Tuesday, February 11, 2020
Sunday, January 26, 2020
Short Story: NA CAJE SHI, YA CAJE NI
NA CAJE SHI, YA CAJE NI!
Kabiru Yusuf Fagge
Karfe tara da wasu 'yan mintuna ne na
dare a lokacin, muna zaune ni da abokina Hassan muna hira, mutane suna ta
wucewa ta gabanmu da motoci, a cikin motocin, wata motar 'yansanda ta zo, ta
gifta mu, tana tafiya a hankali, har sun yi nisa kadan daga inda muke, sai
kuma, muka ga sun dawo da ribas a hankali, har suka zo daf da mu, sannan suka
tsaya, 'yansanda biyu daga cikin hudun da ke bayan motar, suka diro, suka iso
inda muke.
Thursday, January 23, 2020
LITTAFIN KOYAR DA TAJWEEDING RIWATY QALUN
Wannan littafi mai suna TAJWEEDIN
RIWAYATI QALUN fassara ne na littafin (SHARHI RISALATI QALUN) wanda Shehin
Malami Aliyu Muhamad Ad-Dhiba’i mutumin Misra ya rubuta, shi ma kuma sharhi ne
ya yi a kan baitocin da Shehin Malami Muhammad Sa’udi ya tsara a bisa
hukunce-hukuncen tajweed da Imamu Abu Musa Isah, wanda aka yi wa laqabi da
Qalun, wanda shi Shehu ALiyud Dhiba’i ya yi sharhin sa da Larabci, shi kuma
Malam Muhammadus-Su’udiy ya tsamo hukunce-hukunce ne daga littafin Shaxibiy.
Thursday, January 16, 2020
MURUCIN KAN DUTSE.... Tsakure
MURUCIN KAN DUTSE...
(Tsakure daga littafin Murucin Kan Dutse, inda Sanusi ke karanta wani sashe na littafin da mahaifinsa ke rubutawa)
Ahmadu ya yi imanin dan adam ba zai ketare abin da Allah ya rubuto masa ba. Watakila da ya so, da ya gudu lokacin da Akintola ya zo masa da tayin haka. Sannan ‘yan kawanki kadan kafin zuwan Akintola, ai yana Ummara a kasar Saudiyya. Yana can aka kira aka sanar da shi babu lafiya, akwai rade-raden wasu na shirya juyin mulki a kasar, wannan labari bai hana shi kamo hanyar gida ba. A lokacin da ya dawo gida, wani bature D.J Muffet ya zo gida ya same shi, inda a cikin tattaunwarsu yake fada masa ba ya jin zai kai sallah, ma’ana sallah karama. Sannan a daren ranar juma’a ya kira Sarkin Kano Ado Bayero a waya yake sanar da shi labarin juyin mulkin da ake shiryawa, wanda shi ne maganarsu ta karshe.
(Tsakure daga littafin Murucin Kan Dutse, inda Sanusi ke karanta wani sashe na littafin da mahaifinsa ke rubutawa)
Ahmadu ya yi imanin dan adam ba zai ketare abin da Allah ya rubuto masa ba. Watakila da ya so, da ya gudu lokacin da Akintola ya zo masa da tayin haka. Sannan ‘yan kawanki kadan kafin zuwan Akintola, ai yana Ummara a kasar Saudiyya. Yana can aka kira aka sanar da shi babu lafiya, akwai rade-raden wasu na shirya juyin mulki a kasar, wannan labari bai hana shi kamo hanyar gida ba. A lokacin da ya dawo gida, wani bature D.J Muffet ya zo gida ya same shi, inda a cikin tattaunwarsu yake fada masa ba ya jin zai kai sallah, ma’ana sallah karama. Sannan a daren ranar juma’a ya kira Sarkin Kano Ado Bayero a waya yake sanar da shi labarin juyin mulkin da ake shiryawa, wanda shi ne maganarsu ta karshe.
Monday, January 13, 2020
Gajeren Labari: BUHARI YA ZAGA
BUHARI YA ZAGA
Kabiru Yusuf Fagge
Tun da na samu sahalewar hukuma a kan
bincike ya sa, duk lokacin da na samu dama nakan leka ofishin 'yansanda na kusa
da mu, na zauna a bayan kanta ina ganin abubuwan da ke faruwa na tsakanin
jami'an tsaro ('yansanda) da masu kawo kara ko masu laifi.
