Friday, September 6, 2019

MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA


Rubutunka Tunaninka

 MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA
Gabatarwa
Muna farawa da sunan maqagin baiwa da hikima, wanda ya saukar da Alkur'ani da ya labarta mana labaran al'ummun da suka gabata don izina da misali. Yabo ga mafi girman darajar halittun duniya da na lahira, (S.A.W.)
Da farko an samar ko in ce an sabunta wannan fili ne a wannan zaure domin darasi a kan DABARUN RUBUTA LABARI (littafi ko gajeren labari); DA SAURAN MATAKAN YIN RUBUTU MAI ARMASHI, a lokaci guda za a rinqa tattaunawa don faxaxa ilimi a harkar rubuce-rubucen labaru na Hausa.
Rubutunka Tunaninka;- Duk marubuci kafin ya yi rubutu sai ya yi tunani akan abin da zai rubuta, don haka kenan rubutun da marubuci ya yi tunaninsa ne, (hakan ya zama rubutunka tunaninka) akasi daya da ake samu shi ne tunanin ya zama ingantacce ko karvavve ko kuma akasin hakan.


MARUBUCI SHI NE UBANGIJIN LABARINSA
Marubuci kamar Ubangiji yake ga labarinsa, kenan dole marubuci ya san (1) farko, tsakiya da karshen labarinsa (2) Dole ne ya san wuri (gari, nahiya kasa dss) da labarinsa ya faru (3) Dole ne ya san lokacin sa ya faru (ma'ana lokacin sanyi ne ko damina, bazara ne ko rani, zamanin dauri ne ko kuma yanzu, shin wanne qarfi ne? Dss)
(4) Dole ne marubuci ya san taurarinsa ciki-da-bai (musamman manyan taurari) - ya san halin kowannensu (mugu da na kirki, saffa-saffa, mai walqiya - mace ce tauraruwar ko namiji ko mata-maza dss) - dole ya san mai tauraronsa ke so, mene ne voye a zuciyarsa, me ke damunsa, me yake son cimma, mene ne burinsa, mene ne ko su wane ne tarnaqinsa - mene ne rauninsa, sannan su waye danginsa da sauransu.
(5) Dole marubuci ya san ta yadda da kuma dalilin rikici a labarinsa; rikici da ke tattare da tauraro shi kaxai da kuma tsakaninsa da sauran taurari.
(6) Dole marubuci ya san inda labarinsa zai kai qoli na rikici da kuma yadda zai warware duk rikicin da wasu zarurruka ko qulle-qulle da dabarun da zai bi don yin haka. Kai hatta kai wa qolin ma sai marubuci ya san dalilinsa - a qarshe ya san duk wasu dabarun gamsar da mai karatu.
(7) Marubuci ya san nau'in labarinsa, ya san abin da ya faru a baya da me zai faru a nan gaba.
(8) Marubuci ya san irin maganar da kowanne tauraro yake yi, da yanayin maganar kowanne tauraro, da rabe-rabensu (wani in'ina yake yi, wani kurma ne, wani maganar bata fita sosai, wani da qarfi da sauransu)
(9) Kenan dole marubuci ya san ciki-da-bai na labarinsa da sauran duk wasu abubuwa da ban zayyano ba a cikin wannan gabatarwar.
A qarshe wannan darasi ne mai tarin yawa wanda yau da gobe idan da rai da lafiya za mu rinqa tattaunawa. Sannan filin yana da tsari guda uku, (1) akwai tambayoyi a farko (2) sai kuma kawo darasi (3) na qarshe kuma tattaunawa.
Saboda yanayin lokaci, idan ba na kusa zan so duk wata tambaya ta tafi kai tsaye cikin akwatina - yadda idan na tattara zan bayar da amsoshin a duk ranekun gabatar da filin a lokacin tattaunawa.
Duk abubuwan da aka ga kuskure ne daga ni ne, darasin na kowa ne idan wani ya ga gyara zai iya gyarawa, abin da kuma aka ga daidai wannan Allah ne ya nufa, na gode.
Kabiru Yusuf Fagge (anka)

No comments:

Post a Comment

RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA

 RANAR HAUSA: ƘUNGIYAR HAUSA TA BUK TA CIRI TUTA Nabila Muhammad Ƙungiyar Hausa ta BUK ƙarƙashin jagorancin Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi ...