Saturday, November 9, 2019

LABARIN LAIFUKA KO TASHIN HANKALI



*Rubutunka Tunaninka*
Kabiru Yusuf Fagge

*Labarin Laifuka Ko Tashin Hankali*
A ko'ina a fadin duniya ana samun tashe-tashen hankula, hakan ya zama wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum. Saboda haka ne ake samun yawan rubuce-rubucen labarai a kan tashe-tashen hankula.

Labarin tashin hankali ya kasu zuwa kashi uku:
(1) Akwai kirkirarre; da (2) wanda ba kirkirarre ba; sai kuma (3) tsaka-tsaki (kirkira hadi da gaske).
1- Kirkirarre, shi ne, labarin da marubuci ya zauna ya kirkira a kwakwalwarsa, ba tare da ya taba faruwa a zahiri ba.
2- Wanda ba kirkira ba kuwa shi ne ya kasance labari a kan wani abu da ya taba faruwa a rayuwa ta zahiri, marubuci ya zauna ya rubuce shi tsaf, bayan kwakkwaran bincike a kai.
3- Sai na uku, tsaka-tsaki. Shi ya kasance labari wanda ya taba faruwa, amma a yayin da marubuci ya zo rubutawa, ba zai kwashi duk abin da ya faru gabadaya ba, illa dai ya yi amfani da gundarin abin da ya farun, amma ya sauya abubuwa a cikin labarin.
To mu a nan, za mu dauki wanda ba kirkira ba, wanda kusan in dai a labarin miyagun laifuka ko tashe-tashen hankula ne, shi aka fi rubutawa.

*Matakai:*
1. Marubuci ya zabi irin laifin da zai yi rubutu a kai. Ana so laifin ya kasance fitacce.
2. Tattara bayanai a kan yadda al'amarin ya faru.
3. Bincike a kan ainihin irin wannan laifin. Idan kisa ne, wanda ya aikata kisan, wanda ko wadanda aka kashe da sauran wadanda abin ya shafa.
4. Sai marubuci ya zabi sigar da zai bayar da labarin. Ta fuskar addini, ban dariya ko jarumta.
5. Ka fara zabar sunan labari kafin fara rubuta shi. Sunan zai iya taimaka ma wajen samun abin rubutawa. Amma ka tabbatar labarin zai fassara sunan a karshe labarin.
6. Jera bangarorin labarin a wata takarda, yadda za ka dinga daukowa da xai xai kana fadadawa.
7. Jera sunayen taurarin cikin labarin a wata takardar daban. Za ka iya karawa da sunayen masu tallafa wa tauraron, amma ba dole ba ne.
8. Sai fara rubutu. Kada ka ce za ka rubuta shi a rana guda; a'a ka rubuta shi a kalla tsawon kwanaki ko makonni don bai wa zuciyarka hutu da karin sha'awar rubutun, kamar dai yadda muka fada a baya.

*Karin bayani*
¨     Bayan kammala rubutu, ka tabbatar ka mika shi ga wasu mutanen don dubawa.
¨     Yayin da suka ba ka gyara, kada ka rasa kwarin gwiwa. Ka karba ka gyara.
¨     Koyaushe ka dogara da cikakkun bayanai, kada ka dogara da hasashe.
¨     Kada ka taba tsallake wani bayani a labarin da yake na gaske (wanda ba kirkira ba). Dole komai ya kasance gaske, ba hasashe ba.

KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA NA 3
*da can* ba *dacan* ba
*da dai* ba *dadai* ba
*da ni* ba *dani* ba
*da kai* ba *dakai* ba
*da ke* ba *dake* ba
*da ku* ba *daku* ba
*Da mu* ba *damu* ba
*da nan* ba *danan* ba
*da shi* ba *dashi* ba
*da su* ba *dasu* ba
*da ta* ba *data* ba
*da ya* ba *daya* ba
*damfara* ba *danfara* ba
*darasinmu* ba *darasimmu* ba
*don ka* ba *donka* ba
*donmu* ba *donmu* ba
*don shi* ba *donshi* ba
*Dan'asabe* ba *DanAsabe* ba
*Dandatti* ba *DanDatti* ba
*Dangambo* ba *DanGambo* ba
*Danhassan* ba *DanHassan* ba
*Dankande* ba *DanKande*

Kabiru Yusuf Fagge


No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...