Ba tonon asiri ba, gaskiya ana tafka
magun-magun da kacabe-kacabe, kiri-kiri ga shi an rubuta baro-baro BELI KYAUTA
NE da Turanci da Yoruba da Ibo har da uwa-uba Hausa, amma duk wanda zai zo karbar
dan'uwansa tsakanin mai gaskiya da mara gaskiya sai ya biya kudi.
Da abin ya ishe ni, sai na matsa kusa da
ofisan da ke kula da ni, kuma ka sahalewa ya rinka amsa min duk tambayoyin da
na yi, na ce masa.
"Yallabai ga shi an rubuta beli
kyauta ne amma na ga duk wanda ya zo sai ya biya." Na kammala fadi ina
nuna masa inda rubutun yake.
Ofisa Bello ya ce, "Wannan kudin da
ka ga suna bayarwa ba beli ba ne, alheri ne, saboda irin kulawa da sasanta
'yan'uwansu da aka yi...."
"To amma yallabai..."
Na yi kokarin katse shi, amma shi ma sai
ya katse ni da cewa, "Wai kai Kabiru cewa aka yi komai ka gani sai ka
tambaya?" Ya dan rage murya, yana kallon wasu manyansa da ke gefe,
"Ya kamata ka sani, a Nijeriya ba komai ake yin bayaninsa dalla-dalla ba,
kuma ba komai ake yin tambaya a kansa ba...Shin ko ka san har yanzu ba a gama
yin cikakken bayanin me kundin tsarin mulkin Nijeriya ke dauke da shi ba, duk
da tarin tambayoyin da ake yi a kansa?" Ya tambaye ni, bai jira na amsa
ba, ya ci gaba, "To ka takaita yin tambayoyi kar ka tambayo abin da ba a
tambaya. Ina fatan ka fahimta."
Na girgiza kai, "Gaskiya ban
fahimce ka ba."
Ya harare ni, "To wannan ita ce
amsar ka, don kuwa ba za ka taba fahimta din ba, kamar yadda duk 'yan Nijeriya
ba sa fahimta duk da irin tarin abubuwan tambayoyin da suke da su, kuma suke
yi."
Muka yi shiru na dan lokaci, musamman
don kar na matsa masa, ya sallame ni a wannan ranar kamar yadda muka saba.
A gefen mu, Ofisa Ashakunu ne tsaye, sai
harara ta yake yi cikin bacin rai, duk da tun da nake zuwa wannan dibishin din
ba ma wani dasawa da shi amma ban taba ganin shi cikin bacin rai irin na yau
ba. Na kalli Ofisa Bello na ce, "Yallabai, zan iya yin wata
tambayar?"
"Yi mana, zan hana ka ne ka je ka
rubuta, ka ce 'yansanda ba abokan kowa ba ne." Ya ce da ni.
Na yi dariya, sannan na nuna masa Ofisa
Ashakunu na ce, "Yau na ga mutumin cikin damuwa, wani abu ne ya faru da
shi ne?"
Ofisa Bello ya yi dariya ya ce,
"Abubuwa da yawa ne suka faru." Ya sake kyakyacewa da dariya kamar ba
shi ba ne ya cukule min dazu a kan tambaya ba, ya ci gaba da cewa.
"Ashakunu ya ci burin wannan sabon karin
albashin da wannan gwamnatin ta ce za ta yi, don yana son zai yi aure a wannan
lokaci, aka yi ta jan biyan sabon albashin, lokacin da za a yi karin ya zo
kuma, sai ya zo da wani irin sabon salo na ka-gani-a-kwaryarka, in da shi ya ga
karin Naira dubu daya da naira saba'in. Sannan, dama ga shi tun tuni yana cikin
damuwar rufe boda da aka yi, domin an hana maigidansu shigo da kaya, wanda
kusan kullum suke samun kudi daga gare shi, don haka yanzu shi a duk duniya ba
wanda ya ke jin haushi kamar maigirma shugaban kasa, don ya ce shi ya lalata
masa shiri." Ya ci gaba da dariya.
Ni kam bin shi na yi da kallo ina
nazarin irin girman damuwar da yake ciki.
A daidai wannan lokacin wani dansanda
mai suna Sajan Ado ya shigo rike da wani dogon sauri mai siffar rakumin dawa
saboda tsayi da dogon wuya. A bayansa kuwa mutane ne kusan su shida suka dafo
masa baya, a cikinsu daya na rike da wuyansa wajen da ke nannade da farin kyalle
wanda ya jike da jini, haka nan duk rigarsa jike take da jini - Gabadaya muka
mayar da hankulanmu gare su, musamman ni da nake son labari.
