Sunday, December 22, 2019

GIDAUNIYAR MARUBUTA: TA TALLAFAWA WANI MARUBUCI



GIDAUNIYAR MARUBUTA: TA TALLAFAWA WANI MARUBUCI


Gidauniyar ta dade tana aiki gwargwadon iyawarta ga wasu marubuta da suka cancanci tallafinta. Amma ba kowanne marubuci ne ya sani ba, bare wasu na waje.
Wannan ya faru ne saboda tsarin ita gidauniyar shi ne; yawancin marubutan da suka samu tallafin gidauniyar babu wanda ya taba zuwa ya ce yana cikin wani da ya kamata a taimaka masa, kawai gidauniyar ce take lura da hakan kuma ta yi gwargwadon iyawarta wajen tallafawar.

BABU AMBATAR SUNA
A tsarin gidauniyar ba ta ambatar sunan wanda za a tallafawa, shi kansa marubuci ko marubuciyar ba sa sanin za a tallafa musu sai dai kawai su ga tallafin ya zo gare su.


YADDA AKE TATTARA TALLAFIN
Ana tuntubar wasu daga cikin marubuta ne kawai wadanda suke da dama da sukuni a lokacin da ake bukatar tallafin, ko kuma wadanda suka fado mana a rai,kuma cikin ikon Allah ana samun abin da ya kamata.

MADOGARA
Allah da Manzonsa (S.A.W) ne madogarar wannan gidauniya, amma akwai wasu marubuta da dole za mu ambaci sunayensu saboda gidauniyar tana dogara da sahalewarsu, domin ko a wanne lokaci aka je gare su, kai tsaye suke bayarwa, babu je ka ka dawo, a ciki akwai:-
1. Prof. Yusuf Adamu
2. Prof. Abdallah Adamu
3. Aminu Ladan Abubakar (ALA)
4. Sa'adatu Baba Ahmad
5. Fauziyya D. Sulaiman
6. Nazir Adam Salih
7. Umma Sulaiman 'Yan awaki
8. Zahradeen Kallah
Da sauransu.


YADDA AKA FARA
Maganar gaskiya akwai wasu mutane a marubuta wadanda da zarar sun fuskanci wani marubuci ko marubuciya suna cikin halin bukatar taimako za su sanar, kuma za a yi kokarin yin wannan abu, a ciki akwai: Auwal Garba Danborno, Abdulkarim Papalaje, Kabiru Yusuf Fagge, Ibrahim Indabawa kuma sukan shige gaba wajen ganin ko ya ya ne an tallafa wa masu bukatar wannan tallafi.

WADANDA SUKA TALLAFA A WANNAN LOKACI:
-Aminu Ladan Abubakar (ALA)
-Sa'adatu Baba Ahmad
-Prof. Yusuf Adamu
-Abdullahi Hassan Yarima
-Larabi
-Nazir Adam Salih
-Mustapha Jafar
-Bilkisu Yusuf Ali
-Zahraddeen Kallah
-Maimuna Idris Sani Beli
-Muhammad Muhammad Assadiq
-Rahma Abdulmajid
-Kabiru Hannu Daya

KOFA A BUDE TAKE
Kuma har yanzu kofa a bude take ga wadanda idan hakan ta faru, su taimaka, gidauniyar ta kowanne marubuci ne. Sannan muna bai wa wadanda ba ma tuntuba hakuri, hakan na faruwa ne saboda ko dai mantuwa, ko kuma kyale mutum sai wani lokacin.
Mun gode

Kabiru Yusuf Fagge, Abdulkarim Papalaje, Auwalu Danborno, Ibrahim Indabawa
A madadin kwamitin Gidauniyar Marubuta

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...