• Nadama
• Kaddarar Rayuwa
• Maraici
• A Juri Zuwa Rafi
• Bakin Alkalami
• Gaba ta Wuce
• Cikar Buri
• Da Guminmu
• Rudin Duniya
• Ba a Yi Komai Ba
• Awa Arba'in da Takwas
• Abin da Ka Shuka
• Zamanin da Nake Raye

Dukkan labaran 15 dai za a karanta su nan gaba a rediyo a kuma saka su a shafukanmu na intanet da na sada zumunta.

Daga shafin BBCHausa

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...