Kai tsaye a gaban Ofisa Ashakunu suka
tsaya, ya daka musu tsaya, "Kai me ya faru?"
Sajan Ado ya nuna dogon saurayi ya ce,
"Ga su nan musu suke yi, shi ne wannan ya dauki almakashi ya caka wa
wannan."
Ashakunu ya dubi saurayin wanda aka
cakawa almakashi, da alama jini na daukarsa yana bukatar taimakon gaggawa,
sannan ya dubi dogon saurayin nan ya ce, "Kai wanne irin musu kuke za ka
kashe shi haka?"
Cikin gadara dogon saurayi nan ya gyara
tsayuwa, don a tunaninsa idan ya fadi abin da ya faru 'yansandan nan za su goya
masa baya, ya ce, "Yallabai wani mummunan laifi ya aikata, shi ya sa na
hukunta shi."
Muka kara nutsuwa, don jin irin laifin
da ya yi, ya yi masa wannan hukunci da yake fada.
Ashakunu ya ce, "Kai muke
sauraro..."
Dogon saurayi ya ce, "Yallabai muna
cikin musu kawai sai ya yi zagi, shi ya sa na kaddamar masa..."
"Wa ya zaga?" Ashakunu ya bukata.
"Buhari ya zaga..." Dogon
saurayi ya yi kokarin fada, amma bai kammala maganarsa ba, sai jin mari ya yi
hadi da barin makauniya daga kamfacecen hannun Ashakunu. Kafin wani lokaci ya
hadawa dogo jini da majina har da cire masa hakori guda, ya dora da fadin.
"Ka ji dan iska, wahalalle, wanne
kundin doka ne ya ba ka ikon ka hukunta mutum ba tare da zuwa wajen hukuma an
tantance laifin da ya yi ba, tare da sanin dalilin da ya sa ya aikata laifin da
kuma halin da yake ciki a lokacin da ya yi laifi irin wannan? Ka san wane hali
aka jefa shi ya sa shi aikata laifin? Ko kuma ka san wanne Buhari yake
nufi?"
Yana magana yana kirbar dogo, ni dai na
lura Ashakunu fanshe haushinsa yake yi a kan dogo, ya gama yi masa laga-laga,
ya watsa shi a sel, sannan ya ba da dama a je, a kai saurayin da aka cakawa
almakashi asibiti, don taimakon gaggawa.
Suka rankaya, ni ma na tashi, na rufa
musu baya, don ganin yadda aikin 'yansandan yake a asibiti.
Mu kwana nan.
Kabiru Yusuf Fagge
Wednesday, January 8, 2020
TARIHIN MARUBUTAN HAUSA
TARIHIN MARUBUTAN HAUSA
Muna farincikin sanar da marubuta cewar mun fara tattara tarihan marubuta don samar da littafi guda da ba a taba yin irinsa ba.
Tuesday, January 7, 2020
RUBUTUNKA TUNANINKA: MARUBUCI MAI TSARA JADAWALIN RUBUTU
RUBUTUNKA
TUNANINKA
Mataki na
2: MARUBUCI YA SAN SHI MAI TSARA
JADAWALIN RUBUTU NE KAFIN YA FARA, KO MAI DURFAFAR YIN RUBUTU BA TARE DA
TSARAWA BA?
Monday, January 6, 2020
Sunday, January 5, 2020
AN KARRAMA BALARABA RAMAT
Makarantar Unity College of Health Sciences and Technology, Kano sun karrama Hajiya Balaraba Ramat da kyautar Recognition Award.
Balaraba Ramat ita ce marubuciyar:
-Wa Zai Auri Jahila?
-Badariyya
-Wane Kare Ne Ba Bare Ba?
-Alhaki Kwikwiyo Ne
-Ilimi Gishirin Rayuwa (wasan kwaikwayo)
-Kyakkyawar Rayuwa (wasan kwaikwayo)
-Ina Son Shi Haka
Allah ya kara lafiya Hajiya, amin.
Subscribe to:
Posts (Atom)
MAKAHO MAI FITILA
MAKAHO MAI FITILA Wani saurayi yana yawo da dare sai ya hangi wani mutum da fitila. Da suka gamu, ya ga ashe makaho ne. Ya ce, "Kai wa...













